AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Adama tana cikin faɗa taji kanta na juya mata ta fara ganin fareeda da wannan almajiri dake tsaye yana ganinsu shima, uku uku take kallonsu bata yi aune ba ta tafi baya luuuuu ta faɗi ƙasa sumammiya…..
????????????AUREN FANSA????????????
BOOK ONE
NA
Ummu Fadeela
Typing????
page 12 / 13
……..A hankali adama ta buɗe idanunta, ta sauƙe su akan wani tsohon fanka dake tafiya a hankali alamun wutar nepar ta mishi kaɗan, ko kuma fankar ta gaji da duniya, ta bi ɗakin da kallo, fareeda ta hango kwance a ƙafar wata mata, kallo ɗaya zakama matar ka fahimci kyakyawa ce amma fuskar ta yayi jajawur da bilichin ga wasu kuraje tabka tabka sunyi wa fuskar ta ado, ga uban gashin dokinda ta kima wa kanta, yatsun hannu da kafarta yasha uban janfarce, ta na sanye da atampa dinkin riga da siket da ya bayyana surarta gaba daya, ta yafa wani matsiya cin gyale wanda shi da babu duk ɗaya, tana riƙe da wayar ta ƙirar android sai latse latse take yi.
Ɗan kokarin tashi adama tayi hakan ya janyo hankalin matar zuwa gareta, da hanzari ta tashi ta zo wurinta, ta ce Alhamdulillahi, kin farfaɗo, haba tun jiya kike ta barci zoki farka abu ya gagara, in banda ma zuciyar musulunci da bazan taɓa ki ba yanda taimako ya zamo jaraba a wannan zamani namu, ka taimaki mutum da zuciya ɗaya shi kuma ya cuce ka, can na ganki kwance a kofar gida kin sume ga yar yarinya tana ta rusa kuka, ga kuma ciki wannan dalili yasa na ɗauko ki. yanzu dai tunda kin farka taso ku wuce inda kuka nufa, tun ɗazu ake ta ƙira na wurin aiki amma na rasa yadda zanyi dake. tunda ta fara magana bata yi shiru ba har sanda ta kai aya.
Take adama taji kanta na sarawa tsabar yanda matar take magana da karfi karfi. Ta matso kusa da ita tace” sai surutu nake miki na manta ban gabatar miki da kaina ba, sunana hafsat! kuma ni……koda shike ma kinsani, ba wanda baisan wannan fuskar ba a arewacin nigeria.ko da shike wataƙila baki da tv a gidanki, bari kawai in faɗa miki, nice hafsat fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina finai na kallowood. yanzu haka tauraro nane yake haskawa ko ke baki gani ba? ta faɗa tana shafa fuskar ta gami da karkaɗa jiki.
Duk na isheki da surutu koh? haka nake wannan shine halin hafsatu, ina da barkwanci kuma inason masu barkwanci, ammafa da ba haka nake ba rayuwa ce ta maida ni haka.
Kirrrr wayar ta tayi ƙara alamun shigowar ƙira da sauri ta amsa ta kara a kunne, shiru tayi na dakika 3 sannan tace ” kayi haƙuri ranka ya daɗe wllh ganinan zuwa minti talatin zai kawo ni kayi hakuri karka mi haka ” . kit ta kashe wayar ta juya da sauri ta kama hannun adama ta miƙar da ita tace “maza muje ku kama gabanku kinga daga taimakonki kinja zan rasa aiki na, directors nan ba kirki ne dasu ba yanzu sai aba wata role ɗin da zan taka, tunda gadai can matan zube a location kamar jampa a jos kowa so take ta fito a cikin fim.
Har suka iso bakin ƙofa zuba take kamar yayan kurna, fareeda ne ta sake kuka ganin barin gidan zasu yi, tana faɗin”ammi kar muta fi mu zauna anan. kallo ɗaya hafsat tayiwa yarinyar da tunda ta kalleta da farko taji kaunar ta ya samu wuri a zuciyar ta, kuma kallon yarinyar yana tuna mata da wani abu da ya shuɗe a rayuwar ta.
Ganin kukan ta yana ƙaruwa ne yasa hafsat dakatar da adama wacce jiri ke ƙokarin kayar wa, tace “ku koma ciki ku zauna kafun indawo kinɗan ƙara warware wa sai kisan inda dare ya miki, godiya sosai adama tayi mata sannan taja fareeda suka koma ciki, ita ko hafsat ta fita ta tare ɗan sahu ta shige ta wuce wurin aikinta.
ADAMAWA.
Lokacin da su alhaji manga da da twins da kuma mai gadi suka dawo daga sallar asuba mamaki ne ya cika su ganin karamar kofa a wangale kallon kallo suka fara a tsakaninsu, kafun mai gadi ya sa kai yana ƙokarin fitar da sandae shi a maɓoyar ta, duk tunaninsu ɓarayi ne suka shigar musu gida, kaf gidan suka chaje amma basu ga komai ba kuma basu ga alamun anshigo ba, hakan yasa su Ammar wucewa cikin falo, mai gadi kuma ya koma wurin zaman shi suna tunanin wataƙila tun fitar sune basu rufe ƙofar ba.
A can falo kuwa zama iyalan suka yi bisa kujerun da suka ƙawata falon sukayi gaisuwar su na al’ada yadda suka saba duk safiya idan sun dawo sallar asubahi su kan zauna a falo su gaggaisa sannan mum ta zuba wa kowa tea yasha kafun su koma su kwanta sai gari ya waye, bayan sun gama sha ne Amaan ya kalli mum yace ” Sweet mum sun tashi kuwa,? ya tambaya yana kallon kofar ɗakin da’aka sa adama jiya da dare,” mum da shaff ta mance da wasu baki ta riƙe kanta tace ” kashh boɗɗi na, manta wllh amma zanje in duba yanzu ku wuce kukam,
Da kallo alaji manga ya bisu kafun ya juyo kan mum yace” wasu baƙi ake magana akai bani da masaniya. dr hauwa tace ayi haƙuri yallaɓai lokacin da ka dawo jiya nace zan baka labari akan ƴan biyu, amma sai kace inbari zuwa safiya domin kana da aikin yi.”
Yace”ohk ohk na tuna anyi haka, me ya faru da yan biyun? kuma waɗanne baƙi kuke magana akai”? tace………….. nan ta faɗa masa duk abunda su ammar suka sanar da ita daren jiya, ta kara da cewa” idan gari ya gama wayewa anyi brwakfast sai mu ji me ke faruwa da ita ko?
Da hanzari ya miƙe yace ” mace da ciki da kuma yarinya? ae matar sama’ila ce tace wane samaila kuma yace mata samaila dai mutumin ki sarkin noma , jiya tsakar dare ya ƙirani yake faɗa mun ɓacewar matarsa da ciki da kuma ɗiyar su, bana ce zan faɗa miki nauyin da mutuminki ya ɗaura min ba to ae shine, nasan yanzu haka ma yana hanyan zuwa domin muje mu shigar da report ofishin yan sanda.”
Muje inganta cewar shi yana nufar guest room dake palon da sassarfa dr hauwa ta bishi auka shiga, sai dai me wayam suka gani ba adama ba dalilinta, bathroom suka leƙa nanma wayam suka gani, Alaji manga ne ya furta Inna lillahi wa’inna ilaihi rajiun tunawa da yayi sun ga ƙofa a buɗe ɗazu bayan dawowar su sallar asubahi. me ya faru yallaɓai inji mum, da ɗan rawan harshe yace inaga ta gudu wataƙila taji wayan da muka yi da sama’ila daren jiya.
Dr hauwa tace subhanallah to me ya haɗasu dama har tabar gida a tsohon darennan, ina kuma ta nufa yanzu? Allah masani cewar alaji manga ya juya zai fita har ya kai kofa sai kuna ya dawo yace.
Kar ki kuskura maganar nan ta fito daga bakinki koda samaila ya iso sannan kijawa yarannan kunne karsu yadda su nuna sunsan wani abu akan batunnan let pretend we know nothing, kinsan halin samaila ba mutunci ne dashi ba, yanzu sai ya ɓata min siyasa ta, banda ma abunda nake samu a gidan gonarshi mezai haɗa ni abota da someone like him, ya juya ya fita yabar mum da tunanin ina wannan matar ta shiga a halin da take cikinnan.
Alaji manga yana fita yajiyo sallamar samaila daga kofar falon, ƙarasawa yayi yabuɗe kofar ya fita yace” wai sarkin noma wnn kam a hanya ka kwan ne? ” yace ” hmmm bari kawai alaji manga kasan yadda naga rana haka naga dare yanzu haka dai daga masallaci ko gida ban shiga ba nayo nan. kan wasu fararen kujerun dake karkashin wani germain tree suka zauna suna tattauna al’amarin alaji manga yana jajanta mishi. haka har gari ya gama wayewa, suka rankaya duk wani ofishin yan sanda dake yola sunkai report, sun kai gidajen redio da na tv sannan ansaka tukwici mai tsoka ga duk wanda ya kaita ko kuma yabada bayanin inda ya ganta,



