AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nuhu, mai adaidaita sahu da ya ɗauke ta da asuba daga kofar gidansu zuwa tasha yana tafe a mashi nashi yana sauraron wani gidan rediyo, kawai yaji an bada sanarwar cigiya volume na rediyon mashin ɗin ya ƙara jin ana lissafo kamannin matar da ya ɗauka dazu, da sauri ya gangara gefen kwalta jin an ambaci million biyu ga duk wanda ya ganta, da sauri yace tabbas itace……..

Kuyi manage da wannan ba yawa wani ɗan uzuri ne ua hau kaina.

Yanzu ne fa za’a fara wasan, nasan mai karatu ya ƙagu yasan wai suwaye ne zasu yi auren fansar.? to ku biyo alƙalamin ummu fadela don jin tirƙa tirƙan da zai faru daga next page Insha Allah. one luv guys????????

????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE
NA

Ummu Fadeela

Typing????

page 14 / 15

…….. Yace har million biyu akan wanda yaga inda tabi kawai hmmmm, wata zuciya tace mishi “kayi ta kanka faa don siyasa ya kusa karka je garin neman kuɗi a kulle ka don wannan duk a cikin takun siyasa ne,” a bayyane yace ” haka ne fa hmmm ” ya tada mashin nashi yayi gaba ba tare da ya ƙara bi takan sanarwar ba.

          KANO.....

Adama na zaune ɗaki shiru har kusan azahar, zuwa lokacin yunwa ya gama mata illa, abinda ke cikinta yayi fareti har ya gaji ya nutsu, fareeda ma tayi kukan yunwan har bacci ya kwasheta tana zaune shiru ta rasa tunanin me za tayi taji fareeda ta farka tana cewa “ammi zanyi fitsari” tace to mamana taso in kaiki bayi, fitowa suka yi da niyyan shiga bayi , al’ajabi ne ya kama adama ganin irin tsarin gidanda tun da take bata taɓa ganin irinsa ba,.

Gida ne dogon gaske mai ɗauke da ɗakuna masu kallon juna a ƙalla zasu kai ɗakuna hamsin ko wanne layi yana ɗauke da ɗakuna ashirin da biyar, duk yawan ɗakunan gidan kuwa banɗaki biyu ne kacal a ciki ko wanne layi ɗaya bayi ɗaya, kicin kuwa ba’a maganar sa sai dai kowa ya ajiye risho ko murgun gawayi a kofar ɗakinsa. mafi yawa daga cikin ɗakunan a rufe suke, masu shi sun fita neman na rufawa kai asiri.

Gidan yanci kenan kamar yadda yawancin mutane suke ƙiran gidan dake anguwar sabon gari a jihar kano kamar yadda aka san sabon gari anguwa ce dake ɗauke da mutane mabanbanta ƙabilu kuma suna zaman lafiya domin ba ruwan kowa da ɗan uwansa kowa ka gani harkar gabansa kawai yake yi, to haka wannan gida ma yake cike da jama’a ƙabilu daban daban kuma daga garuruwa daban daban a faɗin nigeria, kowa kuma harkar sa yake yi.

A hankali take bin dogon layin dakunan tana baza ido neman inda zata hango bayi, ɗaiɗaikun mutanen gidan da basu fita bane suka bita da kallo koda shike ba sabon abu bane a wurinsu, sun saba cin karo da yan mata da dama waɗanda ke yin ciki su gudo daga gaban iyayensu, ko kuma waɗanda ƙadddara ke afkawa su shigo duniya, yayin da wasu kuma kyan ta ne yaɗau hankalinsu suke binta da kallo.

Sannu a hankali ta iso karshen ɗakunan wani ɗan lungu ta gani ta sa kai da sauri ta dawo baya ganin wata mata ta gama wanka tana ƙoƙarin sanya kayanta, fitowa matar tayi bayan ta kimtsa taja wani dogon tsaki tace ” da tsakar ranar ma mutum bazai yi wanka cikin salama ba sai an samu masu leƙo shi, aikin banza to me zaki gani wanda baki dashi. ɗan rusunawa adama tayi tace” kiyi haƙuri bansan da mutum a ciki ba” wani tsakin ta kuma ja ta wuce abinta, shigar da fareeda tayi saidai ta rasa inda zata tsugunnar da yarinyar tsabar yadda bayin ke cike da ƙazanta kala kala ga wani shegen wari da hamamin da ke tashi, haka ta lallaba ta tsugunnar da ita a gefe tayi fitsarin yayinda adama ke ta toshe hanci dan wani irin amai ne ke taso mata.

Da ɗan sauri suka dawo ɗaki, tana ɗaga labule ta ganshi zaune bakin katifar dake ɗakin ya baza gasassun kaji guda biyu a gabanshi, ga kwalin fresh milk a gefe ɗaya, kanshi a ƙasa yana ƙoƙarin kwance qani leda da batasan meye a ciki ba.

Still adama tayi a wurin ganin ƙaton gardi zaune ɗakin bayan lokacin da ta fita ba kowa kuma, yana ta kiciniyar kwance ledar yace yau kuma kunya ta akeji ne? to ga favourite ɗin naki na taho miki dashi nasan inba haka ba yau bazaki barni insha iska ba a gidannan,jin shiru ba’a amsa ba kuma yasan wannan abune mai wuya wurin ta yasa shi dagowa karaf idanunsu suka sarƙe cikin na juna kusan minti ɗaya yana kallon ta without blinking yaka sa janye idanunsa itama ana ta ɓangaren haka ne, labulen a ka kuma ɗagawa hafsat ta shigo ɗakin sanye da wani lafcecen madubin fuska wanda ya cinye kusan rabin fuskar tata.

Ganinshi zaune yasa ta daka wani uban tsalle ta watsar da duk abunda ta shigo dashi, da gudu ta je ta rungumeshi tana faɗin yayaaa oyoyo”, ture ta yayi gefe yace ” wai yaushe zaki girma ne hafsa bakisan kin kusa samun surkai ba” baki ta ɗan turo gaba tace “sai randa kayi aure yayaa, ya hanya ina fata dai kayi musu aiki mai kyau don suji dadin nemanka gobe” sannan ta ɗau tsokar kaza ɗaya takai baki ta tauna tana cigaba da zuba mishi surutu kamar yadda ta saba.

Dakatar da ita yayi ta hanyar tambayar ta” who do we have here?

Sai lokacin ta tuna da adama da ta gani tsaye tun shigowar ta, da sauri ta kalli adama wacce ke tsaye har lokacin riƙe da hannun fareeda data zubawa gasassun kajinnan ido yawu yana bin bakinta duk yunwar ds takeji sai taji ys ninku.

Hafsa tace ahaan shigo ki zauna mana kin wani tsaya kamar gunki, ƙarasowa tayi ta zauna, hafsa ta kalli ɗan uwannata tace “yaya LAMIƊO wannan itace wacce nake baka labari jiya a waya, gyaɗa kai yayi yace “I guess” nan suka tambayeta me ya fitar da ita daga gida tiryan tiryan ta basu labarinta daga farko har ƙarshe, ba karamin tausaya mata suka yiba lamiɗo yace” hafsa sai kuyi sharing ɗakinnan da ita kafun muga yadda Allah zai mana . da toh ta amsa, sannan ta tashi ta ɗibar masa kazan ta matso musu da sauran, kallon adama tayi jin yadda take tsamin datti tace ” kai tun yaushe rabonki da wanka ta kuma kallon fareeda tace matso nan gimbiya ta zo muci abunmu rabu da wannan kurmar uwar taki, matsowa tayi suka fara cin naman duk su ukun amma adama dai a takure take, ganin yadda fareeda ke ci hannu baka hannu kwarya yasa hafsa yin dariya tana shafa kanta tace ” ci a hankali gimbiya ta zamu rage miki ae, ya sunanki ? FAREEDA ta ce a takaice, take wani tari ya kama hafsa sanda lamiɗo ya miko mata ruwa sannu suka dinga mata,.hafsa da ɗan uwanta lamiɗo dukansu yan fim ne hafsa karamar jaruma ce domin ba wani fita sosai take yi a fim ba wani fim ɗinma baifi a nuna ta sau ɗaya ba, lamiɗo kuma mai daukan sauti ne, a wurin wani ƙaddara ne ya kawo su kano har suka faɗa wannan harka.

Wannan shine mafarin zaman adama da yaynta a gidan yanci dake sabon gari, bayan sati biyu da zuwan su, wata rana hafsa ta shirya da zata tafi wurin wani shiri da suke ɗauka, ta kalli adama dake zaune tayi jugum ba abunda take sai aukin tunani, tace ” koza ki bini kema kiɗan sha iskan Allah a waje haba ace mutum baida aiki sai tunani sai kuma kuka taso kisa hijabi mutafi” ta faɗa tana kama hannun fareeda suka nufi kofa, tashi adama tayi domin harga Allah ta gaji da zama dama, lokacinda suka iso location ana ta haɗa kayan aiki yawancin mutanen wurin suna riƙe da script ma’aikata kuma nata kai kawo, directornne yake waya rai bace yace” tasan baza ta yi wannan aiki ba meyasa zata ɓata mana lokaci, yanzu duk ta ɓata mana shiri kasan kuma da scene nata zamu fara, yaushe zan samu wata har ta karanta script nan yau tayi aiki yau kasanzaiyi wuya, da sauri ya yanke wayar hango hafsa da yayi tana nufoshi tare da wata kyakyawar mace mai ciki, sannu da hutawa hafsa ta mishi ya amsa da walwala har hakan ya bata mamaki, yace wa muka samu haka yana nuna adama, tace kanwata ce ranka ya daɗe ta kawo min ziyara domin aurenta ya mutu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button