AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

ajiyan zuciya ya sauƙe yace ” faɗuwa tazo daidai da zama dama akwai wani scene na mai ciki da murja zata hau kuma bata zo ba ki mata magana inza ta iya sai abata kuma yanzu ne da shi za’a fara, da mamaki adama take kallon hafsa bayan ta juyo tana mata bayani ,” tace gaskiya nikam bazan iya ba ɓan taɓa gani ba kuma bansan yadda akeyi ba, hafsa tace to ai koya ake yi kowa kika gani ae koya yayi beside kuɗi za’a baki fa kinga kinsamu na rufawa kanki da yarki da kuma abunda zaki haifa asiri, ko kinɗauka haka zaki ta zama baza ki nemi aikin yiba hakan ba mai yiwuwa bane ai,.

Wannan maganganun da hafsa ta faɗa mata shine dalilin da ya sa ta amincewa ta karɓi aikin and wannan shine mafarin shigar adama masana’antar fim,.

Bayan wata biyu, wata rana cikin dare naƙuda ya kama adama nishinta da murƙususun azaba da ta keji shiya tayar da hafsa dake kwance tana jan minshari, a firgice ta farka tace adama ya dai ko dai haihuwar ne da ƙyar adama ta gyada mata kai zufa yana ta keto mata da gudu ta fita ɗakin ta fara kwankwasa kofar dake kusa da ɗakinta wata yar dattijuwa akalla zatayi shekara hamsi nne ta fito a firgice hafsa tace mama ladi dan Allah zoki taimakemu ga can adama a kan ƙafarta, da hanzari wacce aka ƙira da mama ladi ta ɗauko hijabinta suka rankaya dakin ita ta shige hafsa kuma ta fara buga kofar dake hannun hagunta tana cewa” yayaaa zoka buɗe mana kofa ” da sauri lamiɗo ya buɗe kofar yace ” me ya faru ne da rawan harshe tace yay… adam…..adama zata haihu fitowa yayi shima ya tsaya bakin ƙofar yana ta zagaye. tun ƙarfe biyu na dare take fama da naƙuda amma haihuwa shiru ga jini yana ta zuba har akayi sallar asuba . mama ladi ne ta sharce zufar dake diga a goshinta ta kalli hafsa tace ” hafsatu ki sanar da lamiɗo ya nemo abun hawa mukaita asibiti domin abun yayi ƙamari.

Suna isa asibiti aka karɓeta a emergency har bayan awa biyu shiru ba haihuwa ba labarinshi ga wuya tana sha ga jini dake cigaba da zuba, likitanne ya fito yace ina mijinta, kallon kallo suka fara a tsakaninsu kafun lamiɗo yayi karfin halin miƙewa yace” nine dacta” yana tafiya yace ” biyoni ofis” wasu takardu ya fitar yace “zaka sama na a hannu anan yanzu za’a shigar da ita ɗakin tiyata sannan muna da buƙatar jini leda biyar, wani gingirigim lamiɗo yaji a kansa hakan kuma bai hanasa yin sign na papers dinba sannan yace” jini kuma a duba nawa inzaiyi sai a diba i think i have enough blood.

Lab likitan ya turashi da wasu takardu kana ya fara shirin shiga tiyata, anyi tiyata successful a ka cirowa adama yarta kyakyawar gaske mai ruwa biyu wato balarabiya kuma bafulatana.( nasan mai karatu har ya ƙiyasta irin kyawun da wannan ƴa zata yi .)lols.

Ɗakin hutu a ka shigar da ita bayan an kimtsa su, hafsa dai na riƙe da ƴar tunda nurse ta miƙa mata taƙi ba kowa, likita ne ya shigo da goran jini da kuma wasu takardu, bayan ya maƙala mata jinin yace ” me sunan uwar ƴar zamu cika mata file, hafsa tayi saurin cewa adama ” yace sunan baban yafaɗa yana kallon lamiɗo nan ɗakin yaɗau shiru kafun zuwa can yaɗago kai yace LAMIƊO, shine abinda adama taji na karshe bacci ya kwasheta sakamakon allurar baccin da’aka mata saboda ta huta,

Kwana uku suka ɗauka a asibitin kafun aka sallamo su lamiɗo yayi hidima dasu sosai tamkar shine uban da gaske, adama tayi yarta huɗuba da kanta, ranar suna yarinya taci suna AISHA sunan mamar adama kenan inda ta mata alkunya da SUHEER. lamiɗo ne ya mata yanka daidai karfinshi mutanen gidan suka sha shagali adama ta samu rigunan yarinya kamar me, domin wani irin farin jini Suheer ke dashi tamkar flower mai kamshi.

Haka rayuwa ta ke juyawa adama kamar almara, a hankali suheer ta fara girma yayinda kyawunta yake daɗa bayyana wani irin shaƙuwa ne a tsakanin suheer da fareeda tamkar yan biyu, domin amminsu tayi ƙoƙarin hada kansu da nuna musu yadda zasu kaunaci juna. a haka har suka shiga boko da islamiyya a ɓangare guda kuma iyayen suna ci gaba da sana’ar su ta fim saidai adama bata yadda da duk wani abunda zai taɓa mutuncinta, sannan bata manta cewa har yanzu ita matar aurw ce ba. sau tari da yaranta take zuwa location, hakan yasa wa fareeda sha’awa da kuma burin zama babbar jaruma wanda duniya zata sani idan ta girma.( hmmmm)

     BAYAN SHEKARA  ASHIRIN.

20 YERA’S AFTER…

……….????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

   STORY AND  WRITING 
              BY 
 ASMA'U MAI  ANGUWA 

      Ummu Fadeela

Typing ????

Page 16 / 17

BAYAN SHEKARA ASHIRIN….

….. Wasu kyawawan yan mata biyu ne zaune a wani ɗan madaidaicin palo, ɗaya na zaune kan kujera, dayar kuma na zaune a kan carpet tayi pillow da kafan na kan kujerar tana ta latse latse a wayar da ke hannunta. wacce ke zaune saman kujerar fara ce sol, kallo daya zaka mata ka fahimci ta haɗa iri da larabawa, ɗayar ma fara ce amma bata kai yar uwar ta haske ba. dogon gashin kanta ne na kan kujerar ke riƙe dashi tana mata combing nashi a hankali, suna hirar su irin na yan uwan junan da suka yi mugun shaƙuwa,

Fareeda ta taɓa Suheer dake gyara mata gashi tace ” sweetheart kinsan me?” suheer tace bansa niba rabin jiki sai kin faɗa”.

Ɗan shiru tayi sannan ta muskuta a hankali kamar wacce bata so a jita tace ” just imagine, me zai faru idan mr arrogant yaga hoto na yau!?”

Ɗan marin kanta suheer tayi sannan tace ” stop dreaming mrs arrogant, a ina shi mr arrogant ɗin naki zai ga hotonki har ma yayi noticing wani abu”, kedai kawai ki maida hankali wurin addu’ar samun nasarar jarabawar ki kinsan wannan shine burin ammi ba wai maganar fim ɗinnan ba, jin shiru fareeda bata ce komai ba yasa ta leƙo kanta don ganin me take kallo, hoton dake bisa fuskar wayar ta ta ƙure da kallo, wannan ba sabon abu bane a wurin suheer, don haka wayar ta janye daga hannunta gami da cewa ” ya kamata ki hutar da kanki haka ki rage kallon da zaki masa gobe,ɗan murmushin da ya ƙara ƙawata fuskar ta tayi sannan tace

“Suheer baza ki gane yadda nake ji bane, bazaki gane yadda nake ji a zuciya ta ba a duk lokacin da na ɗaura idanuna a kan hoton fuskar RASHEED MATAWALLE, ba.

Ina tsoro yar uwa ta, ina tsoron kar in rasa shi, bansan ya rayuwa zata yi dani ba idan na rasa shi, gashi abun takaicin ma baisan niba, baisan da zamana ba, bai taɓa gani naba, nikaɗai nake kiɗa na nayi rawa na, bai…… kuka ne yaci karfin ta ta kasa ƙarasa abunda tayi niyyar faɗa.kuka take sosai kamar wanda aka cewa mamar ta ta rasu.

Sauƙowa suheer tayi ta rungume yar uwarta tana share mata hawaye, tace kidena kuka sweetheart, ko so kike nima inyi kukan, insha Allah wata rana zaisan da zamanki, harma ya ƙira ki a waya, wataƙil ma yazo har fallonnan ya gaida ammi da kawu lamiɗo, da kuma aunty hafsa. duk a ta dalilinki.
Wani irin dariyar farin ciki ne ya kama fareeda saida ta dara son ranta sannan ta kuma rungume suheer cikin muryar tausayi tace ” amma rabin jiki ina jin tsoro kwana nan ina yawan jin fargaba, gashi ina yawan yin mafarki dashi, ” ɗan shafa bayanta tayi alamun lallashi tace ” ki yawaita addu’a kinji, shaiɗanne, nima haka nake fama da fargaba kwana nan sai inga kamar wani abu mara daɗi yana gab da faruwa dani ga yawan mafarkin da nake yi da wani mutumi amma bana ganin fuskar shi duk ƙoƙarin dana yi.” ta kamo hannun ta tace “muje mu kwanta kinga dare yayi gashi in Allah ya kaimu gobe sammakon duba result namu zamuje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button