AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Alwalan kwanciya bacci sukayi domin ya riga ya zama musu kamar farilla dan tun suna yara ammi ta koya musu gashi har sun girma basu dena ba.koda suka hau gado addu’ar bacci suka yi suka shafa kafun su kwanta, ƙarƙashin filo fareeda tasa hannu ta janyo wani envelope ta buɗe ta ciro wani hoto daga ciki ta rungumeshi gamm a ƙirjinta, nan da nan bacci ya kwasheta, a hankali suheer ta tashi ta zare hoton cikin dabara ta aje a gefe, sannan ta gyara mata rufar ta, ta koma ta kwanta itama.

Zaune suke akan wani lallausan darduma dake tsakiyar lambun wani hamshaƙin gida ko’ina ka waiga shuke shuke ne masu daɗin kamshi da suka ƙawata wurin ga kukan tsuntsaye masu kwantar da hankali, a gefe ɗaya kuma wani kwancaccen swimming pool ne cike da ruwa fari ƙal, tana kwance ne akan kafafunshi yayinda yake zaune hannunshi ɗaya akan dogon gashinta mai santsi da sheki sai aikin shafawa yake yi.

A Hankali yake sauƙo da hannunshi zuwa kasa yana ci gaba da shafawa romantically, har ya dire zuwa kan lallausan fatar cikinta, ɗan zabura tayi kaɗan haɗe da riƙe hannun tace “. plss mana hayatie”.

Ɗan murmushin gefen baki yayi ganin sakonshi yakai inda yake da buƙata, yana mimicking muryar ta yace “plss mana hayatie, sai kuma ya sauƙo da bakinshi daidai kunnenta ya raɗa mata wani abu da yasa duk wani gashi dake jikinta miƙewa. da gudu ta tashi saida ta tabbatar tayi nisa dashi ta tsaya ta masa gwalo tace ” only in your dream”,

Yi yayi kamar zai tashi ya kamota da sassarfa ta faɗa entrance na gidan..
A firgice suheer ta farka daga baccin da take duk ta haɗa uban zufa sai haki take yi tace “Subhanallah wannan wane irin mafarki ne? ɗan juyawa gefenta tayi ta kalli fareeda dake baccinta peace fully har wani murmushi take yi alamun tana mafarki mai daɗi, kanta kwance kan fillon suheer, wato ta baro filonta cikin bacci ta dawo kan na yar uwar, tsaki suheer tayi tace haba no wonder mana tunda na haɗa filo dake ai dole inyi irin mafarkin ki, dayan filon ta ɗauka ta jefa ta kafan fareeda tagi kwanciyar ta, sai ya zama sun kwanta kai da ƙafa. duk yanda suheer taso ta koma bacci abun ya ci tura sai wannan mafarki ke ta dawo mata arai.

Washe gari bayan sallan asuba,aikace aikacen da suka saba suka yi sannan suka yi wanka suka shirya domin zuwa duba result nasu da aka kafe, a gaggauce suka yi breakfast ammi ta basu kuɗin mota suka wuce, tafe suke suna ɗan tattaunawa fareeda tace” sweetheart zuciya ta cike take da fargaba, bansan me ya sa ba ji nake kamar bazan yi nasara ba, rashin nasara ta kuwa daidai yake da rashin cikar burina na zama fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fim, rashin shiga ta fim kuma daidai yake da rasa numfashi na sweetheart, ta ƙarasa hawaye na zirara daga idanunta wanda ke nuna tabbacin daga karkashin zuciyar ta maganar ke fitowa.

Cikin share nata hawayen itama domin sosai a yan kwanakinan al’amarin saurin kukan yar uwarta ke sata kuka itama suheer tace “no sweetheart have hope Insha Allah zamuyi nasara kuma ammi zata barki kizama jaruma kamar yadda kike da burin zama,” ɗan girgiza kai fareeda tayi tace” nikaɗai nasan me nakeji rabin jiki!”.

( kasancewar tun da daɗewa adama ta fahimci irin burin da fareeda ke dashi nason zama tauraruwa, wanda hakan yasa bata da aiki sai kalle kalle da karanta magazines na taurari duk shafukan dake kan wayarta dandalin yan fim ne, hakan yasa take wasa da karatun ta matuƙa tun suna sakandire, shiyasa ta gindaya mata sharaɗin cewa sai ta kammala jami’a ta fito da first class kafun ta barta ta shiga harkar fim tayi hakanne kuma don ta samu tayi karatu mai kyau, tun shekaru goma da suka wuce adama da hafsa suka bar harkar fim sakamakon aure da hafsa tayi hakan yasa adama ta dena jin daɗin harkar saidai auren hafsa baiyi shekara ba suka rabu da mijin hakan yasa ta dawo suka cigaba da zama, saidai su chanza sana’a inda adama take sana’ar kayan sawa na mata dangi su laces, atampa, shadda, materials, veils, jeweleries, da duk wani nau’in kayan sawa, sannan tana haɗawa mutane lefe, hafsa kuma tana aiki da wani cathering school kasancewar ta gwana a fannin girki, lamiɗo dai yana masana’antar har yanzu a matsayin mai ɗaukan sauti dukda cewa zamani ya sauya,kuma har yanzu baiyi aure ba, kamar wanda aljana ta aura, lolls. tunda daɗewa hafsa ta kawo musu form na cathering school da ta ke aiki amma fareeda taki zuwa sai suheer ne ke zuwa, ita dai fareeda ba ta da aiki sai labarin jarumi kaza ko jaruma kaza.)

Lokacin da suka sauƙa a makarantar kirjin fareeda ne ya tsananta bugu, har suka ƙarasa inda aka kafe sakamakon jarabawar a hankali suke jerin lambobin da kallo wani uban tsalle suheer ta daka ta rungume fareeda, “yadai rabin jiki andace ne”? cewar fareeda, gyaɗa mata kai tayi tana nuna mata sakamakon ta. a hankali fareeda ke cigaba da duba nata, da sauri ta matsa baya, sai kuma ta fara tafiya da ɗan gudu gudu, binta suheer tayi tana ta aikin kwala mata kira amma sai ƙara karfin gudunta ma tayi kafun suheer ta cimmata har ta iso bakin get na makarantar ta tsaida abun hawa, tana ƙoƙarin shiga suheer ta iso a tare suka shige sahun sukabar makarantar suheer ne tayi karfin halin sanar dashi inda zasu sannan ta riƙe hannun fareeda tana shafawa, dan gaba ɗaya tunaninta ya tsaya ta rasa abun faɗa domin alamu sun nuna wannan karon ma rabin jikinta batayi nasara ba,.

Koda suka iso gida sun iske ammi zaune palo ita da aunty hafsa kamar yadda suke ƙiranta da kuma wata ƙawar ammi kuma costomer ɗinta zaune a falo ga kaya zube hajiya saratu tana zaɓa, da sallama suka shigo ganin baƙuwa palon yasa suna gaisheta suka shige cikin ɗakinsu, kallo ɗaya ammi tayiwa duskar fareeda jikinta ya yi sanyi domin ta fahimci wannan karonma ba bu nasara, kallon juna sukayi da hafsa ta mata wani sign da idanu hakan yasa ta tashi tabi bayansu, hajiya saratu ta ɗago bayan wucewar hafsa ta kalli ammi tace “niko hajiya adama akwai abunda nake so infaɗa inba damuwa.” kallonta ammi tayi tace”ina jinki ba damuwa” .

Gyara zamanta tayi tace” niko ya ta ta tsaida miji ne? ammi tace wacce kenan daga cikin ƴaƴan naki tace fareeda naga ita ce babba gashi har yanzu shiru kodai saita ƙare karatunta ne,? ammi tace ” ai almost karatu kam ya ƙare domin yan watanni ya rage musu amma basu tsaida miji ba, da so nayi insun kammala sai inhaɗa su kawai lokaci ɗaya in aurar, ” hajiya saratu tace “ah to faɗuwa yazo daidai da zama kenan ga can saleem ya dawo, da daɗewa nake masa zancen aure amma yaronnan sai cewa yake tukunna bai shirya ba ni na rasa wanne irin shiri ne yake magana akai , inba damuwa sai kiyiwa babanta magana inya amince sai inturoshi yazo ya ganta.

Wani irin sauti kirjin adama ya bada jin hajiya saratu ta ambaci kalmar babanta, yanzu kowa kallon matar lamiɗo yake mata kenan anɗauka shine uban yaranta, akwai matsala ta faɗa a hankali. sai kuma tayi saurin aro fara’a ta yafa a fuskar ta tace ” naji daɗin wannan magana taki insha Allahu duk yadda mukayi dashi zaki ji daga gareni.

Kuka hafsa ta samu fareeda nayi kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa, suheer kuma na gefe tana taya ta. shiru ta ɗanyi kafun ta ƙarasa shigowa ɗakin zama tayi a tsakaninsu ta hau aikin lallashi da kyar ta samu sukayi shiru, sai bayan wani lokaci mai tsawo kafun ammi ta gama da hajiya saratu ta shigo ɗakin,.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button