AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin fuskar ammi kawai ya tabbatar wa fareeda hasashenta, zama tayi fuskar nan ba alamar fara’a tace baki yi nasara bako? idanu kawai fareeda take zarewa, labulen ɗakin aka buɗe lamiɗo ya shigo yace” me ya samu gidanne haka yau yazamo so dull,” ganin fuskokin su yasa shi shigowa ɗakin sosai yana kallon yaran yace ” me ya samu gimbiyoyi na kuma” ƙara fashewa da kuka suka yi da kyar suheer tayi karfin halin cewa “fareeda ta faɗi jarabawa” .
Ya buɗe baki da niyyan magana Adama ta katse shi ta hanyar ɗaga masa hannu tace” wannan yana nufin ba maganar shiga harkar fim don haka ƙar inƙara jin maganar nan a gidannan , matuƙar bazaki maida hankali kiyi karatu ba to aure zan miki yanzu haj, saratu tamin maganar dan wurinta zai zo ya gank…..da gudu tazo ta faɗi gaban ammi ta riƙe kafafunta ta ringa rusa ihu kamar ana ƙwaƙule mata idanu, suheer ma ta kariso ta zauna a wurin suna ta kuka, inka ga yadda suke kuka sai sun baka tausayi.cikin kuka fareeda take magana” dan Allah ammi kimin rai karki bari in mutu rashin shiga ta fim daidai yake da rasa rayuwata, dan Allah ki barni incika burina, kullum mafarkina shine in zama jaruma da wannan burin na taso ammi na kowa shaida ne a wurinnan, kullum mafarkina shine inzama babbar tauraruwa yadda zanyi kuɗi in gina mana babban gida da motoci mu ringa fita kasashen waje yawon buɗe ido wannan shine burina ammi karkice a’a komai zai iya faruwa dani zuciya ta zata iya bugawa in mutu ammi naaaaa ” ta karisa da sake wani kukan da ya fi na farko, sosai suke kuka su biyun yayinda idanun hafsa ya cika da ƙwalla kallon ammi tayi tace adama dan Allah ki dubi lamarin yarinyar nan kibar ta ta cika burinta lamiɗo yace plsss adama kibar yarinyar nan ta tabbatar da mafarkinta,.
Da faɗa adama tace wai ba wanda yaji abunda fareeda take faɗa ne sai ni kaɗai, wato ta rena abunda muke mata so take ta zama jaruma wanda duniya ta sani tayi kuɗi ta gina mana babban gida da motoci mu ringa fita duniya yawon bule idanu, ba maganar aure da karatu a rayuwar ta so take ta ƙare rayuwarta a harkar fim daga karshe ta tashi ba aure, ba ƴaƴa, ba kuɗin, kuma ba jarumtar kowa ya manta da ita kamar ba’a taɓa yayinta ba, tunda kullum sabbin fuska ake samu sannan mace karamin lokaci gare ta idan damar ta wuce mata kuma shike nan so take ta ƙare rayawar ta kamar hafs……sai kuma tayi shiru.
Dariyan daya fi kuka ciwo hafsa tayi sannan tace” ta ƙare rayuwar ta kamar hafsa ko?ko ba haka ba adama ? karisa mana bazan hanaki ba ai sai kuma kuka ya kwace mata, wanda abune mai wuya kaga tayi kusan ma adama zata iya rantsewa bata taɓa kallon hawayen hafsa ba tsawon shekarun da sukayi a tare, jikinta ne yayi sanyi tace ba nufina ba knn hafsa, ɗaga mata hannu hafsa tayi tace tabbas da ace ana maida hannun agogo baya dana maida tawa rayuwar baya, da na sani na zauna dana sani bankai ta na aje ta a tsakar gida ba, dana sani naji shawaran baba na, dana sani ban….. kuka ne yaci karfinta har ta kasa magana lamiɗo ne ya kamata yana share mata hawaye kirjin shi na mashi nauyi yana tuna rayuwar su na baya, tadan tsagaita kana tace” ko ta na ina yanzu kota na raye ko ta rasu Allah masani gashi yau ana min gorin rashin haihuwa.
Adama tace ba gori nake miki ba kawai ina yin abunda ya dace inyi ne a matsayina na uwa sannan nauyin fareeda dake kaina yafi nauyin suheer girma wannan abunda nayi shine daidai kuma shine abinda yadace da kowacce uwa ta gari.
Lamiɗo ya dube ta yace me kike nufi da nauyin fareeda yafi na suheer girma a kanki”?
Tace “saboda fareeda ƴata ce amma ba ni na haifeta ba.”
????????????AUREN FANSA????????????
BOOK ONE
STORY AND WRITING
BY
ASMA'U MAI ANGUWA
Ummu Fadeela.
Typing ????
Page 18 / 19
……..Lamiɗo ya ɗago idanunshi ya kafe adama da su, hakan yasa ta fara rawan harshe, yace”me kike nufi da maganar ki? cikin inda inda da rashin jurewa ganin idanunshi wanda ya tsayar dasu kyam a kanta tace ” Fareeda ƴata ce, tun tana tsummar ta nake riƙonta sakamakon rashin mahaifiyar ta da ta yi, hakan yasa dole inkula da’ita fiye da komai domin ita ɗin nauyi biyu ce a kaina.
Lamiɗo yaɗan matsar da idanunshi daga kanta yace ” wannan bai zama dalilin da zai sa kihanata cimma mafarkin ta wanda ta daɗe da burin son cimma shi ba, kiyi wani abu a kai adama ki ƙara bata wani dama idan tayi failing, thats d end saiki ɗau duk matakin da za ki ɗauka.
Ɗan murmushi adama tayi sannan tace ” mafarki” hmmmm kasan irin mafarkin da take da burin cimmawa kuwa,? mafarkinta kullum shine ta zama jaruma tauraruwa, ta ringa fitowa a cikin fina finai wanda RASHEED MATAWALLE yake taka rawa a cikinsu, irin wannan fim datake son zama tauraruwa a cikinsu tunda hafsa ta fara harkar bata taɓa fitowa ko a mai sharan office ba, tunda ka fara ɗaukan sauti tsawon shekaru ba’a taɓa gayyatan ka aiki a irin fina finan da RASHEED ke fitowa ba . shine kake so in bar fareeda taje,? ta ina zata fara,? bazan yadda ta zubarda mutuncin ta ba, yazam tayi biyu babu ba, ita bata zama tauraruwa ba ita ta rasa ƙimarta a idanun mutane ,
hafsa ne tayi saurin cewa “amma adama baki san me gobe zata haifar ba kowa da kalan sa’an shi da kuma ƙaddarar shi,
Dariyan takaici ammi tayi ta fara zagayen ɗakin sannan tace ” hafsa kenan tunda na sanki tsawon shekaru wannan shine mafarkin ki kema ko ba haka ba? kullum mafarkin ki shine wata rana zaki zama babbar tauraruwa, kullum kalmar ki itace baki fidda rai da cewa zaki zama tauraruwa ba, shin wannan burin naki ya cika ? kice min a’a, yanzu shekarun ki nawa? akwai nasaran da zaki buga kirji ki nuna wanda kika samu a rayuwar fim?.
Share hawaye hafsa tayi zuciyar ta na mata zafi, ta san gaskiya adama ta faɗa amma wannan gaskiyar tafi maɗaci daci a wurinta,
Adama wacce ta kasa tsayuwa wuri ɗaya sai aikin zagaye dakin take kamar ansa ta dole, taci gaba da cewa “don haka yanzu zanyi abunda ya dace na mata “, ta faɗi haka tana ƙoƙarin daddana wayar ta, tunda ammi ta fara magana suheer da fareeda suka haɗa kai suna rusa kuka, basu ɗau maganar ammi na cewa ba ita ta haifi fareeda ba da wani muhimmanci, a tunaninsu tayi hakan ne domin neman mafita, amma maganar ta na karshe yayi mugun ɗagawa fareeda hankali a tsananin firgice ta zage ta ware gaba daya sautin murya da Allah ya mata ta zabga wani ihun da illahirin anguwar sai da ya amsa, ƙara ƙanƙameta gaam suheer tayi ganin alamun tana gab da ficewa hayyacinta.
Ko kallon inda suke ammi ba ta yi ba, ƙara wayar ta tayi a kunne , da sallama hajiya saratu ta amsa wayar gami da cewa” hajiya adama badai mantuwa nayi ba ko?” ƙaramin murmushi ammi tayi kana tace “ko ɗaya dama akan maganar da mu ka yi dake dazu ne kan batun yarannan zaki iya turo shi saleem ɗin ya ganta” , ” to to babu matsala zai zo insha Allahu kuwa Allah dai ya bar zumunci hajiya” cewar hajiya saratu. bayan sun ajiye wayar ne ta juyo ta kalli yaran har cikin ranta take sonsu da kuma tausayinsu amma yaza tayi,? wannan shine abunda duk wata uwa ta gari zata yiwa ƴaƴanta abun alfaharin ta.
Tace” sai ki shirya any time soon zaki iya samun baƙo” ta juya tayi ficewar ta daga ɗakin ta barsu suna cigaba da kukan su, lamiɗo ma fita yayi ya barsu domin baison cigaba da jin kukan su, jinsu yake a ranshi tamkar shi ya haifesu. hafsa ne tayi ƙoƙarin janyo ƙafarta da suka mata nauyi tamkar an aza musu buhun siminti ta matso kusa dasu tana aikin lallashin su yayinda itama take ta yaƙi da nata hawayen.