AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fareeda ta ɗan tsagaita da kukan da take yi zuwa lokacin kanta ya mata nauyi idanunta basa kallo mai kyau, sai wani dishi dishi take gani, ga wani uban sanyi da take ji yana shiga daga tafin ƙafarta yana haurawa ya samu matsugunni a cikin ƙwaƙwalwarta take jikinta ya amsa ta fara karkar war sanyi har wani karo da juna haƙoranta keyi, cikin minti biyu jikinta ya ɗume da zazzaɓi mai zafin gaske.
Ganin halin da ta shiga ne yasa hafsa ɗago ta da taimakon suheer suka kwantar da ita kan gado suka rufa mata bargo, zama sukayi jugum jugum kamar masu makoki suka sata a gaba da kallo, da ƙyar fareeda ta buɗe idanta da suka mata nauyi ta kamo hannun suheer tace” rabin jiki! kiyi wani abu kar ki bari ammi tamin aure, kar ki bari inrasa mafarkina. plssss help your sister plsssss, ta kare wasu hawayen na ƙara zubo mata wanda suka fi na farkon zafi.
Gyaɗa mata kai suheer tayi tace” karki damu sweetheart zaki samu cikar burinki insha Allah yanzu ammi tana cikin fushi ne amma da zaran ta sauƙo zaki sha mamakin abunda zatayi, ki kwantar da hankalin ki kinji karkizo kuma wani ciwon ya kama ki. da haka wani bacci ya kwasheta bayan hafsa ta ɓallar mata paracetamol tasha.
Washegari haka suka tashi gidan ba wani walwala kamar yadda aka saba a baya, da misalin karfe huɗu na yamma saiga saleem yazo har ɗan madaidaicin palon nasu aka isar dashi, bayan sun gaisa da ammi sai ta shiga dakin yan matan ta same su zaune suna tattaunawa su uku ganinta yasa su yin shiru suna ta zare idanu kamar ɓerori a cikin bokitin gari, shigowa tayi ta kalli suheer tace ” me kuke ƙullawa “? da sauri tace ba komai ammi kawai ina mata faɗan ta tashi tayi wanka ne kar baƙon ya iso yasa meta da datti” juyowa kan hafsa ammi tayi ta kalle ta ita kuma ta juyar da kanta tana taɓe taɓe a wayarta. hakan yasa nuna fareeda tace ” to maza ki tashi ki kimtsa domin baƙon ya iso saura ki masa wani abu na rashin da’a kuma” ke kuma ta nuna suheer “tashi maza ki kai masa ruwa da abun motsa baki,” da to ta amsa sannan ta miƙe ta fita, ammi kuma ta samu wuri ta zauna to make sure fareeda ta shirya akan lokaci.
Suheer tana sa kai a palon suka haɗa ido da shi, ba laifi yana da ɗan kyanshi domin baza’a sashi a layin munana ba, kuma da ganinshi ɗan boko ne. da fara’a ta karasa shigowa tace sannu da zuwa bari a kawo maka ruwa, kitchen ta shige yayin da ya bita da kallo kamar mayunwacin zaki yana lasar leɓenshi na ƙasa. a ranshi yace chakwai kenan, da ɗan madaidaicin tire ta fito riƙe a hannunta ta kariso ta dire a gabanshi ruwan leda ne guda biyu a kai sai wani ɗan faranti mai ɗauke da doughnut guda uku, ” bismillah ga ruwa” ta faɗa tana komawa kan kujerar, da kallo ya kuma binta ita dai duk ta taƙura da kallon da ya ke mata irin na ƙurilla kamar mai son gano wani aibu a tattarw da ita. cikin sigar kwarewa a iya barikanci ya ɗan karkata kanshi ya kashe murya yace ” mu fara gaisawa mana tukun my fareeda ni kallon ki ma kawai ya ƙosar dani” da hanzari suheer ta ɗago kanta ta zuba mishi idanunta masu kamar an diga zaiba a cikinsu kana ta riƙe baki tace ” kai tuba nake babban yaya amma ba ni bace yayata ce tana kan fitowa yanzun nan.
Wani ƙululun bakin ciki ne ya ziyarci zuciyar shi wanda har hakan ya kasa boyuwa akan fuskarshi, yace” au to na zata kece ai shiyasa, tace” a’a” doughnut din ya ɗauka guda ɗaya ya fara ci yana kallonta ta wutsiyar ido har ya gama ya ɗau ruwa leda ɗaya yasha kamar rabi ya aje sauran, ɗan kallonshi tayi tace” haba kaci mana bayan don kai nakawo, kodai kunyar kanwar taka kake yine”? ɗan girgiza kai yayi yace ” not at all” nan suka gaisa ya faɗa mata sunanshi saleem atakaice ta ce mishi” suheer” nice name kina da suna mai daɗi ,” nagode” ta faɗa sannan tacigaba da magana wanda yajawo hankalinshi kacokam zuwa gareta, ta kai minti bakwai tana magana kafun ta ɗan tsagaita, kallonta yake yi without blinking yace ” are u sure ” jinjina masa kai tayi, yace but ni hajiya ta bata sanar dani duka wannan ba .
Suheer tace ai ba lallai tasan da hakan ba, nima na sanar da kaine dan banason a cuceka inkuma baka yadda ba kasa a maka bincike ganin fareeda ta fito yasa suheer jan bakinta ta tsuke kamar ba ita ke zuba magana ba yanzu. a haka fareeda ta ƙariso kanta a ƙasa, kallo ɗaya ya mata maganganun suheer suka fara dawo mishi dalla dalla, wuri ta samu ta zauna a kusa da suheer still kanta a ƙasa ta gaisheshi amsa mata yayi, daga gaisuwan ɗakin ya ɗau shiru na tsawon minti biyu sannan saleem ya miƙe yace ” ni bari inzo in wuce kar magriba ta shigo, suheer ne kawai ta iya cewa mun gode, ya juya ya fita, kallon juna suka yi suka buɗe baki a tare zasu yi ihu kome suka tuna kuma suka kuma yin shiru a tare sai kuma suka rungume juna suna ɗan tsalle kaɗan kaɗan, sai kuma fareeda ta sake ta tace “wait sweetheart me kika faɗawa gayennan naga kamar har ya ɗauka,” ?
Dariya tayi tace “kamar dai yadda muka tsara ” lakace dimples nata da duk sanda bakinta yayi motsi yake loɓawa balle kuma in tayi dariya fareeda tayi haɗe da cewa “thats my sister” ƙara rungume ta suheer tayi tace anything for you sweetheart” so yanzu no more zazzaɓin aure kenan dariya suka yi sannan suka koma ɗakin yanda suka bar ammi da aunty hafsa haka suka taddasu, dagowa kaɗan hafsa tayi daga kan wayar ta suka haɗa ido da suheer ido ɗaya ta kanne mata, ɗan gira kaɗan ta daga sannan ta maida kanta ta cigaba da abunda ta keyi kamar bata ga shigowar su ba.
Tashi ammi tayi tace ” har ya tafi “?kai fareeda ta ɗaga mata ta kuma cewa da sauri haka”? suheer tace yace yanada uzuri yanzu amma zai kuma dawowa, zama tayi sannan ta kalli hafsa tana sauƙe ajiyar zuciya tace ” hafsat kina ganin nayi daidai? kuma zuciya ta ta kasa tsayuwa wuri guda . ɗan kallonta anty hafsa tayi ta saman ido sannan tace” uhmmm tun yanzu har kin fara karaya ne? to Allah kyauta, tsamm ta miƙe tayi gaba abinta ammi ta bita da kallo.
Da daddare suna zaune suna dinner gaba ɗayansu kamar yadda suka saba wayar ammi yayi ƙara alamun shigowar kira dauka tayi ganin mai ƙirannata bayan sun gaisa tagi shiru na tsawon lokaci tana sauraron bayanin da hajiya saratu ta ke mata, zuwa can tace to ba komai hajiya Allah yasa hakan shine mafi alheri saratu kar ki dam.
Sauƙe wayar tayi sannan ta tashi ta shige ɗakinta abincin da basu ci ba kenan a ranar.
Washegari suheer ta tashi da niyyar zuwa cathering school nasu don ta jima bata jeba bayan ta shirya ta ɗauki jakarta ta rataya sannan ta matso kusa da fareeda dake aikin da ta saba wato kallon fim magazines, ɗan side hug ta mata tace ” iam going sweetheart” ɗagowa fareeda tayi tace Allah yaba da sa’a rabin jiki amma har yanzu ammi bata ce mana komai bafa,
don’t worry dear everything will going to be alright okey. gyaɗa mata kai fareeda tayi, ta juya ta fita ammi da anty hafsa da lamiɗo ta samu palon zaune suna magana ga ammi tana ta sharan hawaye, kallon su tayi ɗaya bayan ɗaya zuciyar ta na tsinkewa , amma da shike ba tarbiyar da aka musu bane shiga maganar manya sallama kawai ta musu tasa kai ta fita gidan.
Taxi ta tare ta shiga mutum ɗaya ne zaune gaban motar da wani a baya hakan yasa ta zauna a bayan can kurya suna cikin tafiya duk motsin da tayi sai taji idanu a kanta alamun ana ganinta, gashi ta kasa samun courage na dagowa taga maishi, wayar ta ne ya fara ruri da irin ƙiɗan da ta sawa fareeda mai taken ƴan uwan juna da hanzari ta fitar da wayar daga cikin jakar ta ta kara a kunnenta, muryar fareeda da taji kawai tabbatar mata da how happy she is, da mugun mamaki suheer tace “what, me kika ce? come again i don’t get you, da farin ciki fareeda tace wllh da gaske ammi ta barni in fara fim amma da wasu sharaɗi sai ki dawo zan faɗa miki, da matsanancin farin ciki suheer tace congratulation rabin jiki, dole ne inna iso wurin aiki i mana special cake wanda zamuyi celebrating wannan abun farin ciki dashi, amma ta ya ya hakan ya faru,? fareeda tace bayan sunyi zaman mitin ɗazu shine kawai ta shigo ta faɗa min, ina cikin farin ciki sister yanzu na samu daman dazan fito cikin fim tare da RASHEED kawai abunda ya rage min shine ta yaya, a ina zan ganshi, mitumin da bai san da zama na ba. suheer tace ” ai an riga da anyi babban tunda ammi ta amince kekam sai na dawo zamu tattauna sosai.