AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da tsananin damuwa suheer ta shige wani adaidaita dake wurin tana share hawayen da suka ki tsayamata tace” mu bi bayansu”, da sauri yabi bayan motar da akasa habeeb gidun karsu musu nisa.

Buba P.A da direba kuwa saida suka gama clearing komai a airport sannan suka fito, taxi suka shiga kasancewar boss ya tafi da motar kuma da mota daya aka zo daukanshi tunda yace bayason kowa yasan da dawowarshi.sunzo shigewa ta anguwar su suheer suka ga kan kwalta a cike da jama’a gashi ana kokarin saka wani kamar gawa a mota, leko da kai buba yayi kallo daya ya musu ya fahimci boss ne ya hada wnn crowd din, dan yadda ya fita daga airport dinnan yasan kawai sai kariyar Allah,

Jira suka yi saida taron yadan watse kafun suka samu hanya suka wuce.

Tunda ya kade shi bai tsaya ba gudu kawai yake a ranshi yana jan tsaki, sitiyarin motar yakuma bugawa a karo na uku ranshi yana tukuki kamar zai qone, a haka ya shigo cikin anguwar Nasarawa G.R.A bai fasa gudun ba har ya riski wani wawakeken get mai kama da kofar shiga gari horn ya danna da karfin gaske, da gudu mai gadin gidan ya karaso ya bude kofar domin yasan mutum daya ne mai irin wannan aikin, wani tsalle mai gadin ya buga ya koma gefe ganin alamar takanshi zai bi da motar, gida ne mai girman gaske domin yafi karfin ace masa gida ma saidai mansion, duk inda ka wurga idanka baza kaso daukewa ba tsabar haduwar wurin, a kalla gidan zai kai rabin wani anguwa ta ko’ina shuke shuke ne masu ban sha’awa daga bakin get baka iya hangi main house din saika yi dan tafiya mai tazara.

Wani dan kwalta ne kwance daga bakin get din wanda zai maka jagora har izuwa parking space, da irin gudun nashi mai kama da gudun fanfalaki ya iso wurin ajiyar motocin wanda shima wani duniya ne na mussam zaune da kafafunsa. Parking yayi sannan ya kuma danna wani horn din wanda yafi na farko kara, saida yaja wasu seconds din kafun ya bude motar ya zuro kyawawan kafofinshi waje yana ta aikin karkadasu kamar mai jiran wani abu.

Tunda taji karar horn nashi ta kara gyara zamanta a palon wanda kawatuwar shi bazai misaltu ba saidai mai karatu ya kiyasta a ranshi irin palon daza’a samu a irin wadannan gidajen. zuciyar ta na tsananta harbawa da sauri sauri, kara gyara zama tayi duk ta kasa nutsuwa, kyakyawan mata ce da kallo daya zaka mata ka gane hutu da jin dadi ya samu matsugunni a jikinta, baza ta haura shekara hamsin ba a duniya.

A hankali ya sauko gaba daya daga motar ya nufi entrance na gidan, kara murtuke fuska yayi kamar wanda bai taba ganin ana dariya ba kafun ya bude kofar palon karaf idanunsu suka hadu kasancewar tana facing kofar ne dama, dauke kai yayi da sauri, tashi tayi da hanzari tace “welcome son,” ya hanya ? inkawo maka ruwa ne? fatan baka da wani damuwa ko? duk a cikin kasa sekon talatin ta mishi wadannan tambayoyi yayinda jikinta yake dan karkarwa, kara tamke fuska yayi still yana tsaye kuma baice komai ba,bude kofar palon akayi saiga buba ya shigo wani ajiyan zuciya Rasheed ya sauke sannan ya juyo ya kalli p.a nnashi yace ” bana bukatar sannu da zuwa, kuma bana bukatar ruwa, sannan bana bukatan kulawar kowa,” daga haka ya juya da sassarfa ya iso bakin staircase ya haura sanda yakai karshe sannan ya kuma kama wani wanda zai haura dashi hawa na biyu inda nanne bangarenshi. Nan ya barsu sakato buba yasan me yake nufi haka ita ma tasan me yake nufi,shidai buba yana mamakin anya kuwa itace mahaifiyar boss, tunda yake tare da boss bai taba ganin ya mata magana ba inta mishi magana ma saidai ya kalli wanda ke gefe ya mishi shagube, idan akayi rashin sa’a ba kowa a wurin kuwa haka zai ta tsayuwa a wurin har sai ta tafi kafun ya tafi, a bangare guda kuma bai taba ganin caring mother irin UMMIE ba, yanda take kula da Rasheed yafi yanda take kula da kanta, ko menene silar wannan abu dake faruwa? Allah masani amma zai so ya ji wannan labari,

Sheshshekar da ummie ke yi ne ya dawo dashi hayyacinsa, da sauri ya dawo kusa da ita “yace plsss hajiya kiyi hakuri kima menene kar ki zubar da hawayenki akansa, domin hawayenki masifa ne a gareshi”, da sauri ta goge hawayen sannan ta kawo murmushi ta daurawa fuskar ta, tace” yauwa kadau abincin can ka haura masa dashi sama dan tun da safe nake kitchen ina hada masa abincin ka tabbatar yaci sannan make sure yasha maganinshi dan naga kamar ranshi a bace yake”, ta fada tana nuna saman teburin dake cike da manya manya kuloli kai kace biki za’ayi a gidan”.

Da to buba ya amsa yana mai rusinawa.

Lokacin da Rasheed ya shigo bangaren shi komai yana nan neat sai tashin kamshi yake yi yasan aikin waye wannan don haka direct daya daga cikin kofofin dake palon ya shige komai na dakin fari ne tas tas sai walkiya yake wayarshi ya jefa akan gado sannan ya wuce cikin closet nashi bai wani jima ba ya fito daga shi sai boxer da kuma kayan da ya cire a hannunshi, bathroom ya shige ya jefa kayan a cikin basket dake kusa da washing machine dake bayin, iya haduwa bayin ya hadu domin mutum zai iya zuba abinci a kasan bayin yaci, komai a cikin yawancin abubuwan da suke bathroom din is computarized, ruwa ya hada a mai dan dumi a baf sannan ya cika shi da shower gel masu dadin kamshi kusan kala uku sannan ya taba tsakiyar katoton mirron dake manne a bango bayin sai gashi wasu abubuwa sun bayyana,
( nidai da na bishi dauko muku rahoto saida na tsorata ganin a take mirror ya zama tv alhalin shigowata nidai madubi na ga ni. lols kar kuce min yar kauye dai)

Remote ya dauka ya canza zuwa tashar da ya ke so sannan ya koma ya shige cikin baff din ya lumshe idanu yana jin dadin ruwan a jikinshi.

Ya kwashe kusan 40 minutes a bayin sannan ya fito daure da towel a kugunshi dawa ni kuma a hannunshi yana tsane ruwan dake kanshi. A tsanake ya shirya cikin wasu kaya na shan iska sannan ya dau wayar shi ya fito palo buba ya samu zaune yana jiranshi, bayan ya zauna ya gabatar mishi da abinci, ba musu ya dauka ya ci, wasu magani buba ya miko mishi , dan kallonshi yayi ta gefen ido sannan yace ” no need” ajiye wa buba yayi domin ba musu a tsakanin su, bayan wani lokaci kadan har an fara kiran sallar magriba buba ya tashi da niyyan tafiya Rasheed ya kalle shi yace “akwai wani dan karamin accident da ya faru akan titin sabon gari don haka ka kula da komai”, ya fada yana yamutsa fuska.

Lokacinda aka iso da habeeb asibiti da gaggawa aka karbe shi aka wuce dashi accident and emergency, banda kuka ba abunda suheer take yi, likitoci manya kusan hudu ne suka rufu akansa, bayan shude war kusan awa daya duk suka fito sun share gumi , daya daga cikin likitocin ne ya kalli suheer da wasu maza biyu da suka rage domin sauran jama’a duk sun watse, yace “waye dan uwanshi a cikinku”, da sauri suheer ta mike da rawan harshe tace gani nan, dan kallonta yayi kana yace”biyoni office” bayan sun zauna a ofishin sanda yadau wasu dakiku yana dan rubuce rubuce a takarda , sannan ya dago ya kalleta yace ke wayen shine ? ya kuke dashi? ganin fuskar likitan kawai yana sa suheer jin wani kuka yana zuwa mata.

Tana share hawaye ta ce “likita ya rasu ko?, take jikinta ya kara tsananta rawa ganin kallon da likitan ke mata, a hankali ya dau hankerchief dake bisa table nashi yana share zufar dake tsatsafo mishi a goshi sannan ya gyara zaman gilashin shi yace “s….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button