AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Tabawa ya ƙira sunanta da azabar karfi wanda yasa ka fareeda sakin sauran fitsarin data riƙe kana ta ƙara damƙe hannu amminta. yace “ki adana wa’azinki domin inna sa abu a gaba ba wanda ya isa yamaidani baya. Ya dubi adama wacce sam ta kasa fahimtar abunda suke tattaunawa a kai yace ” maza wuce ki shirya mutafi yanzunnan .

Fahimtar da tabawa tayi cewa alaji fa yayi nisa bayajin ƙira dole wa’azi kawai bazaiyi amfani ba sai ta haɗa da dabaru irin na mata, har ga Allah bata son a maimaita abubuwan da suka faru a baya a kan sauran matan alaji da suka shuɗe, tana jin adama a ranta tamkar yar uwa bawai kishiya ba, tana da yaƙinin wannan ciki da ke jikin adama shi zai kawo ƙarshen abubuwan da ke daruwa Insha Allah , dole tayi wani abu domin tasan sakamakin irin wannan gwajin baya haifar da ɗa mai ido dalilin irin wannan gwajine aka mata sharrin da har yau bata oya sakewa cikin jama’a.

A hankali tace “tunda baza kaji wa’azi ba ae zaka ji shawara ko? to ayi a hankali kar aje a salwantar da magajin ta hanyar doguwar tafiya, da gargadar hanya, ga kuma dare ya fara shigowa. domin da alama wannan ciki na adama ɗa namiji ne a cikinsa.”

Karo na farko kenan da alaji sama’ila yayi murmushi jin an danganta cikin da namiji.

Yadubi Uwani dake shesheƙar kuka har lokacin yaja gajeren tsaki kana yace ” kuzama cikin shiri gobe asubar fari zamu tafi yola zaki yiwa adama rakiya.” a hankali tace “to ranka ya daɗe”. Cikin sauri mai haɗe da sassarfa ya wuce sashin shi.

Tabawa tayi wani murmushi na samun nasara ta wuce ɗakinta. a bangaren uwani ma ɗakinnata ta wuce cike da ƙunan rai. yayinda adama taja hannun fareeda suka koma madafa domin cigaba da girkin da ta ke na dare.

Lokacin da duhun magariba yayi nisa tabawa ta fito cikin sanɗa ta shiga ɗakin adama ta iske ta zaune tayi tagumi ga kuma fareeda maƙale a gefenta idan ba sani kayi ba zaka ɗauka cewa itace mahaifiyar ta ta haƙiƙa tsabar shaƙuwar dake tsakaninsu, murya ƙasa ƙasa tayi sallama ta shigo ta zauna a gefensu,

Cikin ƙara yin ƙasa da murya tabawa tace “shawara zan baki adama a matsayina na wacce ta girme ki koma ta haifeki zance, alaji ba mutumin kirki bane tun da daɗewa na fahimci hakan sam ba Allah a ranshi kiyi ƙoƙari ki ceci rayuwar ki da na abunda ke cikinki, tabbas kika bari aka je wannan gwaji to ina tabbatar miki bazaki ƙara kwana a duniya ba dake da abunda kike ɗauke dashi zaku baƙunci lahira ne, a ruɗe adama taɗago kai ta kalli tabawa, tabawa ta jinjina mata kai alamun tabbatarwa,( lokaci ɗaya ƙwaƙwalwar adama ya fara aiki ta tuno maganar ladiyo dillaliya, wacce take kawo musu kaya wata rana ta shigo gidan da sana’arta taga adama da katon ciki tace toh ikon Allah kece nagaba kenan.) bayan tafiyar ladiyo tayi iya ta nazarin maganar amma ta kasa bashi gurbin da ya dace ƙarshe dai watsar da batun tayi ta barshi a matsayin munafurci irin na dillalai.

Tabawa tacigaba da faɗin “in akwai wadda kika sani a kasar nan kiyi ta kanki ki tafi wajensu, inkuwa babu kiyi ƙoƙari ki koma ƙasar ku ki nemi sauran yan uwanki nasan baza a rasa waɗanda suka yi saura ba. amma duk yadda za’ayi kiyi dabaran barin gidannan kamun gari ya waye. ” ta miƙe ta fita.

Take adama ta miƙe ba tare da tunanin komai ba ta buɗe wadrobe nata ta ɗauki wani ɗan akwati mai kyau ta dade tana kallonshi sannan ta buɗe a hankali ta zaro abunda ke ciki, zobe ne mai masifar kyau da walƙiya ta zura shi a ɗan yatsanta na tsakiya hawaye masu zafi suna zubo mata tana mai tunawa da mahaifiyarta, kana ta ɗauki hijabi ta zura a jikinta, ta dau wasu yan canjinta ta daure a bakin zaninta ta dawo bakin gado ta zauna tana mai shafa cikin dake jikinta,

A ranta tana ayyana wannan cikin shine duniyar ta shine rayuwar ta bata da kowa a wannan duniya daga Allah sai wannan ciki dake jikinta shikaɗai take shafawa taji daɗi, shikadai ne motsin shi yake sata dariya, sai kuma fareeda a ɗaya gefen. amma ai fareeda ba ƴarta bace a kowanne lokaci mahaifiyar ta zata iya zuwa ta amshi a barta.

Tana zaune har agogo ya buga karfe bakwai na dare ta miƙe tana gyara hijabinta ta nufi kan gado ta gyara wa fareeda kwanciyar ta, ta daɗe tana kallon yarinyan sannan ta juya a hankali ta ɗaga labule ta leka tsakar gidan,ganin ba alamar mutane tasa kanta da niyyar fita kamar daga sama taji muryar fareeda tana faɗin “AMMINA karki barni”. da sauri ta dawo ɗakin ta leƙa fuskar yarinyan abun mamaki baccinta take yi wato mafarki na takeyi cewar adama take zuciyar ta ya karye ba tare da dogon nazari ba ta saɓa fareeda a kafaɗarta suka fice daga gidan.

Kamar walƙiya alaji sama’ila dake zaune a fadarshi nesa kaɗan da mashigar gidanshi, yaga gilmawar mace sanye da hijab da yarinya a kafaɗarta ta jikin gidanshi kamar daga cikin gidan ta fito, har ya basar kuma sai zuciyar shi takasa nutsuwa, ya miƙe yacewa yan zaman fadanshi yana zuwa, da gaggawa ya shiga gidan ɗakin tabawa ya fara leƙawa ya ganta kwance bisa darduma ya fita ya leƙa dakin adama wayam babu adama ba wannan ja’irar yarinyar take zuciyar shi ya shiga hasko mashi matar da ya hango, nan ya hargitsa gidan da nema tabawa da uwani suna taya shi amma ba adama ba labarinta.

Da sauri ya fita ya sanarwa fadawan shi take nan mutum biyar suka miƙe suka bi hanyar da ya nuna musu yaga kamar adama tabi wurin.

Adama kam tunda ta samu ta wuce kofar gida lafiya take ta zuba uban sauri ga dare, ga nauyin fareda, ga kuma uwar ciki da kyar take numfashi amma inta tuna abunda ta baro sai ta ƙara sauri wani zubin ma harda dan gudu gudu har ta fara barin gari taji alamun kamar ana binta bata tabbatar ba saida taji muryar wani daga cikin fadawan alaji sama’ila na fadin “wasu suyi hagu wasu suyi dama”

Wani irin ɗaci adama ta ji a maƙoshinta take afka cikin duhun masara ta ɓuya tana sauƙe numfashi n wahala fareda tayi yunkurin yin ihu domin galabaitar da tayi da ƙarfi ta sa hannu ta danne mata baki. jin ta daina jin motsinsu ne alamun sun yi gaba yaba ta daman cigaba da ratsa duhun masara tana gudu, bata yi aune ba kawai taji ta bugu da wani katon icce tayi taga taga ta faɗi rimmm a ƙasa a tare suka ƙwala wani uban ihu da ya amsa kap jejin ita da fareeda take suka sume a wurin, ihun su yayi daidai da isow………..

Comment Likes and Share.
Comment naku shi zai sa na fahimci ƙaunarku ga labarin.

Follow my facebook group @ Ummu Fadeela Novels.
Bismillahi Rahmanir-Raheem

????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

STORY AND WRITING
BY
ASMA’U MAI ANGUWA
(Ummu Fadeela)

Page 2

……..Wasu kyawawan samari ne su biyu da baza su haura shekara ashirin da takwas a duniya ba, zaune cikin wani tsaleliyar mota ƙirar SVUs a tsakiyar jejin Allah, duk da kasancewar dare ne hakan bazai hanaka ganin tsabar hasken fatarsu ba na jinin fulanin asali, kallo ɗaya zaka masu ka fahimci cewa tagwaye ne, irin tagwayennan da ake kira Identical twins, wanda ke zaune a driver seat ne ya ɗago kyawawan idanunshi ya ɗaura su akan wanda ke zaune gefen mai zaman banza, fuskar shi ya gaza ɓoye yanda ranshi ke bace.

Cikin husky voice yace ” forgod sake AMAAN yanzu dubi abunda ka jawo mana, kaja mun maƙale a tsakiyar jeji, a kan wani banzan baƙin halinka, da yanzu mutum yana kwance yana hutawa amma kasa munbi dare munbar ƴar tsohuwa da shiga uku, ehh shiga uku mana yanzu inta duba taga bama nan mai zai faru kake tsammani ina tabbatar maka bala’in matar nan sai ta tada gaba ɗaya mutanen ƙauyen can, sannan auren ƴar ƙauye tunda ta riga ta fara dole sai mun aura, you know what will be her next action dady zata faɗawa taza ɓamana wasu ƙazaman mata, and dady have no choice than accept maganar ta, duk ma ba wannan ba yanzu yaza muyi ga mota ta tsaya dole sai mun fita mun nemo ruwa kuma banga alamun inda zamu samu ruwa a nan ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button