AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

You manage with dis you guys.. Ina wani uzuri ne…..
Daga page na jiya na fahimci kamar dai Rasheed bai da fansss, haba mana ku kuma super star ne fa???? kar kuma na haka mana.. Ummu Fadeela luv u all a cigaba da sharhi????.
????????????AUREN FANSA????????????
BOOK ONE
STORY AND WRITING
BY
ASMA’U MAI ANGUWA
Ummu Fadeela
Typing????
Page 21 / 22
……Yana gyara zaman gilashin dake fuskar shi yace,” da taimakon Allah munyi nasaran jawo numfashin shi amma yana cikin halin dogon suma, sannan ya samu karaya guda biyu, daya a kafa daya a hannu sai raunin da ya ji akai wanda ya haddasa masa zubar jini but Allah ya kiyaye bai taba wani bangare na kwakwalwar shiba. And now he was still onconsciuos amma any time zai iya farfadowa.
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke sannan tace”Alhamdulillah….. Na gode likita”, likitan ya tari numfashinta da cewa “amma ke wayen shi ce ,? rufe fuskar ta tayi da dogayen tafin hannunta, a hankali kamar mai tsoron magana tace, “his fiancee”, murmushi yayi yace”i see irin wnn rudewa haka saidai fiancee din kam”, dariya tayi sannan ta mike ta fita, dakin da aka kwantar da habeeb ta leka ta kofar glass din dake wurin domin anhana ta shiga, hango shi tayi kwance anzagaye kanshi da bandage, yayinda kafarshi daya da hannunshi daya ke daure shima alamun gyaran kariya. Tana nan zaune har isha, saida likita ya kara dawowa dubashi sannan yace mata yakamata taje gida hakanan sa ta turo babba mai kula dashi inya farfado. Tace “amma likita ni bansan gidansu ba, kuma bani da lambar kowa a danginsa,.
Murmushi dacta yayi sannan yace” toh duk ba damuwa zaki iya tafiya bai kamata ki kwana anan ba, sannan zai kai 24hrs kafun ya farfado by then ki nemo inda gidansu yake sai ki sanarda iyayenshi,” da to ta amsa kana ta kara leka shi still yana kwance sambal dashi kamar gawa.
Gida suheer ta koma tasanar da ammi duk abunda ya faru nan suka jajantawa juna, suheer tace ” amma ammi dole ne wanda ya aikata wannan abu ya fuskanci hukuncin shariya, domin kasancewar shi mai kudi yadau ran talaka kamar ran kiyashi, wato ran talaka bashi da wani amfani da daraja kenan,? mai kudi shine mai daraja? bayan Allah yace “walkaad karramnaa banii adama’, to lallai sai an hukuntashi sai ya zama darasi wa sauran masu hali irin nashi. Ta karishe a dan zafafe,.
Murmushi irin na manya ammi tayi sannan tace kar kisa kanki a abunda bazaki iya ba suheer har kullum al’amuran masu kudi saisu karki shiga abunda zai zo ya juya dake, idan ma kince zaki sa a hukunta shi to ta yaya?kin sanshi ne ko kinsan inda zaki sameshi,? suheer tace “hanyar hukuma, dan na riga da na dau lambar motar shi dan haka gobe in Allah ya kaimu zan kai report police station. Dan Allah kar ki hanani ammi na,ta fada pleadingly.Fareeda dake zaune tana ta karatun script da za ta je audition akai gobe, ta dago kai tace ” eh ammi kibar rabin jiki ta kai kara wallahi ya kamata a koya wa koma waye darasi yadda sauran masu aikata hakan zasuyi learning lessons mai kyau.” Ammi ta gyara zama tana kallon kyawawan yayan nata abun alfaharinta tace” yaro man kaza, bawai ina hanata bane, saidai ganin yadda zamanin ya dawo hukumar yan sandan ma ba al’umma gaba daya suke wa aiki ba saidai masu kudi kawai, amma tunda kindage kije Allah ya miki albarka, shikuma Allah yaba shi lafiya, maganar iyayenshi kuma lamido yasan gidansu yaron zamuyi waya dashi sai ya kwatanta mana.
Wani dariyan jin dadi sukayi sannan suheer tace mun gode ammin mu. fareeda tace ” uhuuumm soyayya ruwan zuma, ni ban gane ba a maimakon ki karya masa zuciya tashin farko sai kika karya masa hannu da kafa, filon kujera suheer ta dauka ta harba mata cafke wa tayi tana dariya wani ta kuma dauka da niyyan jefa mata, fareeda ta tashi tayi daki da gudu suheer tabi ta suna ta dariya,. Dariya ammi tayi tare da share hawayen da ya zu bo mata, har cikin ranta tana jin dadin rayuwar yaran nata.
Washe gari karfe tara na safiya a ofishin yan sanda ya yiwa suheer, kallon juna yan sandan suka yi bayan ta gama karanto musu lambar jikin motar, dan gajeren cikin su ne ya kalle ta yace” yan mata kin tabbatar wannan lambar kika gani a bayan motar?” suheer ta ce “eh yallabai tabbas shine, bayan tukin ganganci ya buge bawan Allah kuma ya gudu sannan ya zage mu , laifuka uku nake tuhumar shi da.
Dariya dan sandan yayi a ranshi yana yaba confidence na yarinyar , a zahiri kuma yace, “tabbas zai fuskanci shariya hukuma zata koya mishi hankali wannan ai take hakkin dan adam ne, karki damu yanzu kije gida, amma kibamu adireshin inda marar lafiyar yake domin muje mu tabbatar, sunan asibitin da lambar daki ta basu sannan ta juya ta tafi zuciyar ta na mata sanyi.
Rasheed…. Tunda buba p.a ya fita yanan zaune inda yake idanunshi lumshe, yana son fita sallah cikin jam’i amma yasan tilas inya sauka yanzu dole ne sai ya hadu da ummie da kuma wannan……. Dan tsaki yaja jin zuciyar shi tana barazanar balle wa daga jikin jijiyarta, a hankali ya mike ya wuce bedroom anan yayi sallar magriba da isha’i gaba daya, wanka ya kuma yi sannan ya dauro alwala domin wannan al’adarahi ce baya taba bacci ba tare da alwala ba, bayan ya fito ya tsane jikinshi, sure ya shafa ba tare da ya bi ta kan man shafawa ba, sannan ya fesa body spray masu dadin kamshi , ya matsawa bakinshi mouth spray mai strawberry flavour, kana ya wuce closet nashi wani bangare ya bude, pyjamas ne jejjere a wurin tamkar kantin su, wasu masu kalan sky blue riga da wando ya fitar yasa sannan ya dawo dakin ya bude firji ya dau fresh milk mai sanyi tsakiyar gadonshi ya hau ya jawo laptop nashi ya bude yana aiki yana sipping fresh milk, har ya fara jin bacci kafun ya ture laptop din gefe ya ajiye sauran milk a kan bedside, sannan ya kwanta yayi addu’a ya shafa, har ya rufe ido kuma sai ya bude ya tashi da sauri kamar wadda ya manta wani abu drawern bedside din ya bude sannan ya zaro wani abu a ciki ya fitar, hoto ne ya kai tsawon minti biyu yana kallon hoton wani dan guntun hawaye mai dan karen zafi ne ya gangaro ta gefen idanunshi guda daya yayinda idanun suka yi jajawur jijiyoyin kanshi suka fito rudu rudu, how he wish zai iya yin kuka, zuwa can ya kifa hoton saman kirjinshi yana jin zuciyar shi na mishi nauyi.
Washegari misalin tara na safiya ya sauko cikin gayu kamar kullum yauma sanye yake da kananan kaya da kuma p-cap mai dauke da tambarin tauraro a gabanshi wanda akayi da zallar gwal, sai zuba kamshi yake kamar yaci karo da motar turare a hankali yake taka steps din har ya sauko karshe. Zaune suke a kan tebur suna breakfast wani dattijone da kuma wani dan saurayi zaune, sai kuma ummie dake tsaye da serving spoon a hannunta.
Da sauri tace” son ga breakfast karka fita baka ci komai ba kaga haka jiya ma baka yi dinner ba, plsss ka ci wani abun”, ko ci kanki baice mata ba saima nufar kofar fita da yayi, dattijon dake zaune ne yace” aikin kawai haihuwan asara yaro dai kamar shaidan uwarka na maka magana bazaka tanka mata ba.
Har Rasheed ya kai kofa ya jiyo maganar shi, a fusace ya juyo takowa yayi gabansu cike da izza sannan ya nuna mutumin da yatsa yace ” mind your business you fool, karka manta nan a gidana kake ba gidanka ba, so maintain your dignity if not…… Yaja wani kwafa yayi gaba abunsa, kallon ummie alaji umar yayi sannan yace” kedai kin haifi jaraba tunda baisan darajar ki ba balle na ubansa, ai inda daraja ni ubansa ne ya kuma jan tsaki ya tashi ya haura sama, kuka ummie takeyi sosai itama ta wuce kitchen dan saurayinne yaja tsaki yade da mikewa yace ” duk ya bata mana mood ya tafi, shima wucewa yayi nan suka bar abincin ba wanda yaci.