AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fitowar Rasheed yasamu buba p.a zaune cikin shiri ga direba ya fitar da mota ya goge ta sai walkiya take tana daukan ido, bude mishi motar yayi cikin takun kasaita ya shige suka nufi location domin yau akwai shirin daza su dauka, lokacin da suka iso anriga angama shirya komai shi kawai ake jira dama a hakanma ya bata musu lokaci amma ba yanda directorn ya iya saidai shiru, fitowa daga motar yayi walking slowly as super star he is, mutane suna ta daga mishi hannu da ambaton sunanshi.
Maimakon ya wuce a fara daukan shirin tunda angama shirya komai sai kawai ya wuce karkashin wani kyakyawan rumfa irin na zamani mai dauke da wasu kujeru masu daukan hankali, zama yayi hade da daura kafa daya kan daya yana karkadawa, ganin haka yasa wani ma’aikaci yazo da gudu yana tambayarshi “yallabai me za’a kawo?,buba p.a ne yace panecake with black tea, sanin cewar boss din nashi ba lallai yayi magana ba. Abunda aka umurce shi ya kawo, bayan ya kammala breakfast dinne ya kalli buba yace” akwai magana a bakinka”? da rawan harshe yace eh boss akan maganar accident da ka samu jiya ne dazu inspecta ya kirani, yace wata yarinya taje ta shigar da kara a ofishinsu kuma lambar motar ka ta bayar sannan tace tana so……… Sai kuma yayi shiru, kara murtuke fuska rasheed yayi yace” uhmm go on” tana son a hukunta ni ko tana son a rufe ni a cell right?. Ya fada yana dage gira sama.
Da sauri buba yace” karya take yi ae boss kai kafi karfin shiga cell akan wani banza can talaka, miskilin murmushi rasheed yayi sannan yace.” wacece yarinyar?, da sauri buba ” boss ba fa wata bace she is just d eye witness,akan idonta abun ya faru.
Tashi rasheed yayi yana wani rangaji kamar reshen bishiyar da ya ji iskan damuna, matsowa yayi kusa da buba sannan cikin miskile fuska yace “Buba waye ne idan babu shi masana’antar kallowood bazai tafi daidai ba? da sassarfan harshe buba yace,”kaine boss” rasheed yace nine wa? buba yana murmushi yace” RASHEED MATAWALLE”, Kuma murtuke fuska yayi yace,” so kama rasheed da hukunta shi tamkar girgiza KALLOWOOD ne kuma hakan ba abune mai wuya ba so stop being so tensed ok? now smile, ya fada yana kama gefe da gefen kumatun buba, buba yayi murmushi yace “ai yanzu haka ma murmushi nake yi boss,.” Good boy” cewar rasheed, yaci gaba da cewa ina son ganin inspecta abu daya kawai zai aikata zaka ga gobe yarinyar tazo nan tana cewa plsss raaheed nima ka karya min kafa da hannu indai zan samu irin wannan, ya karishe yana munafikin murmushi, but deep down yana jin zuciyar shi na tsananta kuna, yana yin murmushi ne kawai domin ya samawa kanshi farin ciki,.
Suheer, tunda ta bar ofishin yan sanda asibiti ta wuce kai tsaya, luckily ta tararda habeeb ya farfado, dukda yana jin jiki sosai hakan bai hanashi aro jarumta ya mata murmushi ba, itama murmushin ta mayar masa tace ” habeebi sannu kaji Allah yabaka lafiya Nakai kara ifishin yan sanda Insha Allah sai wanda ya aikata maka wnn abun ya fuskanci shari’a, cikin tsananin ciwo yace why suheeer? me yasa kika yi involving police a ciki? tace domin su fahimci ran talaka ma raine, so keep shut plsss karka ja ciwon ya kara yawa bari indubo likita.
Tana fita wasu mutane uku suna shigowa babbar macece da kuma dattijo sai wata yar budurwa da baza ta haura shekara 22 ba, ba laifi talakawa ne, dan daga suturar dake jikinsu zaka fahimci hakan.A rude suke dan fuskokin su ya bayyana hakan, kallon matashiyar kyakyawar likitan suka yi har suna hada baki wurin fadin” dacta ya jikin habibun?” sunne kai kasa suheer tayi tace sannunku da zuwa nice na kawo shi yanzu ma dactan zanje in kira dan ya farfado, ku shiga ku ganshi”, sannan ta wuce duk kunya ya kamata dan kallo daya ta fahimci iyayen habeeb ne, da kallo asabe mamar habeeb ta bita, a ranta tana yaba wauta irin na habeebu, in banda sa kai a uku ina shi ina zukekiyar yarinyar nan mai siffar larabawa hmmm, ta shige dakin da sauri tana matso guntun hawaye.
Lokacin da inspecta ya amsa kiran da buba yamasa ya sanar dashi cewa boss yana neman sa, a take ya garzaya inda ya sanar masa zai same su yana ta washe hakora kamar gonar auduga dan yasan yau kakarsa ta yanke saka, isowarshi yayi daidai da gama daukan shirinsu na lokacin sai kuma daukan dare ya rage, don haka dakin hutunshi rasheed ya wuce, wanka yayi ya sanya three quater wando da wani riga armless yazo ya zauna ya harde kafafu wanda hakan kamar dabi’ar shi ce, buba ne yawa inspecta jagora zuwa ciki bayan boss ya masa izini, da sallama ya suka shigo a cikin ranshi ya amsa idanunshi a lumshe, inspecta yace ” barka dai yallabai, wato daga ganin alama yarinyar zata yi wuyan sha’ani domin ta dage lallai sai an kamo wanda ya aikata wannan laifin an hukunta shi, ba tare da tasan cewa da wa take fada ba, amma karka damu ranka ya dade nasan maganinta ka bar komai a hannuna. Ya karisa yana shafa katon tumbin shi.
A hankali rasheed ya bude idanunshi ya sauke su akan inspecta cikin yamutse fuska kamar mai shirin yin amai yace yana nuna tumbin inspecta din ” wnn kadai ya’isa yasa ta maka wuyan sha’ani ai don haka zo in nuna maka hanya mafi sauki na rage wnn tumbi”, ya fada gami da mikewa ya taka tsakiyar dakin sannan ya kwanta filat a kasan tattausan carpet din da ke dakin sai kuma a hankali ya daga jikinshi yazama iya babbar yatsar kafar shi da kuma hannayenshi ne a kasa, press up ya fara da sauri sauri guda goma yayi a cikin second goma, sannan ya dago ya kalli inspecta dake ta faman yaken dole yace oya matso muyi dariyan yake ya kuma yi, yace ” ranka ya dade wnn sai kai ai,” mikewa yayi yace” eh tabbas sai ni” buba ya kalla yace ” me ne ne kudi bazai iya saya ba a duniyannan?” buba yace eh to gaskiya basu da yawa boss abu kadan ne kudi bazasu iya s……. Kafun yakai karshe rasheed ya dakatar da shi ta hanyar cewa “wrong wrong, RASHEED MATAWALLE ne kawai kudi baza su iya sayaba, ” da sauri buba yace gaskiya ne wannan boss, kai kadai ne kudi baza su sayaba.”
Duban inspecta yayi kana ya dauko cheek yayi signing blank, ya mika mishi yace ka nemi danginshi ka basu su cike ko nawa suke so,sannan ka biya hospital bill nasan baza su kara bi ta kan yarinyar ba bare kuma case din.
Da rawan jiki inspecta ya karba cikin hanzari yabar location din farin ciki fal zuciyar shi, bai zame ko’ina ba sai asibitin da suheer ta kwatanta mishi, direct room numban da ta fada mishi ya nufa.
Lokacin da asabe da malam mamman da kuma kanwar habeeb mai suna maryam suka shiga dakin, kuka asabe ta dashe da, tana sharbe majina tace “wayyo sun kassara min rayuwar yaro dama shi kadai ne mai taimakonmu uban da shi da babu duk daya, yanzu ya zanyi da raina, wayyo Allahna ta daura hannu aka, maryam ne ta ce “haba mama ki dena abunda kike yinnan mana,nanfa asibiti muke dan Allah ki bari haka sai ki kara masa ciwo ae, dame zaiji,? ” ke dallah can rufe min baki sakaryar yarinya kawai,ina ce tsabar mutuwar zuciya irinna ubanki yasa har yau ankasa aurar dake, kudin gado da katifa kawai ya gagareshi, mai kukutawa ya kawo mana abincin kuma gashi an kassara min shi, kuma shine dama mai kokarin rufa mana asiri a samu a aurar dake, shiru maryam tayi, tsabar masifar asabe, mamman dai bai bi ta kanta ba, don bazai yarda su raba hali da ita ba, gadon ya nufa yana kallon habeeb dake kwance baya iya motsi mai kyau, ga hayaniyar asabe tana kara masa ciwon kai sannu ya masa kana yaja kujera ya zauna,kanshi ta karaso tana matsar wasu kwallan tace ” sannu kaji babana, Allah ya bima hakkinka, dayan hannu mai lafiyan ya daga mata sannu maryam ta masa.