AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani yace ” hajiya tunda taki fada mana ko zaki ari bakinta kimana bayanin yadda accident din ya kasance, da kuma yadda ta shigar da kara ofishin yan sanda?.
Wanne ofishin yan sanda ta kai karar ?.
Sannan wane dan sanda ne ya karbi case din?.
Wani irin ajiyan zuciya hafsa ta sauke jin ba akan abunda ya faru a wurin audition ne ya bazu a duniya ba, amma kardai ace rasheed ne wanda ya kade saurayin suheer?.
Goshinta ta dan shafa sannan ta dago ta kalli inda yan jaridar suke kowannensu ya daga abun daukan muryar shi yana jiran ta bada amsa ya samu na yadawa duniya.
Hade rai tayi sannan ta fara masifa kamar yadda ta saba hadi da musu korar kare, sannan ta juya zuwa cikin palon ta garkame kofar, da sauri fareeda ta taso ta zo wurin ta hannunta biyu ta rike hawaye na silalo mata tace, ” me suka ce anty? yace bazan shiga fim din bako? shafa bayanta tayi tace”karki damu ba akan maganar bane, saurayin suheer dake asibiti rasheed ne ya buge shi da mota, a tare fareeda da ammi suka dago kai suna jiran karin bayani,
Rasheed na zaune a hadadden palonshi da banda kamshi ba abunda ke tashi ciki, (Rasheed akwai tsafta da bala’in son kamshi, yana iya kashe ko nawa ne akan siyen abu mai kamshi, shiyasa koda yaushe yana cikin kamshi idan ya tashi a wuri yana kai tsawon minti talatin kamshinshi na manne wurin.) idanunshi lumshe suke, idan ka ganshi zaka dauka bacci yake, amma idanunshi biyu banda tunani ba abunda yake yi sau tari yakanyi mamaki,idan yayi murmushi, anya dariya ya cancanta da mutum kamar shi kuwa? anya watarana zai dawo ainahin Rasheed nashi na asali, kafun faruwar abunda ya faru shekarun baya? abunda ya tarwatsa rayuwar shi gaba daya, ya maida shi mugu mara tausayi.
Buba ne ya shigo waya kare kunnanshi, yana magana da dan fada fada, “haba jama’a har cikin daren ma bazaku bar mutane su huta ba, ku kam wadanne irin mutane ne haka da shegen jaraban tsiya?, na fada muku boss rasheed ba zai iya magana da kowa ba a yanzu, don haka a katse kiran yanzunnan,……….Dan yunkura wa rasheed yayi jin muryar buba, remote ya janyo ya kunna tv, daidai ana haska wani shiri LIVE a gidan tvn dayake yawan kallo, ji yayi mai gabatar da shirin yana ta ambatan hello, hello, hello. “kana magana ne da gidan tvn AMINCI kuma shirin kai tsaye ake gabatarwa,” da mugun sauri buba ya sauke wayan daga kunnenshi yana ambatan gidan tv kuma?, “Eh “mai gabatar da shirin ya kuma ambata, kiit buba ya kashe wayan yana zare idanu, rasheed dai sai kallon mai gabatar da shirin yake kamar mai son ganin wani abu a fuskar shi,.
Dan muskutawa dan jaridar yayi sannan ya dubi wanda suke gabatar da shirin tare yace “me zaka iya cewa akan abunda rasheed ya aikata.
na farko yayi tukin ganganci, sannan ya buge mutum da rana kuma a idon mutane sannan ya nuna halin ko inkula ta hanyar tafiya ba tare da ya tsaya ya duba abunda ya aikata ba.
Godiya yayi da wannan tambayar da aka mishi sannan yace” wannan ya na nuna mana yanda doka da oda bata aiki akan wasu shafaffu da mai a kasar nan, abunda Rasheed Matawalle ya aikata da wani talakan ne da tuni yana gidan yari yanzu haka, amma da shike shi wani ne sannan yana takama shi dan wani mai hannu da kumbar susa ne kaga ae ba wani matakin daza’a dauka akanshi,. Wannan shine tsarin da kasar nan ta dade akai mai kudi baya laifi sai talaka, ko kasan cewa ana daure barayin kaji ko awaki a prison ?amma masu satan miliyoyin kudi sunanan suna shakatawa,
Saboda me?” cewar mai gabatar da shirin, dan murmushi bakon nasu yayi yace saboda su wasu ne, saboda suke mulki, don haka sai yadda sukayi damu, yayinda a bangare guda mukuma talakawa rashin sanin hakkinmu sautari da kuma kwadayi shi ya ke kaimu ya baromu.
“yanzu me kake fatan ganin hukumomi sunyi akan wannan al’amarin?”
Wannan abune mai sauki, kuma nasan jama’a da dama zasuyi maraba da shi, kawai hukumomi su kama Rasheed su gudanar da bincikensu akanshi amatsayin sa na dan kasa,bawai a matsayinsa na superstar ba ba kuma a matsayinsa na dan wani da ya kasance jigo a kasar nan ba, idan an same shi da laifi a mika shi kotu, kotu kuma ta yanke masa hukunci daidai da laifinsa wanda hakan zai zama darasi ga yan baya, dama shi kanshi rasheed din,.
Zumbur rasheed ya mike daga zaunen da yake ya fara safa da marwa a palon hannunshi harde a bayanshi, wani zufa ne ke karyo masa, calming kansa yake sosai dan yasan in ya biyewa zuciyar shi zai pasa komai na dakin. yana cigaba da zagaye palon , buba na gefe a tsunbure kamar akuyar da ruwa yai ma duka sai yan idanuwa yake zarewa.
“A wanne mataki zaka sa ita yarinyar da tayi kokarin ganin an hukunta rasheed?”
To a gaskiya dai wannan yarinyar tayi namijin kokari, da’ace zamu samu jajirtattun matasa kamarta da al’amura masu yawa sun mana sauki a kasar nan, duk da kasancewar shi tauraro, kuma wanda mata suke rububi, gashi yayi nasaran abubuwa da yawa tunda kuruciyarshi amma hakan bai rude ta ba ita dai burinta abiwa wanda aka zalunta hakkinshi, tabbas ni a wurina ta cancanci samun lambar yabo.
Madallah muna godiya daka samu halartar wannan shiri har ka tofa mana albarkacin bakinka, “nima nagode .” cewar bakon. Juyowa mai gabatar da shirin yayi yana dan murmushi yace “nasan mai sauraro zai so sanin wannan yarinya wacce ta rikita rasheed matawalle a cikin kwana daya kacal to ku gyara zama domin kallonta,. Ya fada yana nuna wani majigi dake gefensa.
Rumtse idanu rasheed yayi daidai lokacin da ‘aka hasko fuskar fareeda wacce yan jarida suka dauka tana tsaye bakin kofa,. Kallonta kawai rasheed ke yi ko kiftawa babu yayinda zuciyar shi ke saka masa abubuwa marar adadi.
Wani irin zabura buba yayi yana nuna fuskan fareeda da har yanzu yake gaban akwatin talabijin din, kana yace boss wannan ai itace wllh itace, wato fansa tazo dauka, tazo audition din fim naka wanda ake kokarin dauka so sai muka dan samu sabani domin ta kasa abunda ake bukata shine antynta ta tada hayaniya nikuma na gaggaya musu magana wallahi yanzu fansa ta zo dauka .
matsowa kusa dashi rasheed yayi idanunshi sunyi jajawur kamar garwashin wuta yace “inason sanin komai akanta nan da safiya i mean everything,……..” yes boss” inji buba da sassarfa ya fita. rasheed ya koma ya zube akan kujera yana dafe kanshi, a bayyane yace” SUHEEEERR” wani murmushin da shi kadai yasan manufar ta yayi sannan ya koma ya jingina da kujerar hadi da rufe idanunshi ruff.
Jugum jugum suheer ta samu yan gidan lokacin da ta dawo daga sayan biredin da ammi ta aiketa, a hankali ta karisa shigowa ta ajiye ledan ta iso kusa da fareeda dake aiki kuka tace “whats wrong sweetheart?” rungumeta fareeda tayi tace” Rabin jiki, rasheed shine ya kade habeeb da mota , rasheed shine wanda kika shigar kara police station, suheer tace uhmmm meya faru toh, wani kallo fareeda tabita dashi tace ” sweetheart rasheed fa wanda nake son fitowa a fim nashi, ” anty hafsa ne ta matso ta kama hannun suheer ta ajiyeta akan kujera sannan ta tsugunna a gabanta tace” bari inbaki wani dan dabara suheer tashi zakiyi muje gidan rasheed tunda nasan inda gidan yake sai ki bashi hakuri sannan muje police station kiyi withdraw din case dinnan shikenan,” da sauri fareeda tace yess, it will be better.