AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da mugun mamaki suheer take kallon su sannan tace “akan me?”. fareeda ta ce da zaran rasheed ya kalli tv shikenan nawa ya kare bazai taba barina in fito a cikin film ba, kama hannunta hafsa tayi tace suheer tashi mu je da wuri kar dare yayi sosai, mikewa suheer tayi tace ” ba inda zanje accident dinnan a gabana ya faru ba abunda ban gani ba so abunda nakeson yi yanzu shine inga an tabbatar da hukunci akan wanda aka zalunta .

Damqo hannunta fareeda tayi tace don’t talk rubbish sweetheart, shin baki damu da cikar mafarkina da kuma burina ba ne, tana magana har hawaye ya fara wanke mata fuska kamar kullum? jijjigata tayi tace “kiyi magana mana” anty hafsa ne ta kariso wurinsu ta janye fareeda, sannan ta kalli suheer cikin muryar lallashi tace ” ki saurane ni da kyau, bakisan hakan damuwa bane in burin yar’uwarki ya kasa cika sabida ke?.

Suheer tace “amma anty hafsa ta ina hakan zai shafi burin rabin jiki? in Allah ya kaimu gobe zan sanar da kowa cewa ba ita bace nice,. Da sauri fareeda tace”daga zaran kin sanar da hakan rasheed zai san cewa wannan yarinyar da ta shigar da kara akan shi kanwata ce uwa daya uba daya, and tha’s d end of me?

Anty hafsa tace karki zama irin yar uwar nan mana suheer wacce zata bata farin cikin da goben yar uwarta, suheer tace and how about habeeb accident? shima dan uwan wasu ne dan wasu, kuma yayan wasu.

Fareeda tace akan habeeb ne kike kokarin bata min shiri na na tsawon shekaru? girgiza kai suheer tayi tace ba ‘akan habeeb bane akan adalci ne,try to understand me plss sweetheart, koma takan waye adalci ya biyo zan so inga an aikatashi. koda kuwa rasheed dinne, i will bring him to justice.

Matsowa ta kuma yi kusa da fareeda ta rike kafadunta cikin kwantar da murya tace ” plsss sweetheart let meet with rasheed and…….. Katse ta fareeda tayi tun bata kai aya ba cikin tsananin fushi da daga murya irin wanda suheer bata taba sanin yar uwarta na da shi ba sai yau tana nuna ta da yatsa tace,” don’t talk about rasheed again, tell me clearly, what’s your final decision?.

Suheer tayi gathering courage tace my final decision is not to withdraw the case, amma gobe da safe in……. hankada ta fareeda tayi, sannan ta juya a fusace, taga taga suheer tayi saura kadan ta dadi kasa ammi da tayi mutuwar tsaye a wurin tana mamaki don bata taba ganin yayannata suna fada ba sai yau akan wani banzan da basu sanshi ba, saurin riko suheer da ta kusa faduwa tayi,

Fareeda ta juya a fusace ta fara jifa da duk wani abunda ta gani a palon jifa take yi dashi tana kuka, dukkansu kanta suka nufa suna mata magana, amma ba wanda ta saurara sai maka abubuwa take a kasa da gyar ammi tayi nasaran kamata, fadawa tayi jikinta tana cigaba da kuka, ammi tace ” me kike yi haka fareeda zaki jima kanki ciwo fa! dagowa fareeda tayi idanunta sunyi jawur tace” ammi wani ciwon kaddara ne, amma wani ciwon dan uwanka wanda kafi kauna fiye da komai shi yake jawo maka shi. ta fada tana nuna suheer da dan yatsanta,. Dum dum dum haka kirjin suheer ya buga, da sauri tace sweetheart, katse ta fareeda tayi da wani mugun karar da sai da illahirin gidan ya amsa tace “don’t sweetheart me” ba karamin tsorata dukkansu suka yiba jin irin shouting din da fareeda tayi, abune da bai taba faruwa ba a tsakanin yan uwan biyu.

Fizgewa fareeda tayi daga jikin ammi da iya karfinta ta nufi kan fridge inda ta hango wani wuka zaune yana ta walkiya da gudu ta iso ta dau wukar ta rike shi gam hawaye yana ta malala a idanunta, gaba dayansu suka nufe ta da niyyar kwace wukan amma sun kasa, suheer tana kuka tace a’a sweetheart no…don’t.. wani ihun da ya fi na farko fareeda tayi sannan tayo kan suheer rike da wukar, tace” kin riga da kin karbi rayuwa ta rabin jiki, do haka…………”
????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

     NA 

Ummu Fadeela

Typing????

Page 26 / 27

Fareeda tace ” don haka ba kashe kaina zanyi ba domin kin riga da kin karbi rayuwa ta daga wurina, karku damu dukkan ku”, wucewa tayi inda ta hango wani cucumber da plate akan kujera da alama ammi ne ta ajiye zata yanka, dauka tayi tazo ta zauna ta fara yankawa kat,kat,kat kawai kake ji akan plate din,da sauri sauri take yankawa bata ganin gabanta, kanta suka kara dawowa dukkansu uku,kowa da abunda yake fada mata don lallashi amma taki sauraran su, da fada anty hafsa tace me kike yi haka ne fareeda zaki ji wa kanki ciwo fa, dariyan takaici fareeda tayi sannan tace, ” wannan abunda nake yi shine abunda yadace dani tunda dadewa ban fahimci hakan ba, girki, kula da gida, wanke wanke, shara, da sauran aikace aikacen gida wannan shiya kamata inkoya daga nan sai ammi tamin aure, wannan shine abunda yadace da rayuwa ta ba mafarkin zama jaruma ba,.matsota suheer tayi zata yi magana kenan, wukar ya yanke fareeda katttt akan dan yatsanta, take jini ya fara zuba, ajiye wukar tayi yayinda suheer ta kama ta tana kallon hannun tana fada,.

“Yanzu me amfaninshi kinjiwa kanki ciwo a banza duba kiga yadda jini yake zuba ina dalili?” kallon ta fareeda tayi calmly tace ” kinga wannan ciwo da naji, ta daga dan yatsarta dake digar jini, bana jin zafin shi kamar yadda nake jin zafi a zuciya ta, wanda kuma kece silar wannan zafin na zuciya ta, ban taba tsammanin zaki min haka ba, koba kece kwannan baya kika roki ammi ta barni incika burina nason zama jaruma ba, ohk ammi ta barni sai kece zaki kasa, hadda hannayenta tayi wuri guda tace thank you so much rabin jiki, ta juya ta fice daga gidan gaba daya, kokarin bin bayanta suheer tayi, anty hafsa ta kamo ta tace” na rokeki suheer, kibar ta ta huta tunda kin nuna soyayyar saurayinki wanda da haduwar ku baifi wata daya ba yafi cikar burin yar uwarki wadda tafi shekara goma sha takwas tana mafarkin zuwan shi, kin zama muguwar yar uwa, idanu suheer ta zaro jin abunda anty hafsa ta fada.

Ammi ne tace me kike aikatawa haka hafsa? meyasa ke kullum kike nuna kinfi supporting fareeda?, yarannan dukkansu yayanmune, sannan dukkansu ba wanda yayi laifi kowa akan gaskiyar shi yake magana, zama ya kamata muyi dasu ayi solving problem dinnan bawai ki kara ingiza su ba.

Wani shegen kallo anty hafsa ta yi wa ammi, sannan tace Adama kenan wannan shine abunda kika gani ta bangaren ki, amma ni a nawa bangaren wannan mugunta ne, ta fada tana nuna suheer da yatsa,fuuu ita ma ta fice daga gidan gaba daya.

Fadawa jikin ammi tayi ta fashe da wani marayan kuka, tace” yanzu ammi laifi ne dan nayi kokarin ganin anyi justice wa wanda aka cuta? ashe sweetheart bazata bani goyon bayan abunda nake kokarin aikatawa ba saidai ta zarge ni ? me laifi na ammi ? me na yi dana cancanci haka daga gareta”? ammi tana shafa bayanta tace” baki yi laifi ba yata, abunda kika aikata daidai ne, yar uwar ki kuma zata sauko kibarta ta sha iska kadan zaki ga kamar ba ita ta miki shouting dazu ba, wannan gado tayi gadon wannan halin tayi a wurin mahaifinku, amma abunda nake so dake yanzu karki zafafa akan case dinnan, sannan……….. Tsawon 20minutes ammi tana bata shawarar abunda yadace tayi, koda fareeda ta fita wani dan dakali dake wajen gidansu ta hau ta zauna ta ringa kuka harta godewa Allah, batare da ta damu da masu tsayawa kallonta ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button