AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari rasheed na wurin motsa jikinsa as usual sanye yake da three quater da armless, wanda da alama sune irin kayan dafi sanyawa a gida, buba ne yazo da bayanin da rasheed ya ce ya nemo masa akan Suheer, wasu private investigators buba ya biya domin suyi masa aikin, saida yagama abunda yake kana buba ya fara masa bayani da cewa ” boss yan matan su biyu ne ashe yaya ce da kanwa fareeda lamido da suheer lamido kamar yadda suke amfani dashi, fareeda itace babba kuma itace tazo wurinmu audition, sai suheer itace karama kuma itace eye witness na accident din, matsalan da aka samu shine yan jaridar ba hoton suheer suka nuna ba hoton fareeda ne, sannan sunan lamido ba shine ainahin sunan babansu ba……..nan buba ya warware wa rasheed komai game da rayuwar yan uwan tunma ba’a haife suba sai da masu binciken suka bincikowa buba, shikuma yakawowa uban gidansa,.
Wani irin murmushin da ya bayyana kyawawan hakoranshi rasheed yayi, kana yace da buba ” ina bukatan ka hada min conference da yan jarida a cikin lambun gidannan”, da” to” buba ya amsa kana ya fice da sauri domin cika umarnin boss dinnasa. Bayan fitar buba kwanciya rasheed yayi hadi da lumshe kyawawan idanunshi yana cigaba da murmushi a hankali jajayen labbansa suka motsa yace ” Suheeer, wow i really like the game.
A bangaren suheer kuwa sosai ta dauki shawaran da ammi ta bata, har lokacin kwanciyar su bacci yayi bata ga fareeda ba, hakan yasa ta yi shirin kwanciyar ta ita kadai ta kwanta a gadonnasu duk yadda taso bacci ya dauke ta hakan gagararta yayi, tunani take yi sosai na irin rayuwar su da yar uwarta, gashi rana tsaka wani ya shigo zai tarwatsa musu farin ciki, ko ina ta shiga yanzu? tuna hakan yasa ta mikewa da sauri ta fito palon ammi ta gani tana kokarin bude fridge, cikin raunin murya mara karsashi na alamar wadda yasha kuka tace “ammi har yanzu sweerheart bata dawo ba fa,” dagowa ammi tayi tace “karki damu ta dawo tana dakina jekiyi baccinki zata shigo anjima, simi simi haka ta koma ta hau gado ta kwanta, tana ta tunanin lamido, da ace yananan yanzu da duk haka bai faru ba, ko sai yaushe zai dawo,? da wannan tunani bacci barawo ya saceta.
Lokacinda suheer ta farka da asuba kwance ta samu fareeda gefenta kamar yadda suka saba kwanciya, a hankali ta tasheta domin suyi sallah, bata musa mata ba suka fita suka dauro alwala nan cikin dakin suka dawo suka gabatar da salla, sunanan zaune suna azkar har gari ya fara wayewa, a hankali fareeda ta tashi ta hau saman gadon ta kwanta domin wani irin ciwo kanta ke mata, lulluba tayi da bargo ta lumshe ido a haka bacci ya dauke ta, tunani Suheer take yi na me ,ai faru idan taje gidan rasheed da sunan bashi hakuri, tabbas badon ammi ne tasa ta ba baza ta taba janye wannan karar ba. Mikewa tayi ta nufi kitchen nasu, anty hafsa ne tsaye tafara hada musu breakfast don yau dutin ta ne, kamar yadda suka saba suna shiga ayi girkin tare dasu, kallo daya ta mata ta dauke kai, gaisuwanta ma sama sama ta amsa mata, haka dai suka gama girkin ba wani annashuwa tattare dasu kamar baya.
A gaggauce suheer ta kimtsa, bayan sun gama cin breakfast sunyi wanke wanke, fitowa tayi sanye da wani turkish abaya grey colour wanda yasha stones sai walwali yake yi, ta tubke uban gashin kanta wanda inba saninta kayi ba zaka ce attachment tasa ka, ta yane kanta da mayafin rigar, babu kwalliya ko digo a fuskarta sai dan lip gloss da ta gogawa lebenta,lumsassun idanunta farare tas sun dan tasa saboda kukan da tasha jiya, jikinta na tashin wani sanyayyen kamshi, domin tana amfani da turare kusan kala biyar, ne saika rasa gane wani kalar kamshi takeyi saidai kamshin mai daukan hankali mutane ne ,musamman ma’abota son kamshi, kafar ta sanye cikin flat shoe bakake masu kwalliyan stones farare sol sai kyalkyali suke yi,kasancewar ta doguwa bata amfani da dogon takalma, bata dauki komai ba sai wayanta da kudin adaidaita daza ta shiga yakaita gidan rasheed daga nan ta wuce asibiti duba jikin habeeb,. a palo ta sami ammi tace,” ammi zan wuce sai na dawo idan sweetheart ta tashi kice mata na fita dan har nagama shiri bata farka ba,” ammi tace ” to amma ki kula da kanki sosai kinji ko allah ya muku albarka baki daya” “ameen” tace sannan ta fita gidan tana taku daidai wanda yanayin hallitar tace hakan, har ta isa bakin kwalta ta tsaida napep ta kwatanta mishi inda zata.
Lokacin da suheer ta sauka a kofar gidan rasheed kwankwasa kofar tayi mai gadi ya leko da kanshi ya mata kallon tsaf sannan ya bude mata kofar ta shiga tana karewa wurin kallo sannu tayiwa mai gadin ya amsa sannan tace “wurin Rasheed matawalle nazo, kozan samu ganinshi?, mai gadi yace “eh kishiga suna can cikin lambu da alama yau taron gaggawa sukeyi a gidan,. Suheer tace ” ammm dan Allah kayi hakuri ta ina lambun yake ban taba zuwa gidan ba sai yau, kwatan ta mata yayi yace amma tafiyar da dan tazara, tace “ba damuwa na gode” kana ta mike hanyar daya kwatan ta mata a ranta tana cewa ba dole ya taka kowa yanda ya so ba a ce cikin gidama kwance da kyakyawar kwalta irin wannan amma anbar talakawa suna shan wahala, ita kadai take magana tana tafiya,
Sannu a hankali Rasheed ke takawa fitowar shi kenan daga main house zai nufi garden inda taron yan jarida ke jiranshi, taku yake yi kamar baiso yana sanye da bakin wando mai dan fadi kadan da farar riga wanda aka rubuta HANDSOME a gabanshi da kalar baki, yana sanye da p-cap shima baki mai tambarin star a gabanshi, zuwa yanzu na fahimci wannan star din kamar sign nashi ne duba da dukkan p cap dayake dasu suna dauke da tambarin kuma da gwal ake yinsu,. kafafunshi sanye cikin wasu kyawawan sneakers suma farare , hannunshi sanye da agogon diamond iyama fara sol,sai baza kamshi yake yi yana tafe buba na binshi a baya rike da tarin wayoyinsa, a haka suka kariso cikin garden din,.
Taron yan jaridar suka mishi caaaa da tambayoyi daga isowar shi, sir mezakace akan yarinyar da ta shaida lokacin da komai ya faru?,
Daga musu hannu yayi kana ya iso ya tsaya yace dukkanku ku zauna plssss nasan tsoron ku shine kar a kama Rasheed a kulle shi a kurkuku right? to na muku alkawari ba wanda ya isa yakama Rasheed a kap fadin kasar nan babu shi, wannan maganar da yake, yayi daidai da isowar Suheer wurin, ido ta runtse ta sake budewa jin yaci gaba da magana, yace “banga labarin da gidan tv suka yada mai kyau ba shin kozaku iya fada min me ya faru,?” wata daga cikin yan jaridar tayi saurin cewa akan maganar accident ka buge mutum kuma ka gudu,”
Rasheed yace a ina abun ya faru?, wata ta kuma cewa kan titin sabin gari”, murmushi buba yayi a ranshi yace what a sharp guy, maimakon shi zai basu amsa, amma shine mai tambayar,.
Rasheed yakuma cewa wacece taga lokacin da abun ya faru a tare yan jaridar suka ce fareeda lamido fareeda lamido, dariya yayi yace ” so congratulate to fareeda lamido ada ba wanda ya santa, amma yanzu sabo da ta ambaci sunana na kwana daya tal gashi dare daya ta zama celebrity, wannan shine amfanin alaka da rasheed matawalle, dariya suka yi gaba dayansu, yace don haka ku dena wahal da kanku wannan tana daya daga cikin masu neman suna kuma ta samu,.