AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Rap rap rap suka ji tapi a bayansu suheer ne ta bayyana( tunda ya fara magana take sauraron shi tazo wurinne da niyyar bashi hakuri kuma ta janye kara amma tunda taji irin maganganun da ya ke tasa aranta lallai sai ya fuskanci hukunci,) har ta iso gabanshi tana tafi sakato sauran jama’ar wurin sukayi suna kallon ikon Allah, yayinda kyamarar yan jarida yasamu abun dauka, tsaya wa tayi tana kallonshi har cikin ido kana tace” yakamata kafarka da ga baccin da kake yi haka nan, kai a tunaninka wannan karyayyakin da ka tara wadannan kake musu zai hanaka fuskantar shari’ah ne? you are mistaken mr Rasheed Ahmad Matawalle, i promise you sai shari’ah tayi aiki a kanka,
Rasheed da tunda ta fara magana yake kallon lumsassun idanunta da kuma pink lips nata ko kiftawa bayayi ganinta yake yi kamar a mafarki ga wani uban kamshi da ya mamaye mishi kofofin shakar iska matsowa yayi kusa da ita sosai har suna shakar numfashin juna, don tabbatar da daga jikinta wannan masifaffen kamshi ke tashi.
Buga yatsunta tayi daidai fuskar shi tace ” what do you think? kana claiming cewa kafi karfin shari’ah ko? a hankali ya lumshe idanunshi kana ya bude yakuma saukewa a kanta, ya bude baki cikin murya mara amon sauti kamar wanda akayiwa duka yace “dani kike magana ne? m…………. Uhmmmmmm su oga Rasheed knn. Nidai bakina da goro.
Da yawa daga cikin fans naga sunan tauraruwar tamu yana baku wahalan kira akwai masu cewa saheer ko kuma suheer when it come to pronounciation. Sunan SUHEER NE BA SAHEER BA.Saheer fa means mai asiri.
????????????AUREN FANSA????????????
BOOK ONE
NA
Ummu Fadeela.
Typing????
Page 28 / 29.
Rasheed yace “dani kike magana,? waye ke,? daga ina,?” tace” nice Suheer lamido,” kuma akan idona ka kade bawan Allahn, wani kallo ya mata take kwakwalwarshi ta fara tuna mishi maganar inspecta, tace infada maka ( ita suheer lamido bazata taba janye wannan karar ba har sai ka fuskanci hukunci,) ……( tace inbaka wannan sarkar ka sanya a wuyanka ka shiga kitche kayi kayi girki domin mata a ka sani da tsoro),
Wani munafikin murmushi yayi yace ” so kece SUHEEER” Tace” kwarai nice,” taci gaba da cewa, so da yawa ku masu kudi kundauki rayuwar talaka ba komai ba, kun dauka kowa irinku ne saidai ashiga store a debo abinci a yi girki kala goma a rana daya kawai, aci azubawa karnuka saura, yayinda wani talakan ya kwana baiga idon ko guntun garin kwaki ba! ka buge shi kayi wucewarka not minding cewa mutane nawa ne zasu cutu dalilin wannan barnar da kayi, yess shi talaka ne amma shi bango ne, bango ne na wasu iyalan dashi suka jingina, sai ya fita ya nemo kafun zasu sa wani abu a bakinsu, ba a rufe abincin yake a store irin na gidajenku ba, wanda in ya kare waya kawai zakuyi a babban store a kawo mota mota a jibge muku, a’a su sai sun fita sun yi aiki da guminsu sun samo halak kafun aci, kasan iya adadin mutanen da suke cikin yunwa da bakin ciki dalilin abunda ka aikata? nasan baka sani ba, wallahi wallahi hakkinmu bazai barku ba, wannan kadai ya isheku rashin nutsuwa, you rich brat people will pay for this one day,.”
Ta fada da karfi, sai kuma ta sassauta murya a hankali tana share hawaye, tace ” baka ji kunyar abunda ka aikata ba kazo ka tara wadannan taron tsintsiya ba sharan, ta fada tana nuna yan jaridar da dukkansu jikinsu yayi sanyi, masu raunin cikinsu ma har sun fara hawaye domin sun san maganganunta gaskiya ne wannan shine halin da kasar mu ke ciki,…. kazo kana shirya musu karyayyaki, and all what i know is, they would not wrote something against you,….but i have one faith cewa wannan karon hukuma zatayi aiki a kanka da masu aikata laifi irin naka, ta juyo ta kalli taron yan jaridar tace “idan labarin gaskiya kukeso kuje asibiti inda aka kwantar da majinyacin kuga halin da yake ciki saiku rabawa duniya.,
Rap, rap, rap shima ya tafa mata kana yace”FABULOUS,” ta ya akayi kika haddace dukkan dialogue din, tabbas kamata yayi mu hada guiwa dake mu fitar da sabon fim, domin fim ne ya dace dake ba girke girke ba, koya ya kika gani? ya fada yana daga mata gira daya, wani suna ma ya kamata mu sanya fim din, ya dan daga kai alamar tunani caan yace” yauwa zamu sawa fim din suna (THE CRIMINAL AND THE SIMPLETON,) koya kika ce suheeer lamido?,… Kallonshi kawai tayi sannan ta juya ta fita daga wurin,. tana share hawayenta da bayan hannu ta nufi asibiti,.
Tun da suheer ta tafi yan jaridar ma suka watse, sai rasheed ya zama so restless, gaba daya ya rasa abunda yake masa dadi, maganganun yarinyar suna so suyi tasiri akanshi ,gaba daya ta dagula masa lissafi.Teburin gabanshi ya buga da karfi yace “noooo, ” buba ne ya shigo da sauri dama yana kan shigowa ne, yace ” sorry boss”
kallon shi yayi da rinannun idanunshi yace “me ka fahimta akan yarinyar nan?, buba ya samu fili ya zauna kana yace “boss dukda dai ba hurumina bane, amma tunda ka bani dama zance wani abu, wato yarinyar nan da karfinta ta shigo rayuwarka, sannan akwai wani sirri a tattare da ita wanda inba muyi da gaske ba zaka iya rasa matsayinka, kallon da ake maka na tauraro mai farin jini duk zai kare za’a ringa maka kallon mugu wanda bai damu da kowa ba sai rayuwarshi, im sorry to say iya reaction din yan jarida dazu ya nuna mana abunda zai iya faruwa idan suka watsa abunda ta fada a duniya, me kake tunanin zai faru idan ta kara samun damar tara mutane ta musu irin bayanin da tayi dazu?. You most do something boss, tun kafin wankin hula ya kaimu ga yin dare, domin wannan yarinyar ba irin saura bane, sai tayi iya kokarinta na ganin ta kaika cell, sannan naga tsanar ka karara a cikin idanunta, you have to fear this girl boss, she is dangerous for you,da wannan nake cewa, sort this out as soon it can be sorted.
Shiru yayi idanunshi a rufe kamar mai yin bacci, amma ba baccin yake ba, tunani ya fara to me zaiyi? shi ba abokai yake dashi ba balle su bashi shawara, ba yan uwa na jiki yake da ba, mahaifinshi ya rasu sannan mahaifiyar shi bata damu dashi ba karshe ma aure ta yi kuma a cikin gidan ubanshi, abunda yafi hurting nasa the most ma shine wadda ta aura din,… jin kirjin shi ya fara harbawa alamun komai na iya faruwa, yasa shi kauda wannan tunanin, dago wa yayi ya kalli buba yace ” me ya kamata inyi?”.
Dan jim buba yayi kana yace ” boss why not ka…….. ya matso kusa dashi ya rada masa magana kasa kasa wanda nidai banji ba…
Rasheed yace “hakan za’ayi, na baka minti biyar ka nemo min lambar,.
Fareeda na zaune a palo tana kwance kalabar dake kanta, anty hafsa na zaune a gefe ta kurawa tv ido kamar mai kallo amma ba kallon take ba hankalinta yayi nisa a tunani,ammi kuma ta fita kasuwa, yayinda suheer tun fitanta bata dawo ba wayar fareeda ne yayi kara, dauka tayi ganin bakuwar lamba, har saida kiran ya kusa katsewa kafun ta kama ta kara a kunnenta, sallama tayi daga daya bangaren aka amsa mata, tace wake magana? cikin yaudararriyar murya yace “shin ina magana ne da fareeda lamido? a hankali tace “eh waye akan waya”? yace wani ne wanda kika fi tsana, nasan zaki canka, shin zan iya magana dake na minti biyu? tace ” amma waye ne yake magana ?” dan dariya yayi mai sanyi sannan yace” Rasheed matawalle ne yake magana” wani dariyan rainin hankali tayi sannan ta ce “waza ka yaudara? badai fareeda bako? murmushi yayi, cikin kara yin kasa da murya yace “fareeda ba yaudara bane Rasheed ne yake magana inason ganinki a gidana idan babu damuwa zan tura miki address din,