AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin abu fareeda taji yana sauka daga cikin kanta zuwa tafin kafanta, a hankali ta furta Ra….Ra…..Ra…. amma ta kasa karasawa, devilish smile rasheed yayi ganin tarkon shi ya kama tsuntsu, yace” sorry baby amma Ra daya ne a sunana wato Rasheed, ina son ganinki a gidana idan ba abunda kikeyi zamu tattauna abu mai muhimmanci, da sauri tace ba abunda nake yi, kiit ya kashe wayar sannan ya ce ” i will wait for you fareeda yayar suheeeeeeeer, ya wani ja sunan saida yaji harshenshi ya amsa.

Tunda fareeda ta sauke wayar sai ta kasa ko motsi a wurin idanunta suna tsaye a wuri daya kyam ko kiftawa basa yi, anty hafsa ne ta karaso wurin tace “ke lafiyar ki kuwa?, shiru ba amsa saida ta kara magana da karfi kafun fareeda ta juyo tace anty hafsa ki dan mintsineni , mintsininta tayi da sauri fareeda tace “auchhh ” kenan ba mafarki nake yi ba, hafsa tace waya kiraki ne duk kin rikice haka,? cikin dauki tace anty hafsa kamar mafarki nake, kinsan wa ya kira ni girgiza mata kai tayi, tace Rasheed matawalle ne, dogon tsaki hafsa taja tace” da alama kin fara haukacewa” da sauri tace wallahi shine wai yana gayyatata zuwa gidanshi anjima idan ba abunda nakeyi, wani irin tsalle hafsa tayi tace da gaske,? wallahi da gaske cewar fareeda, kamo ta tayi tace muje maza ki shirya da wurwuri muje muje, sata a gaba tayi suka wuce dakinsu tsabar excitement rasa abunyi fareeda tayi, nan ta hau sauko da kayan sawanta daga cikin sif, duk wanda ta dauko sai ta yar tace baiyiba, a haka saida ta hargitsa musu kaya gaba daya, da kyar ta samu wani lace yellow mai touches na pink colour dinkin riga da siket masu matukar kyau, takalmi da jaka da mayafi ta fitar dukkansu pink colour ta ajiye a gefe, sannan ta daga wayanta ta shiga daddannawa,anty hafsa dake ganin abunda take yi tun dazu tace me kuma zaki yi? koso kike ki makara,?”

Fareeda tace ‘a’a rabin jiki zan kira in mata albishir, sake baki hafsa tayi ,tace ohhh ni hafsatu mallejo, yanzu duk abunda yar uwar taki ta miki har kin huce kenan, aje wayarnan kije kiyi wanka da wuri nikam, kwabe fuska fareeda tayi tace “amma anty hafsa kinsan wannan ba halinta bane akasi aka samu,” hafsa tace “to ai shikenan tunda kunya zaki bani” da sauri fareeda tace a’a anty, to bari infadawa ammi, dan kar ta dawo bata same mu ba don kinsan dole ki rakani domin bazan iya zuwa ni kadai ba, galala hafsa tayi da baki tana kallonta, sai kuma tayi sauri ta kwace wayar tace ” uwar taku ma baziki kira ba sai munje mun dawo, wannan karon cikin sirri zamuyi abunmu, kinsan wannan shi ake kira do or die situation,…wannan shine final chance da kike dashi na cikar burinki, don haka dole kiyi abunda yadace,don haka wuce kiyi wanka kizo in tsantsara miki kwalliya, fareeda tace inajin wani irin feeling anty hafsa ina jin kamar wani abu zai faru, amma tunda har Allah ya nuna min wannan ranar, then akwai dalilin hakan,…….
????????????Auren Fansa????????????

BOOK ONE

Typing????

Page 30.

……A gaggauce tayi wanka ta fito, nan ta zauna ta tsantsara wa kanta kwalliya na kere sa’a, ba karamin kyau fareeda ta yi ba, kasancewar tana cikin golden age nata, haka suka dunguma ita da anty hafsa suka tafi gidan rasheed. taxi suka shiga har kofar gidan, ba karamin kaduwa fareeda tayi ba da ganin kyawu da tsaruwar wannan gida mai kama da aljannar duniya. Buba ne ya sanarda get man isowarsu, dan haka ba wani bincike ya bude musu kofa suka shiga, wani mota suka gani bakin get din, mai gadi ya basu damar shiga don ya isar dasu cikin ainahin gidan kasancewar tafiyar da dan tazara, ba musu suka shiga driver ya jasu suka bi kan kwalta dodar har zuwa karshen kwaltan inda gefe daya ta dama wani katon parking space ne,ta bayanshi kuma boys quarters ne amma akwai dan nisa, yayinda gefen hagu kuma wani hanya ne da zai kaika bangaren da rasheed yake sauke bakinsa na musamman, tun mahaifinshi na raye anan yake sauke bakin shi shima, a kuma bangaren ne gym room na rasheed yake, kana baya kadan garden na gidan ne mai girman gaske cike da ni’ima, a tsakiyar kuma wato tsakanin parking space da kuma hanyar masaukin baki, nan main building na gidan yake mai dauke da kyakyawar gini bene hawa biyu,.

Sake baki kawai fareeda tayi tayi tana wa gidan kallo irin na kurilla zuwa can ta juyo ta kalli anty hafsa with much suprise, tace ” anya anty hafsa wannan gida ne kuwa? kuma a cikin duniyannan yake? taka kafar ta anty hafsa tayi cikin kasa da murya tace ” me haka? karki bamu kunya mana. Tsit tayi kuwa ta maze. A hankali motar ta gangara gefe tayi parking kana suka firfito, buba ne tsaye gefe yana jiran isowar, saukowa suka yi da murmushi yake musu barka da zuwa kamar ba shine yaci musu mutunci last time ba, jagora yai musu har zuwa falon baki, karasa rikicewa sukayi a palon ganin irin haduwar wurin, su fareeda harda tuntube saida hafsa ta riko ta, gyada kai buba yayi yana murmushin mugunta yace ” ku zauna hajiya bari a kawo muku abun motsa baki, zama sukayi suna kare wa hadadden palon dake tashin sanyayyen kamshi kallo, shigowa buba yayi dauke da drinks kala kala, da bottle water, da kuma glass cups, da soyayyen naman kaza duk akan babban tire, yace yana kallon anty hafsa hajiya kusha ruwa kafun boss ya fito,.

Lokacin da Suheer ta bar gidan rasheed ,direct asibiti ta wuce zuciyar ta cike da wasuwasi, a hankali ta ke taku cikin ward din har ta iso dakin da habeeb yake, bude dakin tayi ta leka kanta kadan, ido suka hada dashi ya jingina da pillow an kwance abunda aka daura masa akai, amma hannu da kafar still suna daure, murmushi ya mata yace “come in plsss, ” dan murmushin da iyakarshi saman lebenta tayi domin sam zuciyar ta ba dadi, ta karasa shigowa ta zauna a farar kujerar dake gaban gadon, cikin sanyin murya tana wasa da doggin yatsun hannunta tace “habeebi ya jikin? ba inda ke maka ciwo dai ko?” jin shiru bai amsa ba ta dago kadan, ido suka hada duk yadda taso janye idanunta daga cikin nasa kasawa tayi, domin wani irin maganadisu take ji yana fizgar ta shima a nashi bangaren haka ne, da kyar ta janye fuskar tata, yace ” fada min mike damunki ? domin fuskar ki ta nuna ainahin yanayin da zuciyar ki take cik, ko so kike in shiga damuwar nima? cikin muryar shagwaba tace”da gaske ba komai faaa its just a mood swing”….. Ya bude baki zaiyi magana kenan aka bude kofar dakin, inspecta musa ne ya shigo, yana kare musu kallo yace ” ina iyayen naku, ba wanda ya kula shi cikinsu, sake bude kofar akayi saiga mama asabe, dama tadan zaga ne, sake baki tayi tana kallon shi kafun ta fara tafa hannu ,tace ” kai yanzu dawowa ka kuma yi? inace anan na koreka nace karka kara zuwa inda muke, to maza fita fita kar inkara ganinka anan, yana baya baya tana binshi harsai da ya dangana da waje kana itama ta fita ta rufo kofar ta waje.,

Kallonshi tayi da kyau tace me ya dawor dakai kuma?. Munafikin murmushi yayi yana shafa gemunshi yace “wani dan kasuwanci na kawo miki,” tace ban fahimta ba?” yace “yanzu kuwa zaki fahimta” wani envelop ya fitar daga aljihunshi ya mika mata, jiki na rawa ta amsa, yace ” wannan naira dubu dari ne,da sauri ta hade rai tace name?” yace “saurin me kike yi? wannan kudin na hiran daza’ayi dake ne, wasu yan jarida zasu zo asibitinnan kawai abunda ake bukata shine ki nuna cewa danki yana cikin mawuyancin hali sosai don haka kina bukatan abi miki hakkin danki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button