AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Asabe tace shikenan abunda zanyi wannan kudi suzama nawa? cikin dariya inspecta yace wannan ma rabine, inkinyi yadda akeso akwai sauran cikon dubu dari,. Da fara’a asabe tace kayyasa wannan abune mai sauki ai, amma ya batun kudin da mukayi dakai kan janye case,? da mamaki yake kallonta yace” amma ke kikace bakwa so hakkin danki yafi miki kudin,” asabe tace ” haba yaro sai kace bakasan farfaganda ba, ai duk farfaganda ce,” inspecta yace ” to shikenan zamu dawo kan batun amma yanzu kam mu gama wannan dake gabanmu, karki manta inkinyi acting mai kyau akwai sauran dubu dari a kasa. ya wuce yana dariyar mugunta aranshi.
A cikin dakin kuma Suheer ne ta mike tana kallon habeeb wanda tun fitar mamanshi yake binta ta fada mashi abinda ke damunta amma taki, karshe ma kuka ta sanya mishi don dole ya koma rarrashinta kuma, tace” ni zan wuce kar ammi tayi fada, ” cikin salon soyayya yace “nikam ban gaji da kallon ki ba,” rufe fuskar ta tayi da hannayenta da suka sha jan henna tana murmushi, bin hannun nata yayi da kallo, tsawon lokaci bata ji yace komai ba hakan yasa tadan matsar da hannun, a kasalance ya nuna mata hannun ta yace i like this, ya miko hannunshi daya mai lafiyar yace ingani, make kafada tayi hadi da boye hannun a bayanta, langwabar da wuya yayi alamar plsss, tace ” ohk to rufe idanunka” kamar wani yaro ya rufe idon yana jiran ta mika mishi hannu, cikin sanda ta mike tana taku a hankali saida ta iso kofa ta kama handle din sannan tace mishi ” pssss” da sauri ya bude idon jikin kofa ya hangota, gwalo ta masa ta fice da sauri tana dariya, dariyar yayi shima ya koma ya kwanta ya rufe idanunshi yana jin wani irin sonta yana kara shiga cikin dukkan wani sassa na jikinshi, bai san wani irin so yake wa suheer ba daga kallo daya da ya mata, dukda zuciyarshi yana fada masa suheer ba sa’an aurenshi bane dan ta fishi ta ko’ina amma ya kasa hakura, kullum sonta kara ruruwa yake a zuciyar shi da gangar jikinshi tamkar wutar daji.
Yana cikin tunanin yaji an banko kofar da masifar karfi, hakan ba karamin firgita shi yayi ba ba shiri ya mike har ya dan buge hannunshi mai karaya jikin gadon da ya ke kai, asabe ne ta shigo ta iso kanshi tana haki,tace” koma ka kwanta ka rufe ido” yace mama…… cikin tsawa tace kwanta nace ka rufe ido kuma duk abunda za’ayi karka yadda kayi motsi, komawa yayi ya kwanta kamar yadda tace, zama tayi kan kujerar bakin gadon tana kwakwulo kukan dole, shidai habeeb duk mamaki ya isheshi ” to me mama take yine haka ba mai bashi amsa” bayan kamar minti biyar saiga gayyan yan jarida bisa jagorancin inspecta musa da wasu kananan polisawa biyu. Asabe ne ta kara sautin kukanta sosai harda sheshsheka tana yi tana fyace majina da habar zaninta, yayinda yan jaridar ke ta daukanta da habeeb dake kwance kamar gawa hoto. Bayani asabe ta fara mai ratsa jiki akan yadda accident din ya faru da kuma gudun da mai motar yayi yabar danta kwance cikin jini rai a hannun Allah da halin da yake ciki har yanxu baisan ma wanda ke kanshi ba, da bayanin shine dama mai taimakonta, yanxu tun randa abun ya faru basu kara daura abinci a gidansu ba tsabar basu dashi mai kokarin nemowan kuma an kassara min shi ta kare tana pashewa da wani kuka mai ban tausayi harda bubbuga kanta kan karfe gadon, dan jaridar ne ya kuma mata tambayar wane mataki take son ganin andauka yanzu, hada ido sukayi da inspecta ya gyada mata kai, ta na hawaye tace adalci, adalci nake so hukumomi su nuna wa duniya cewa ba wanda yaci karfin su hukuntashi matukar ya aikata laifi, su wanke kansu a idon talakawa yan kasa,….. haka ta cigaba da maganganu tamkar wacce aka rubutawa aka bata tayi hadda.
Lokacin da suheer ta koma gida ta samu ba kowa a gidan don ammi ma bata dawo ba dole makullinta ta cire ta bude gidan kasancewar kowa yana da makullin gidan a hannunshi, a palo ta zauna ta dafe kanta da hannunta biyu ba abinda take tunani sai rasheed da irin mugun halinshi a fili tace anya wannan zuciyar mutane ne dashi kuwa, wayar ta ta dauka ta shiga kiran layin fareeda amma har ya katse bata daga ba, ta kuma kira nanma bata daga basau hudu ta kira ta amma no answer,sosai hankalinta ya tashi don hakan baitaba faruwa a tsakninsu ba, layin ammi ta kira ammi ta sanar da ita cewa gata a hanya tana dawowa ta kusan gida.
Su fareeda suna zaune har tsawon wasu mintina amma ba rasheed ba labarinshi, gashi sun kasa shan ko ruwan da aka kawo musu duk kuwa da yadda yawunsu ya tsinke da ganin hadin da aka yiwa naman kazar sai da suka shafe awa daya cur kafun rasheed ya fito, kamshinshi mai kwantar da hankali mai shaka ne ya fara isowa kafun oga kwata kwatan ya bayyana, cikin takun shi mai cike da charm ya iso ya zauna ya daura kafa daya kan daya kamar kullum sanye yake da kananan kaya wando da riga bakake wuluk da kuma face cap shima baki mai dauke da tambarin star, sosai kayan suka dace da farar fatarshi, yana murmushinsa mai dauke hankalin ma’abocin kallonshi yace cikin cool voice”barka da zuwa hajiya fareeda, wato saida na ganki a zahiri na tabbata hoto baya miki adalci, domin kyanki tacacce ne wanda babu mishkila a ciki ko kadan, fareeda tana washe hakora kamar mai tallan close up tace ” godiya nake yallabai”, yaken dole yayi a ranshi yace mace ba class ko kadan haka, a zahiri kuma cewa yayi ” naga hotonki ne a shafinki kuma naga kin dace da irin macen da nake so ta fito a cikin fim din da muke san fara dauka kwanannan mai dogon zango, sosai fareeda take farin ciki sai zuba godiya take anty hafsa na tayata, danne takaicinshi yayi yace meyasa baku sha ruwa ba? ai bakin rasheed basa zama da yunwa, a tare suka ce a’a sun gode, rasheed yace ” ba damuwa za’a muku take away sai ku wuce dashi, amma yanxu muna bukatar daukan hoto tare dan a turawa masu kula da bangaren hoto,na cikin shirin su duba wani irin make up yakamata ake miki in an fara daukan shirin.
Da sauri ta tashi fuskarta ya gaza boye irin farin cikin da take ciki, ta matso kusada kujerar da yake tana ta kokarin gyara gyalenta, saida ya kwashe tsawon minti biyu a zaune kafun ya taso ya tsaya kusa da ita yana ta yamutsa fuska, zaro wayar shi yayi kirar iphone13pro ya daga ya fara kashe musu selfie, sundau kusan kala goma, fareeda tana ta murmushi , amma gogannaku ya hade fuska tamau, zama suka yi bayan sun gama hoton yace ,”ki zama cikin shiri ko wane lokaci za’a iya kiranki”, da sauri tace “yaushe za’a fara daukan shirin?” yace ehh toh nan da kwana hudu insha Allah, kamar walkiya saiga buba ya shigo, yana zare idanu yace boss akwai damuwa fa, rasheed ya kankance idanu yace “kamar ya wane irin damuwa kuma?” buba yace a’a boss mu bari dai sai anjuma tunda kana da baki yanzu, rasheed ya dan bata fuska yace wadannan ba baki bane zaka iya fada a gabansu, wannan ya nuna fareeda yace itace jarumar da zata taka rawa a sabin shirin da zai fito,buba yace “woww kuma ta dace gaskiya”, murmushin jin dadi fareeda tayi,.
Buba yace “yanzu director ya kira ni yace maganan daukan shirinnan fa an daga shi, dum dum dum haka zuciyar fareeda ya buga, da sauri rasheed yace don me ya sa wai ,”? buba yana sosa keya yace ” boss akan accident case dinnane da kuma dan hayaniyar da suheer lamido tayi a gidannan dazu kasan a gaban yan jarida abun ya faru, a rikice fareeda da anty hafsa suka mike fareeda tace Suheer kuma? tazo gidannanne ? kallon juna rasheed da buba sukayi a tsanake suka yi magana da ido, sannan rasheed yace auchh yana shafa goshi wllh na manta da batun case dinnan, yanzu abunda za’ayi kaje kayi magana da lauya na muji yadda abun yake, amma kana ganin in case dinnan yaje kotu zai daukemu tsawon yaushe kafun a gama, buba yadan daga kai yace ” boss ina ga zai kai wata biyar zuwa shida, rasheed yace yanzu daukar fim namu dole ya tsaya zuwa nan da wata shida kenan? anyway ba damuwa, ka fadawa ma’aikata kowa ya tsaida aikin shi sai mun neme shi. zuwa lokacin zufa ya gama yiwa fareeda wanka yayinda hawaye ya kawi idonta da sauri tace “amma yallabai in aka janye case dinfa? yadaga kagada yace ” shikenan sai mu ci gaba da shirye shirye cikin kwana hudu, da rawar murya tace “acigaba da shirin kawai, suheer kanwata ce, tana sona sosai da kaunar abunda nake so, tana son farin cikina don haka nasan zata janye karar nan domin ni, don haka aci gaba da aikin kawai nan da gobe zata janye karar, kamo lebenshi na kasa rasheed yayi yamasa wani irin tauna saida yaji zafin har cikin kwakwalwarshi, yayinda buba yayi wani irin dariyan nasara yace “amma basai kun wahal da kanku ba lauyan boss zaiyi komai fa,” da sauri anty hafsa tace me wani abun wahal da kai anan bayan ga sauki abu a gida basai an jajubo wani lauya ba ai, da haka suka tsaida magana akan suheer zata janye case idan aun dawo gida.