AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wanda aka kira da Amaan tunda dan uwanshi ya fara magana baice ƙala ba, hasalima idanunshi a lumshe suke,yayinda ya sarƙafe hannayenshi cikin na juna, kanshi na kwance bisa headrest, sai aikin karkaɗa ƙafafu yake , wai kamar shi gaye dashi mai degree na biyu a fannin aikin jarida wanda yayi karatu a second best University in the World shi granny zata kalla ta haɗashi da wancan ƙazaman yarinyar da sunan aure God forbid wllh, tuna yarinyar da yayi ma yanzu yasa shi jin wani amai yana taso masa, mtsssssss yaja wani dogon tsaki.
“How dare you, Amaan ya ina maka magana ka maidani soko mara abun yi har da jamin tsaki wato ga banza yana magana ko.”?
A karon farko wanda aka kira da Amaan ya dago kyawawan idanunshi ya kalli dan uwanshi cikin wani sassanyan murya wanda in ka kalleshi zaka dauka ba magana yake ba yace “Look Ammar am not in d mood will you please keep u’re mouth shuttt?.
Cikin tsananin fushi Ammar yaɗaga hannunshi da niyyan kaiwa Amaan mari, cikin ƙasa da second ɗaya Amaan ya damƙe hannun kana yace ” Srry Dude, ni ba baƙon zafi bane i just told u am nt in d mood, me na tsanani harda kawo duka? yanzu ya ka ke so ayi?” ya karishe zancen yana devilish smile ɗinsa haɗi da shafa beard dinsa da hannu daya.
Kwafa Ammar yayi gami da kwace hannunsa yace ” fita zaka yi ka duba mana motan inba haka ba mu kwana anan.” ohh my godness” cewar Amaan yana tattare fatar goshinsa wuri ɗaya “but am not a mechanic you know! yeap i know, amma masu iya magana sunce (duk tsuntsun da ya jawo ruwa)?
Shi ruwa kan doka Amaan ya karisa masa karin maganar. So maza aje a duba mana mota. murmushi Amaan yayi yasara mishi kana yace “with pleasure sir, sannan ya fita daga motar garin yayi duhu sosai kasancewar wata yayi nisa, haka ya laluɓa yaje gaban motar yatsaya ya harɗe hannu a ƙirji,
Wani lallausan murmushi Ammar ya saki sannan ya buɗe mashi gaban motar kana ya sauƙo shima, gajeren tsaki yaja cikin yin ƙasa da murya yace “dubi abunda ka jawo mana, dan Allah salon kura yafito ya cinye mu ya cuce ni tun banyi aure ba. “
Amaan ya dube shi inka gama gungunin naka sai kazo ka haska min light mr man.
Yana cikin ƴan taɓe taɓe wa injin motar ammar ya taɓa kafaɗunshi yace” kaji abunda nake ji kuwa ɗan uwa ?.
Amaan yaɗago yace ” me kake ji matsoraci kawai haska min nikam muyi mu gama mubar wurinnan.
Ammar ya ƙara matsowa kusa dashi yace “da gaske fa, sa kunne kaji kamar takun ƙafafu ana gudu.”
Ɗan saurarawa Amaan yayi kana yace” Tabbas naji gashi sai ƙara matsomu takun yake, yi maza ka kunna motar muga ni ko ya gyaru kar kidnappers suyi ramm damu musa iyayen mu a uku.”
Taku daya Ammar yayi da niyyar buɗe motar ya kunnata suka alamar faduwar abu timmm a kasa haɗi da wani irin azababben ihu da ya ƙaraɗe ilahirin jejin cikin muryar babbar mace da kuma ƙaramar yarinya,
A ɗari da sittin ammar yadawo ya maƙalƙale dan uwanshi yayinda jikinshi yake ta karkarwa.
A kunne amaan ya raɗa mishi ” relax bro ba komai fa bari mu haska mugani.” menene.
Da mugun mamaki ammar yace u’re mad amaan inkuma abu mai cutarwa ne fa?
Amaan yace what of in abu mai buƙatan taimakon mu ne? kai bakayi mamaki ba just of a recent motar nan ta tsaya alhali lafiyar ta qalau muka fito da ita , plsss muje mu duba.
Ammar yace” cabbb sai dai kai kaje ka duba amma ba dai niba.
Wayar dake hannunshi amaan ya ƙwace ya dan buɗe light na screen ɗin kana yabi inda suka ji ihun da kallo . ya salam ya furta a kasan maƙoshinsa ganin matashiyar mace kwance a kasa wanwar ga yar yarinya kwance a gefenta ba alamar numfashi a tattare dasu.
Da sassarfa ya karasa wurin yana kallonsu ya kunna torch light na wayar yana haskasu from head to toe, to make him sure mutane ne, ganin amaan ya jima a wurinne yasa ammar biyo bayanshi duk da a tsorace yake matuka, yana isowa suka kuma jin wani takun wannan karo kamar mutane dewa ne da kuma magana sama sama suna cewa “tabbas tanan ihun ya fito mu hanzarta mu kamota karta kuma tsere mana. juna twins ɗin suka kalla domin duk sunji abunda mutanen suke faɗa duk da kasancewar suna ɗan nesa dasu.
Ba tare da wani tunani ni ba amaan ya naɗe hannun rigarshi ya cicciɓi adama ganin haka yasa ammar ma sunkutan fareeda suka yi cikin mota dasu, a bayan motar suka shimfiɗe su da gaggawa suka koma gaban motar cikin ikon Allah ammar yana wa motar key ta tashi a ɗari da tamanin ya dige ta suka bar wurin da masifar gudu.
Barinsu wurin keda wuya yaran alaji sama’ila suna isowa hasken motar suka bi da kallo kana suka mara mishi baya gudu suke iya ƙarfinsu saidai ina gudun mota bazai haɗu dana ƙafa ba kafun su ankara motar ta bacewa ganinsu.
Gudu kawai ammar yake shararawa irin na ceton rai, saida suka yi nisan gaske sun tabbatar sun bar yankin gaba daya sannan ya rage gudun ya tsaida motar ruwa ammar ya ɗauka ya buɗe bayan motar ya watsawa fareeda a fuska take ta kawo numfashi watsawa adama yayi amma ko gezau batayi ba ya kuma watsa mata nanma shiru amaan ne ya fito shima ya karbi bottle ɗin ya kwarara mata sauran ruwan a fuska take ta sauƙe wani nannauyan ajiyar zuciya kana ta fara buɗe idanunta a hankali.tar ta sauƙe su akan wasu samari masu kama da juna a rikice ta fara taɓa cikinta jin yana jikinta ta maida dubanta kan matasan tace “ina ne nan dan Allah karku illatamu me muka muku shiiii Ammar yasa yatsa a baki ya mata alamun tayi shiru aikuwa tsiit tayi sannan suka koma gaban motar suka tada ta suka tafi. sai ƙarfe sha ɗaya da kusan rabi suka shigo birnin yola direct wani anguwa naga sun nufa suna shiga cikinta nace wow masha Allah, domin anguwa ce na waɗanda kumbar su yakai susa, ko ince waɗanda ludayinsu yake kan dawo, anguwace na ƙusoshin gwamnati, masu kara zero uku a takarda, da manya manya yan siyasa masu ci da gumin talaka.
A bakin wani tabkeken gida suka tsaya amaan ya danna horn mai gadi ya buɗe karamar kofar dake jikin makeken get ɗin ya leƙo waje ganin motar gida ne yasa shi wangale musu ƙofar suka danna hancin motar cikin wadataccen farfajiyar gidan wanda a kalla zai iya ɗaukan motoci goma sha biyar ba tare da ɗaya ya gogi ɗan uwanshi ba. adama dai tana rungume da yarta a ranta tana raya cewa shikenan tayi gudun gara ta tadda zago, ta gujewa alaji sama’ila ta faɗa hannun yan yankan kai, domin wannan gida da na masu yankan kai yayi kama .
Tunaninta ya katse ne lokacin da taji anbuɗe motar ta ɗago kai suka haɗa idanu da saurayin da ido yamata alamun ta sauƙo ba musu ta sauƙa ammar ya rufe motar suka nufi entrance na shiga gidan. ganin tana tangal tangal kamar zata faɗine ammar dake bayanta yasa hannu da niyyar karɓan fareeda nanma bata mishi musu ba ta bashi domin sam bata da karfi.
Amaan ne ya zuge kofar glass din yashiga cikin haɗaɗɗen falon ɗauke da sallama a bakinshi, wata farar mata ce da bazata haura shekara hamsin ba hakimce a kan ɗaya daga cikin kujerun dake kewaye da falon tana riƙe da remote control, da sauri ta ɗago kanta jin muryar tagwayenta ta amsa sallamar gami da cewa “wa nake gani a daren nan kamar BOƊƊI na daga i…….maganar ta ya maƙale ganin ammar yana shigowa shima ga yarinya rungume a kafaɗarshi ga kuma mace da ciki a gabashi, ƙarasowa amaan yayi yamata side hug kana yace” mune sweet mum kinyi mamaki ko ita dai gaba daya hankalinta nakan su adama wacce ta tsaya nesa kaɗan tana wiƙi wiƙi da idanu.