AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin rawar murya mai alamar tahowar kuka ammi tace ” Uwani kece wnn? sakato uwani tayi jin muryar wacce ke magana da dan gudu gudu ammi taje ta rungume ta ba tare da ta damu da yanayin jikinta ba, kuka suka sake a tare, uwani tace ” Adama kece wnn, kece Allah ya daukaka haka, ku godewa Allah ke da yaya tabawa, tabbas Allah yana sonku. Kun tafi gaba dayanku kun barni da wahala, sai kuma ta sake ta tana kare mata kallo daga sama zuwa kasa tace ” Adama ina cikin da kika tafi dashi,? ina kuma fareeda.?
Da yatsa ammi ta nuna mata yan matan nata dake tsaye suma hawaye yana bin fuskar su ganin amminsu na kuka.
Uwani tace” ya salam , tana toshe bakinta da hannu yayinda take kare wa zuka zukan yan matan kallo, hannu ta ware musu wai su zo. Ba musu sukaje suma rungumar su tayi a tare tana share kwalla, lamido dai na tsaye yana kallon ikon Allah, yayinda bugun zuciyar hafsa ke dada tsananta cikin ko wanne dakika. Adama ne ta katse shirun nasu tana kallon uwani tace “ina su mama da baba,? ina yaya tabawa? da kuma Alhaji?.
Wasu hawayen da suka fi na farko zafi uwani ta share tace”babanmu Allah ya karbi abunsa shekaru goma da suka gabata, mama kuma baifi shekara daya ba kenan da rasuwarta, inna lillahi wa’inna ilahi raji’un, ammi ta furta tana dafe kanta, uwani ta cigaba da magana “tabawa kuma bacewarki da kwana uku itama ta rasu anan ta nuna tsakar gidan, a gabana, a hannuna ta rasu wani kuka ne ya kuma kwace mata, tace alaji kuma gashi can a daki yana girbar abunda ya shuka tun anan duniya kafun yaje ya tadda na can, ta na nuna dakin da wannan gurnanin yake fita daga cikinsa, tace adama na barku a tsaye gaki da baki, mushiga daga ciki idan zaku iya zama a dakin namu.
Girgiza kai ammi tayi ” tace ki kaimu wurin alaji tukunna,” jagora ta musu zuwa dakin da alaji samaila ke kwance, (hasbunallahu wani’imal wakeel, allahumma ajirni fi musibati wa’aklifni khairan minha) shine abunda ammi ta furta lokacin da tayi arba da alaji samaila a kwance, yayinda hafsa ta rufe idanunta da sauri, fareeda kuma a guje ta fita waje suheer ta mara mata baya, lamido ne yayi karfin zuciyar kare mishi kallo a ranshi ya na jinjina ikon Allah, Allahu Akbar ya furta..
Kwance sarkin noma yake a kan katifar da ta gama cinye wa, bangaren jikin shi daya kama daga fuska har zuwa kan yatsan shi a shanye yake, yayinda daya bangaren yake haye suntum kamar anzubawa filawa yeast, tsabar kumburar da yayi har tsagewa yake yi wasu ruwa masu dan karen doyi suna fita ta cikin duk inda ya pashe din , idon shi daya na bangaren dake kumburen ya tsiyaye baka kallon komai sai ramin idon kamar abu aka sa aka cire kwayar idon aka bar kogonsa, hakan ya kara taimakawa matuka wurin munana yanayinsa, anan yake bayan gida yake pitsari dukda uwani tana kokarin kwashewa , amma hakan bai hana ya haifar da wasu manyan tsutsotsi dake badakala a jikinsa ba, sannu a hankali suke cin naman jikinshi, shikadai yasan irin azabar da ya ke sha.
Uwani ta kalli ammi tace “adama kinga rayuwar da alaji ya jefa kansa ko,? domin wnn shi ya jefa kansa baza’a yiwa kaddara sharri ba. Anan yake kwance tsawon lokaci ba baki balle ya riki istigfari, sai wannan uban nishin dake hana makwabta bacci,” ammi tace amma meya sameshi haka, me ya faru bayan na tafi?. Uwani tace,
.............WAIWAYE..............
Bayan anyi cigiyar adama da yarta a yola har an gaji ba labari, haka alaji samaila ya dawo goruba cikin tashin hankali, bayan yayi kwana biyu acan, kiran tabawa da uwani yayi yace lallai sai sun fada mishi inda adama ta shiga domin da masaniyar su hakan ya faru, rantse rantse uwani ta fara akan bata san komai akai ba, caraf tabawa ta karbi maganar inda ta sanar dashi cewa ita ta sa adama ta gudu domin bazata bari ya ida mugun nufinsa akanta ba, aiko baiyi wata wata ba ya cafko wuyan tabawa ya mata wani shaka na musamman tun tana kokarin kwatar kanta har yaci karfinta, tambayarta yake ta fada masa inda adama ta shiga ba tare da ya ankare da abunda yake aikatawa ba, amma tabawa taki magana, lokacin da ya sake ta tuni idanuwanta sun firfito waje, jikinta ya saki don haka faduwa kasa ta kusa yi uwani ta taro ta suka fadi tare, lura tayi cewa bata numfashi, a mugun tsorace tace, “ka kasheta alaji” a zabure ya dawo yana kallonta kamar yaga sabon abu, tabbas ta rasu, nan ya daga ta ya shigar daki sannan ya tsoratar da uwani kan cewa idan labarinnan ya fita a bakin ranta itama.
Bayan wani lokaci da rasuwar tabawa alaji da bala suka koma wurin boka dan sanar mishi bacewar fareeda da kuma cikin adama,…………Wani irin mahaukacin dariya bokan yayi bayan sun gama masa jawabi kana ya dauko wani dogon kibiya da wani wuka mai kyalli ya jefe su dashi, wani irin karan azaba suka saki a tare lokacinda kibiyar nan ta caki idon samaila, sai dan idonshi a kasa,yayinda wukar ta yanke daga tsakiyar cinyar bala shima sai ga kafarshi a kasa jini yana tartsuwa, tun basu gama jin azabar ba bokannan ya kara daga wani sanda mai kama da mashi ya nuna su dashi, yana magana da wani irin yare, wani abu kamar wuta ne ya fita daga jikin sandar ya fara circulating a tsakaninsu, wani irin dambe suka fara su biyun kamar mayunwatan zakuna, jibgar juna suke duk da cewa ba ido da kafa a garesu,ihu suke yi sosai sanda ya musu jina jina kafun ya tsaida abun, zube wa sukayi a kasa suna sauke numfashin wahala.
Tsawan lokaci suna kwance a wurin daga bisani ya kuma nuna su da wannan sandar batt suka bace, sai gasu kwance tsakar gidajensu, sosai iyalensu suka firgita da ganinsu, nan aka hau jinya lokaci mai tsayi suka dauka suna jinya kafun suka sami sauki, alaji samaila ya zama baida ido daya yayinda bala ya zama gurgu. ana haka ne jama’ar gari sukayi mitin akan a sauke sarkin noma a nada wani, mafi rinjayen mutane sun yarda take aka kwancewa samaila rawanin sarkin noma, sosai ya shiga tashin hankali har yi yake kamar zai tabu, domin har ya fara sambatu irin na farkon hauka, a yammacin ranar ne kuma alaji manga babansu twins, mai sa mishi ido a gidan gonanshi dake yola ya kira shi ya sanar dashi mummunan labarin gidan gonar shi ya kama da wuta, anyi kokarin tsayar da wutan amma abun ya gagara gaba daya dabbobin dake ciki daga kan shanaye har kan kaji gaba daya sun kune kurmus ko kasusuwansu babu.
Wani irin kara samaila yasa ya fadi kasa a sume, asibiti a ka garzaya dashi nan aka tabbatar da jinin shi yayi mugun hawa a kiyaye bacin ranshi, da kyar a ka shawo kan matsalar inda yayi doguwar jinya kafin aka sallamosu gida, samaila bai kara shiga tashin hankali ba saida damuna ta sauka ya lallaba ya tafi domin yin shuka a gonakin sa, saidai abun mamaki shine kab gonakin anyi shuka aciki, kida ya nemi jin ba’asi ashe amininsa bala ne ya ha’inceshi yabi duk gonakinsa ya saida su gaba daya, a fusace ya tafi gidan bala ya iskeshi zaune da kafar robar da yaje aka masa “yace bala ashe kai maha’inci ne yaza ka bi ka sayar min da gonakina bayan kasan na rasa komai nawa, kuma duk a dalilinka gashi yanzu kana zaune kai cikin iyalinka cikin jin dadi, da baka tura ni na aikata abunda nayi ba da yanzu ina zamana lafiya, duk kai ka jawo min masifar da na ke ciki yanzu, bala yace “samila kenan ka dauka ni wawa ne, ka dauka zan rasa kafata ta dalilinka sannan inbarka haka lallai kayi kuskure, ai shi zaman duniya iyawane, sannan da na ce kazo inkaika wurin boka saina ciccibeka aka fadane? dazaka iya kin bina ai amma dashike kwadagin mulkinne a ranka baka bini ba, yanzu ina mulkin? to bazan yadda inyi biyu babu ba.