AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tashin hankali kuma yana gaba sai ka duba asusun ka na banki ka samu ba ko sisi tukunna zakasan da bala kake zancen, jiki na rawa samaila yace me kake nufi bala?” yace kaje ka duba asusunka nace shina kwashe naje aka min kafar nan danake takawa dashi yanzu, tunda kaine silar rasa kafata, luuuu samaila ya tafi baya ya fadi kasa sumamme wannan shine dalilin shanyewar barin jikin shi saboda mummunan hawan jini dayake dashi kuma yasamu mummunan labari.

A cikin wannan haline kuma ciki ya bayyana jikin uwani, tayi fama da laulayi sosai, amma ga samaila kwance yau yana ganin ciki amma ba halin ya kaita gwajin da ya saba din halin dayake ciki kadai ma ya isheshi shaidar cewa wancan aikin ya juma da lalacewa, haka tayi ta renon cikinta har lokacin haihuwa ta haifo santalelen danta mai kama da samaila sak, gadai magaji samaila ya samu amma ba abunda zai iya yi masa, sosai yake son yaron tun yana karami dukda baya iya daukanshi, tun dan baba yana shekara biyar suka fahimci ba karamin kangararren yaro za’ai ba a wurin, yana shekara goma sha biyu ya zama tataccen mashayi, ba abunda baya sha na kayan maye…….ba irin daukan maganan da ba ya jawa iyayenshi, ba abun wahala bane a wurinshi ya yanka mutum da wuka,. dan sauran abunda ya ragewa samaila akan case din dan baba da police ya kare domin kullum akan kamashi ake kafun ya gawurta ya zamo babban dan fashi duk cikin shekarunsa dake kasa da sha takwas.

(Allah ka shiryamana zuriya badon halinmu ba),.

A hankali ciwo da damuwa suke cigaba da cin samaila har yakai matakin da yake kai yanzu……..

Ajiyar zuciya lamido ya sauke sai kuma ya dubi adama da hafsa dake kuka kamar ransu zai fita yace kudena kukan hakannan, a hankali adama ta taka zuwa inda samaila ke kwance ta tsugunna tace “wannan shine makomar rayuwar da kai ka zabar wa kanka alaji, wannan shine karshen masu hali irin nanka, koma wanda yafi naka muni kafun su koma su tadda abunda suka shuka cikin kabari da kuma ranar hisabi, ba ruwan kaddara anan kaine ka jawa kanka da kanka, ina ma mutane zamu fahimci cewa abunda yake namu bazai taba tsallakemu ya tafi zuwa ga waninmu ba, ina ma zamu fahimci cewa gaggawa baya kawo samu, ina ma zamu fahimci cewa bazamu taba tsalle har mu wuce wuyar mu ba. tabbas da kayi hakuri zaka samu sarautar sarkin noma ba tare da ka sabawa Allah ba, amma saika nuna wani ne zai baka, Allah kuma ya barka da wayonka da kuma waninsa da ka kama, yanzu wa gari ya waya, ba mulkin, ba sarautar, ba dukiyar, sannan ba lafiya, kace namiji kakeso, kayi ta daukan rayuwar bayin Allah akan hakan, gashi Allah yabaka namijin a odd time wanda bai amfaneka ba, bai amfani al’umma ba, ya zama barazana ga rayuwarka, kayi kuskure samaila, ina fatan wannan ya zamo darasi ga yan baya masu fatan kwatanta hali irinnaka.

Wasu hawaye ne suka gangaro ta idon samaila guda daya, a karon farko tun bayan da bakinshi ya dena magana tsawon lokaci, yau yayi magana, yana fizgar kalmomin da kyar yace, ada….ma ….ina ya..ra..na kar..ki..ce min su.. mutu ..do..n Allah, ki nuna min su kozan samu sumin addu’an samun sassauci a cikin ukubar da nakesha, sosai yabasu tausayi don duk karfin halin lamido saida ya zubda hawaye, yayinda uwani take ta mamakin yau alaji yayi magana.

Ammi ta dube shi da kyau tace “itama dana haifa ya macece, wacce na tafi da itama ya macece, a hakan kana bukatan addu’arsu? i mean kana bukatar addu’ar yaya matan?.

A hankali hafsa ta kariso itama ta durkusa gabanshi tace alaji ina YATA,? kallon kallo aka fara a tsakaninsu ya bude baki da kyar yace mallejo…..

Wannan page din ya taba ni sosai, nazamo so emotionally, yess its an fictious story amma jinake kamar gaske, hango su nake a idanuna, there’s alot if things dake faruwa a duniyannan, wanda wani idan kaji sai ka dauka almara ne amma kuma da gaske ne, shin kin/ka taba haduwa ko ganin mai hali irin na samaila sarkin noma❓. Ku fito mu tattauna akai. Idan kin karanta ki tofa albarkacin bakinki don Allah.

????????????Auren Fansa????????????.

Book Two

Story and Writing

     By

Asma’u Mai Anguwa

Ummu Fadeela.

Typing????

Page 39 / 40.

…………Yana kallon hafsa a hankali yake magana, dan saika maida hankali sosai kagun kaji abunda yake fada, yace “mallejo kene wnn? ina kika shige tsawan lokaci?, kafun anty hafsa tace wani abu fareeda da suheer suka shigo saboda kiran da lamido yai musu,

Ammi ne ta kawosu har gabanshi, kai da ka gansu kasan a tsorace suke kamar kace pit su gudu, karma fareeda taji labari, dan har wani rawa jikinta keyi, ammi ta nuna fareeda tace “wnn itace yata da na tafi da ita, wannan kuma ta nuna suheer itace na tafi da cikinta, gasunan a gabanka Allah ya rayasu, kana kallonsu yanzu ba yadda ka iya, and Iam happy you learned a lessons of your life to the hard.

Ta mike tana share hawayen da suka ki tsaya mata, murmushi alaji samaila yayi, amma inka gani dole ka rufe ido tsabar munin murmushin, yana kallonsu yace Allah maku albarka, Allah ya shirya minku ya hada kanku, ku kasance masu yimin addu’a duk da ban kasance uba nagari a gareku ba, ban sauke nauyin da duk wani uba nagari ya kamata ya sauke akan yayansa ba, amma na roki yafiyarku, ina ji ajikina Ina raye ne don kuzo gareni ku yafemin, tabbas na aikata kuskure a rayuwa ta saidai lokacin gyara ya wuce min, amma ubangiji Gafurrun Raheemun ne, abu na gaba shine ku taimaka min ku kula da kaninku idan kun samu daman hakan, ku tallafe shi ya samu ilimi domin rashin ilimi shine silar tabewa ta, tabbas jahilci musiba ce, wani irin shakuwa ya fara a hankali ya lumshe dayan idonshi wanda dama kusan a rufe suke, yana sauke numfashi da sauri sauri, kasancewar ya dade baiyi magana ba, sai yazama maganar da yayi yanzu ya wahalar dashi sosai, still idonshi a rufe, yace hafsatu! ga yarki nan, ki godewa adama domin ba dan ita ba da yanzu ba labarin fareeda a wannan duniya tamu, kan hafsa ne ya fara juyawa ta tsammaci hakan tun lokacin da ammi ta ambaci garin goruba wa direba, bata kara tsinkewa ba saida suka zo kofar gidan alaji samaila, kana ganin uwani da tayi, domin su biyu ta samu tsakar gida ita da tabawa ranar da ta kawo yarta ta ajiye batare da ta kuma waiwayarta ba, amma meyasa yanzu da aka ambata mata cewa ita ce yarta zuciyar ta ya kasa daukar nauyin maganar, all this while ashe da yarta take rayuwa,? ashe yarta ta taimaka? tabbas taimakon mabukaci yana da amfani a rayuwa. ta san tana son yaran adama har cikin ranta amma tafi nuna hakan akan fareeda tafi kula al’amuran fareeda, tafi tsayuwa akan matsalarta, saidai tana alakanta hakan da sunan ta sunan yana tuna mata da yarta sosai.

A bangaren fareeda kuwa bambarakwai taji maganar, to wacce fareedar ake nufi,? amma kuma ai ita kadai ce fareeda a dakin, take maganar ammi na kwana ki ya fara dawowa kwakwalwarta,

( Nauyin dake kaina akan fareeda yafi wadda yake kaina akan suheer, domin fareeda yata ce, amma bani na haifeta ba,) a lokacin basudau maganar da muhimmanci ba daga ita har suheer, kawai sun dauka ammi ta fadi haka ne dan ta hana fareeda shiga harkar fim.

Inna lillahi, ta ambata tana dafe goshinta, so ta tabbata kenan ba ammi ne ta haifeta ba amma ai……jin kanta tayi yana juya mata ta tafi baya baya zata fadi smammi tayi azamar kamota ta riketa gam, a jikinta. lamido dake tsaye kikam kuwa sai nanata kalmar Allahu akbar yake a zuciyar shi, ashe fareeda yar kanwar shi ce, what a coincidence, take ya fara tina abunda ya faru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button