AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nan twins suka kwashe duk labarin abunda ya faru daga barinsu ƙauyen goruba har zuwa haɗuwar su da adama suka bayyana wa Dr hauwa mahaifiyarsu. mum ta kaɗu matuka da jin abunda suka faɗa kasancewarta mace mai tausayi har hawaye yakawo idonta, tace “ohk dearies kunyi ƙoƙari am very happy with u guys da abunda kukayi, yanzu maza kuje kuyi freshen up kusamu kuci abinci ku kwanta, Insha Allah zuwa safe zamu tattauna da ita by then daddynku ya dawo.” dukkansu suka haɗa baki wurin fadin yesss mum sannan suka miƙe suka hau sama inda jerin dakunansu yake.
Ganin sun wuce dr hauwa ta tashi ta dauki fareeda kana ta kalli adama cike da tausayawa tace muje kuyi wanka ku huta ko, tafiya kadan suka yi ta bude wani daki dake nan kasa ta shiga ta ajiye fareeda a kan gado kana ta wuce bathroom ta haɗa masu ruwa da kanta ta fito tace da adama “kishiga kiyi wanka itama ki mata bari in haɗo muku abinci kafun ku gama”, adama ta amsa da to mum kamar yadda taji twins sun faɗa.
Dawowar dr hauwa da kwanukan abinci yayi daidai da fitowar adama riƙe da hannun fareeda sun gama wanka . mum tace gashi bamuda kayan yara a gidan sai zuwa safe a samo mata ko yanzu ga abinci nan kuci sai ku kwanta ku huta sai zuwa safiya insha Allah mayi magana ko?
Kai kawai adama ta iya gyaɗa mata ta juya ta fita nan suka zauna suka ci abincin adama bata wani ci na kirki ba domin duk fargaba ya cika ta.
Taci gaba da ba fareda saida ta tabbatar cewa ta koshi sannan ta wanko mata hannu da baki tazo ta kwantar da ita saman lallausar gadon ta rufa mata bargo.
Ta hau tattara kwanukan da niyyar fitarwa waje har tazo bakin kofar ta kama handle ɗin da niyyar buɗewa taji anbude asalin kofar shiga palon anshigo da hakan yasa ta dakatawa sai kuma taji karar ringing alamar ana kiran wanda yashigo ɗin a waya.
Alaji manga wadda shigowar shi kenan daga taronsu da suka saba gudanarwa na yan siyasa, har ya kama rails na stair case zai haura sama yaji wayar shi tana tsuwa hakan yasa shi tsayawa haɗi da ciro wayar daga aljihun babbar rigarshi murmushi yayi kana ya kara wayar a kunnenshi yace…………. jin sunan da aka kira ne yasa adama d……..
Like Comments and Share
Follow this link to join my facebook group????????
https://www.facebook.com/groups/299890475435292/?ref=share
Bismillahir Rahmanir-Raheem
????????????AUREN FANSA????????????
BOOK ONE
Na Ummu Fadeela
Page 3
Da murmushi Alaji manga ya kara wayar a kunnenshi yace ” kaga sarkin noma, alaji sama’ila kaine a darennan lafiya kuwa?” dan jim yayi na wasu daƙiƙu kana yace “ashhaa Subhanallahi matar ka da yarka kuma, tun yaushe haka ?… kai abukam baiyi daɗi ba…. ohk to shikenan sai ka shigo goben ma ƙarisa maganar amma ka shigo da wuri dan mu sa mu shigar da report akan lokaci….”ok to Allah ya kiya ye gaba. “kitt ya yanke wayar ya cigaba da haura wa sama.
Anan bakin ƙofar adama ta durƙushe ta aza hannu aka da niyyan kurma ihu, kome ta tuna oho da sauri ta toshe bakinta wani irin zufa yana keto mata kamar wacce ta haɗiye kunama,
A zabure ta miƙe ta nufi jikin taga ta ɗaga curtains na tagar tana observing na tsakar gidan, a hankali ta sake ganin duk wani motsin da tayi na barin gidan a yanzu za’a kama ta ne…inkuma ta bari wannan mutumin ya iso ɗakin matar shi dole zata bashi labarin mata da ƴa wanda yaranshi suka tsinto, “ya zanyi yanzu”? tayi wa kanta tambayar.
Alaji manga yana isa ɗakinshi yasa mu dr hauwa tana kokarin rage ACn dake ɗakin. sallamar shi ta amsa kana tace mutanen meeting sai yanzu a ke ganinku,wato kudai idan an ƙaɗa gangar siyasa baku da lokacin haɗuwa ku tattauna sai tsakar dare, dariya irin na manya alaji manga yayi kana yace “haba honey irin karɓar da za kimin kenan, bayan yanzu mutuminki ya ɗora min wani nauyin bayan wanda na dawo da shi daga wurin taro.
Yana magana ne yana ƙoƙarin rage kayan dake jikinshi, ɗan daka tawa tayi tace wane mutumina ne ya ɗora maka nauyi kuma.?
Kafun ya bata amsa wayar sa ta kuma ɗaukan ƙara ɗagawa yayi yana kallon screen din, ƙwafa yayi kana yai picking call din ya kara a kunnenshi ba tare da yayi sallama ba ” yace alaji sammani what again”?….. shiru yayi na kusan minti biyu sannan yace ohk naji ba damuwa a bar musu a kan 50 Millons ɗin sai mun haɗe gobe zamu tattauna” okey to muta shi lafiya.
Dr hauwa tace” wato har a gida ma mitin ɗin bai ƙarewa kenan”?
Yace kedai bari kawai hajiya kinsan harkar siyasa nan ta yanzu tana buƙatan sirri” wato ina baki labari yanzunnan Alaji s……. wani ƙaran wayar shi ta kuma ɗauka ba shiri yayi shiru, tsaki dr taja gami da ɗaukan wayar da niyyar kashe ta gaba ɗaya, amma sunan da taga yana yawo bisa screen ɗin yasa ta miƙa masa wayar haɗi da cewa” nasan za’ayi haka INNA CE kasan twins sun dawo ɗazu “
Yace”inna kuma cikin tsohon darennan? sun dawo kuma? mai yasa? tace kaidai amsa kaji me zata faɗa.
Kara wayar yayi a kunne daga ɗaya bangaren inna ta rabka salatin da ya sa alaji manga zare wayar daga kunnenshi. tace ” ɗannan kana ina to wllh kayi hanzarin zuwa domin dai an nemi ammaru da amanu sama ko ƙasa an rasa, kai kace yaran layan zana garesu daga nace musu ga nan yan mata nan a dangi suzo su nemi aurensu shike nan in gaya maka ɗannan yasassun yaran naka masu kama da lagwani suka fice daga gida to har yanzu basu ba labarinsu munyi nema lungu da saƙo na garinnan amma bamu gansu ba, to ni tsoro nama kar kinnapa ne suka kama su su talauta ka in shiga uku,”
Tunda ta fara magana bata tsaya ba sai da takai aya. a hankali alaji manga yace kiyi haƙuri inna, ai sun dawo gida tun ɗazu ma , inna ta kuma rabka wani salatin da ya di na farko tace sun dawo fa kace? to ai shikenan sun ma kansu kittt ta kashe wayar ta murmushi alaji manga yayi yace Allah kara nisan kwana innata.
da ameen dr ta amsa kana ta wuce bayi don haɗa masa ruwan wanka, koda ya fito wankan agogo ya kalla wanda ke nuna ƙarfe ɗaya na dare yace plsss dr make a hot coffee 4 me. fuska ta haɗe a take tace cofee kuma yallaɓai, dan tasan indai ya buƙaci coffee a irin wnn lokaci to zaiyi aiki a computer ne.
Tace haba mana ka haƙura da wannan aiki haka sai zuwa safiya its late ai yallaɓai. kuma da akwai labarin dazan baka a kan twins wanda suka dawo dashi. yace “duk mubari sai zuwa safiya kya bani labarin, amma yanzu kam kiyi abunda na sa ki”
Badan taso ba ta sauƙa ƙasa ta haɗo masa coffee ɗin ta dawo tasa mu har ya bude laptop ya fara aikinnasa. ajiye masa tayi ta hau gado ta kwanta tu juya masa baya. murmushi yayi yaci gaba da abinda yake yi.
Adama ta nan tsaye jikin taga ta rasa tunanin me zatayi taji alamar ana sauƙowa ƙasa a ranta tace” shikenan ta faru ta kare , ta riga ta faɗa masa.’
Jin an wuce kofar dakin da take an bude wani ƙofar yasa ta sauƙe wani ajiyar zuciya ba a ɗau lokaci ba taji an ƙara haurawa sama.
Ta nan tsaye har taji ƙafafunta sunyi tsami domin kuwa sun kumbura sunyi suntum suntum amma ta kasa zaune ta kasa tsaye a haka har agogo ya buga karfe biyu na dare. Zuwa wannan lokaci duk ta fice daga hayyacinta tsabar wahala, gaijiya, da kuma tunanin neman mafitabda suka mata rubdugu.
Cikin nutsuwa ta nufi hanyar bathroom ta shige ta kama ruwa kana ta dauro alwala ta fito ta shimfiɗa sallayar da ta gani nannaɗe akan bedside drawer,ta dauki hijabinta ta saka ta kabbara sallar isha’ i da ya kubce mata koda ta idar ta daɗe tana addu’ar neman mafita a wurin Allah kana ta miƙe ta yi shafa’i da wutr, nanma tayi ta yabo da jinjina wa ubangiji mai kowa mai komai sannan tayi addu’o’i masu tarin yawa, ta kuma yiwa iyayenta addu’a da roƙa masu rahamar Allah da haske da yalwa a cikin kabarinsu ta karishe tana zubda kwalla na tuna irin chakwakiyar da rayuwarta ke ciki, da kananun shekarunta gashi ba mataimaki, nan taci gaba da azkar har taji kiran assalatu da wasu massalatai keyi.