AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin sanyin murya suheer tace “habeebi!, bada gangan na kashe wayar ba, inda muka je basu da service irinna wayata shiyasa, tunda mukaje kuma bana jin dadi.” Yace subhanallah meke damunki? meyasa baku dawo ba? amma kinje asibiti ai ko? a jere ya mata tambayar kuma a rikice, gyara kwanciyar ta tayi a kan doguwar kujerar tana lumshe ido, a hankali tace, “eh naje asibiti anduba ni,” da sauri yace meke damunki sukace wai? “kara tamke ido tayi saboda bata jin dadin karyar da take shirga masa, a hankali tace “wai malaria suka ce” yace malaria kuma kinbari sauro sun ciza minke ko?” ohk zan shigo gobe da safe insha Allah saimuje asibiti , sleep tight now naga kin gaji sosai,” to” kawai tace mishi, wani dogon kiss ya aiko mata ta wayan wanda yasa ta bude lumsassun idanunta da sauri, tace “na gode habeebi” yace na gode kawai ko? ok wata rana zaki rama minne, dream of me baby, gud night. kitt ya kashe wayar.

Mikewa tayi daga kwancen ta zauna akan kujerar, tana tunani karyar da ta mishi, batajin zata iya fada masa gaskiyan abunda ya faru, tabbas wayar ta ba caji lokacinda suka iso goruba, tunda suka je kuma abubuwa keta faruwa ba wanda ya samu nutsuwar tunawa da waya har saida suka dawo, dawowar tasu kuma gaba daya gidan ya canja, yazama kamar wani gidan prison tamkar sun sayar da walwarsune tun shigar su adamawa har suka dawo, tunda suka dawo anty hafsa tayi isolating kanta, bata fitowa ma bare tayi magana, ammi kuma suna ganinta amma bayan gaisuwa ba abunda yake kara hadasu, kawu lamido kuma annemeshi wurin aiki, tsakaninta da fareeda ne kawai suke dan magana shima baya wuce eh ko a’a, gaba dayansu sun rame kamar wadanda sukayi wattani suna jinya.

Rasheed na kwance sambal cikin wani dogon gado mai kama da kujera a bakin swimming pool na gidanshi, yadan zarce gadon kadan tsabar tsawonsa, sanye yake da three quarter wando kalar army green, sai fara kal din singlet, murdadden jikinshi wanda ya gina ta hanyar gyming yana bayanne, headphone ne makale a kunnenshi idanunshi a rufe ruff, karatun qur’an yake saurare daga sheikh shureim cikin suratul kahfi, yana yawan sauraron surar domin yana sashi nutsuwa sosai, a hankali kyawawan lips nashi ke motsawa yana bin kira’ar, buba ne ya shigo wurin domin ya san anan za’a samu boss dinnashi airin wnn lokacin, tare suke da wani mutumi wanda Rasheed yabawa izinin bin kwakwafin suheer duk inda ta shiga ko tafiyar da sukayi ma tare da wannan bawan Allah suka tafi amma su basu sani ba.

Saida rasheed yada bubbuga gefen gadon da yake kai kafun ya bude ido ya kallesu, domin duk sallamar da suke kwadawa baiji ba. wanda yasa yabi su suheer adamawa ne ya bashi labarin duk abunda ya faru, dan jimm yayi na tsawon lokaci, kafun ya dago ya na murmushin gefen baki kana yace “Not bad, I like it. aikinka yana kyau, kaci gaba da sa wa duk wani mitsi nasu ido sosai, wasu makudan kudi ya fitar ya mika masa kana ya koma ya jinginar da kansa hadi da lumshe ido again. Nazarin bayanin da mutumin yabashi yashiga yi, dan tsaki yaja a ranshi yana cewa “there’s heartless people everywhere in the world ashe, shi ya dauka a rayuwar shine kawai aka samu irin wadannan mutanen, mtsss ya kuma jan tsaki, what kind of father he is?, ya dade yana tunanin maganganun da investigatorn shi din ya sanar masa daga karshe dai watsar da batun yayi ya mike ya nufi cikin gida, he need to freshen up before maghrib.

A bakin kofar ya tsaya ya kusa minti biyar tsaye wajen baison shiga su hadu da ummie, baya ya koma kadan yana karewa hadadden ginin nasu kallo a fili yace” dole ne innemi contractors suzo su duba min wurinnan idan zai yiwu a samun lifter ta waje wanda zaike daga ni direct zuwa hawa na biyu ba sai na shiga ta cikin gidan ba,….da daddare da kyar rasheed ya samu yayi bacci saida ma ya hada da shan magani,gaba daya labarin da aka bashi dazun yaki barin ranshi, duk kokarin da yayi na hakan kuwa.

Bayan kwana biyu, iyayen habeeb suka zo tambayar auren suheer,…lamido da wasu abokanshi biyu ne suka tarbi bakin, ba tare da jan magana ba yabawa habeeb tunda yaga tana sonsa, godiya iyayen habeeb sukayi inda daya daga cikin wadanda suka zo neman auren ya yabawa lamido da cewa “gskiya mun gode kuma munsan danmu yayi dacen samun iri mai kyau domin kai din uba ne na gari ga dukkan alama yayanka sunyi dace da mahaifi na kwarai, zuciyar lamido ne ya bada sautin das das, mahaifi, ya ambata a ranshi yanxu kowa dauka yake shine mahaifin yarannan fa, karfa hakan ya jawo matsala a gaba kodai ya fada musu ne, amma zanyi shawara da hafsa da kuma adaama, da haka ya taushi zuciyar sa ya fasa fadi musu gsky, kudin tambaya suka bayar dubu hamsin, inda suka tabbatar musu mata zasu kawo kayan tambaya gobe, sun kuma tsaida lokacin biki wattani uku masu zuwa,.

Kamar yadda suka fada washe gari kannen asabe biyu da kuma yayar mamman daya suka kawo kayan tambaya, akwati biyu cike da kayan kwalliya irin na mata, da kuma turaruka, sai sauran kayan dangin su minti da goro da kuma gishiri. hannu bibbiyu adama hafsa da kuma wasu kawayen ammi biyu suka tarbe su, sunci sun sha masha Allah aka rabu ana farin ciki, suka koma suna bada labarin irin tarban da akai musu, asabe ta ringa murna har hakan ya basu mamaki, dan kowa a dangi yasan bata son wannan auren,har cewa tayi zata yiwa habeeb baki matukar ya auri suheer, amma cikin yan kwanakinnan sai rawan jiki take yi akan abun itace ma ta matsa akan azo a yi tambayar asamu a yi bikin ko hankalin habeeb dinta zai kwanta a cewar ta.

Bayan yan kawo sa rana sun tafi kuka Suheer ta kamayi wai ita tayi karama da aure, bayan ga fareeda da ta girme ta ma batayi aure ba, don haka a daga ranar da aka sa yayi kusa, zata jira fareeda sugi auren tare, dariya fareeda ta dinga yi harda rike ciki, rabon da tayi dariya haka har ta manta, anty hafsa ne ta matso ta rike shoulder dinta tana kallon ammi tamata signa tace tana kwaikwayon muryar suheer” gaskiya kam ammi yaushe ma suheer ta girma har za’a mata aure, kawai a kara lokaci kinga by then ta girma sai habeeb yayi na biyu da ita”, da sauri suheer ta dago kanta cikin shagwaba ta wara ido tace anty na biyu kuma?. to ni na hakura ayi kawai, me zasuyi inba dariya ba, sai lokacin ta ankara da irin katobarar da tayi da sauri ta mike ta shige dakinsu, ammi tace “jita da Allah waiwani a daga auren ashe duk borin kunya ne, wani dariyan suka kuma kyalkyalewa da…….. da daddare bayan sun gama dinner anty hafsa ta fito da wani jotter da biro a hannunta, wuri ta samu a lalo ta zauna itama ta dubi ammi kana tace “Adama ya kamata mu fara lissafi fa kar bikinnan yazo ya dabaibaye mu, kinsan wannan shine na fari bana sin muji kunya a idon kawaye”, ammi tace gaskiya kam to yanzu me ya kamata mufara?.

Murmushi lamido dake kokarin shigowa palon yayi yace hooo kaga iyayen amarya wato kar aji kunya a idon kawaye ko? hafsa tayi dariya tace “eh mana yayaaa kasan mata da bidi’a ai, a take suka fara lissafin yanda abubuwa zasu kasance, ammi tace “ko zuwa next week sai muje bank in ciro rabin ajiyan danake yi tsawon shekaru na ribar sana’ata domin zuwan irin wannan ranar, saura rabin kuma na fareeda ne, dan shiru tayi sai kuma tace “naso ace ita na fara aurarwa amma ba haka Allah ya tsara ba anyways Allah ya zaba mata miji na gari itama kafun lokacin in hadasu duka in aurar, na tabbata ba karamin farin ciki zanyi ba idan har hakan ta kasance. Jinjina kai hafsa tayi a ranta tana mamakin hali irinna adama kafun a samu mai irin halinta a wannan zamani namu gaskiya sai an tona, don ko ita kanta hafsar tana jin bazata iya rike dan wani irin rikon da adama tayiwa fareeda ba. me za tayi ta sakama ta abunda tayi cikin rayuwar yarta wadda har gobe fareeda gani take cewa ammi ne ta haife ta kawai drama ce ake shiryawa da aka ce ba ita ce mahaifiyarta ba. gaskiyan mash iya magana da su ka ce “is good to be good”. Da ace bata taimaki adama ba lokacin da ta ganta kwance da yarinya gefenta da kuma ciki ba, da Allah kadai yasan inda zasu fada, ashe ma yarta ta taimakawa, tabbas it pays to be good.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button