AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwanci tashi asarar mai rai, sai gashi har wata ukun da aka sa ya cika, sosai ake shiri both bangarorin, anty hafsa ne tayiwa suheer gaba ki daya kayan kitchen daga kan freezer gas cooker har zuwa kan cokali kuma zababbu ta mata wadda ko yar shugaban kasa sai haka, ba karamin dadi ammi taji ba don saida ta rungumi hafsa ta fashe da kuka, kukansu sukayi tare suka share hawaye suka ci gaba da hidimdimu to sune dangin junansu dama, yayinda ammi ta zage tayiwa yar tata setin kayan gado da kujeru na gani na fada kirar dubai, da sauran decoration na gida, kawu lamido kuwa kayan gara ya mata ba na wasa ba komai buhu buhu aka zo aka jibge, kana ya biya makudan kudi a wani cuisine zasu ringa kawo abinci daga fara hidiman biki har a gama baza’a dora tukunya a gidan ba, ruwa da lemo na roba kuwa katan katan yasa aka ringa jibgewa, sosai lamido ya zame wa suheer uba, ba karamin farin ammi tayi ba da hakan,kuma ya shirya mata events har kala uku, za’ayi walima ranar laraba, ayi kamu ranar alhamis jumma’a ayi dinner, washe gari asabar a daura aure a mika amarya dakinta kowa ya kama gabanshi.
Bangaren fareeda kuwa itace kirjin biki, don haka tayi tsalle ta dire ta ce dole kawu lamido ya kara musu event daya, suna so suyi bridal shower, ko kuma ayi cancelling daya sai a mayar bridal shower, anty hafsa ne ta daure mata kugu, ta hanyar cewa “eh wllh yayaa nima abunda yake raina knn,” dole ya kara musu kudi dan su shirya bridal shower dinnasu.Habeeb kuwa kusan kullum sai ya zo wurin suheer, tare suka hada lefe, duk wani abunda zaiyi a gidanshi da ya gina mai 2bedrooms,parlour, da kitchen sai dan madaidaicin tsakar gida, sai ya nemi shawaranta hatta kalar pentin da zai goga saida ya bata zabi. Saidai abunda yake damun suheer shine kullum suka zauna sai ya ringa cemata zuciyar shi yana yawan tsinkewa, ji yake kamar zai rasa ta, wnn abu ba karamin daminta yake ba, lallashinshi take yi sometimes tace feelings ne kawai da sabbin ango ke yawan ji, saidai ya gyada mata kai kawai, amma shikadai yasan me yakeji akanta.
Rana bata karya, yau laraba yau ne kuma zasu fara shagali, fareeda tabi ta gayyato tsofaffin kawayensu na makaranta gaba daya, sai wasu daga cikin yayan kawayen ammi da anty hafsa, shirin bridal shower sukeyi wanda zasu fara daga karfe biyar zuwa karfe tara na dare, mai makeup ne tazo ta tsantsarawa suheer ado ba wani heavy makeup bane amma tasha kyau, kyawunta na jinin fulani da larabawa ne ya fito sak, wani dogon riga mai kama da wedding gown fari kal tasaka da gyalenshi, amma gyalen net ne shi, wani crown aka samata akan net din mai fararen stones masu walwali, kana aka rataya mata wani tag wanda aka rubuta bride to be a jiki, masha Allah ba karamin kyau tayi ba,sauran kawayensu kuma sukayi shigar wani yadi mai dan rawa kalar dark yellow duka doggin riguna, suka daura net fari akansu suma, nan suka rankaya imda suka tanada domin bikin, shagali sosai aka sha a wurin, yan mata sun sha rawa inda, dj ya kashe musu kida, bayan raye raye aka ci gashashen naman rago da drinks sai hotuna ya biyo baya, hotuna suka ringa yi kamar ba gobe, a gajiye tibis suka dawo gida kusan karfe goma, washe gari alhamis akayi kamu, anan tsakar gidansu akayi decorating yaukam shigar fulani amarya tayi, tayi kyau har ta gaji kawayenta suna zagaye da ita da sauran yan uwa, dangin habeeb ne suka iso da kayan kamu nan aka kamata shima akayi shagali yadda aka saba aka watse, washe gari jumma’a walima akayi da safe yau kam shigar abaya tayi red colour, sosai farar fatarta ta haska a ciki, gashi tasha gyaran jiki na musamman dama sai tashin kamshi jikinta keyi,malamai mata ne suka gabatar da lacca akan hakkokin miji akan matarsa, sosai suheer tasha kuka da jin laccocin har saida idanunta suka dan tasa, fareeda ne ta leko ta cikin mayafin da ta rufe fuskarta, tace ” me haka kikeyi rabin jiki, ko so kike adon da za’a miki anjuma na dinner yaki yin kyaune? plss ki dena kukan haka………. Da dare misalin karfe bakwai motocin dazasu kwashi yan zuwa dinner suka iso, anko sukayi ita da habeebinta na zuwa dinner. Duk yadda tayi da mai makeup akan karta mata slight makeup ki tayi ta zauna ta tsara mata kwalliya as bride she is, a cewarta yau ranar ta ne dole ta fi kowa kyau a wurin, aiko tayi kyau na musamman, wani yadi ne zasu saka cream colour ne aka mata dogon riga dashi, daga sama ya dan kamata har zuwa guiwa, daga guiwa zuwa kasa kuwa a bude yake kamar dawisu, yayinda bayan yake jan kasa sosai gaban kuma yake cib cib,gaban rigar yasha adon stone work, domin tela na musamman ne ya dinka shi, gwagwaro aka nada mata da dankwalin da shike babba ne kuma ansa wani sinadari ta ciki hakan yasa ya dagu sosai, wuyanta yasha adon wani katoton sarka da dankunnenshi mai kirar diamond, hannayenta da suka kawatu da zanen lalle baki da ja, sunsha manyan aworworaye da kuma zabuna, masu daukar ido, kallo daya bazaka gane suheer ba tsabar kyau din da tayi saitafi kama da arab din gaba daya, takalmanta ma cream kolo ne mai adon duwatsu aka sakala mata wani dan jaka mai shape din sipili shima gaba daya zagaye yake da stones din bulbule ta akayi da turaruka kana aka makala mata wani net shima mai adon stones din masu walkiya a keyarta ya zama a iya bayanta kawai ya tsaya yana dan lilo kadan kadan iya kyau suheer tayi shi a wannan lokacin, su fareeda kirjin biki kuwa shigar wani purple din lace sukayi riga da siket ita da sauran kawayensu, suka daura pink head a kansu suma sunyi kyau sosai, a hankali suke taku har zuwa jerin gwanon motocin dake jiransu, bayan wani luntsumemen mota aka bude wa suheer, ta shiga, rumtse ido habeeb yayi jin wani irin mahaukacin kamshi ya bade motar cikin nutsuwa ta daidaita zamanta a bayan motar, ajiyar zuciya mai karfi ya sauke da sauri kuma yace anya masoyiya baza’a fasa dinner dinnan ba kuwa,? cikin jin kunya ta dago suka hada ido, shima sanye yake da yadi kalan na jikinta, amma nashi yar ciki da wando da kuma babbar riga ne, anyiwa babbar rigar aiki da bakin zare don haka yasa hula takalma covers agogo duk bakake, cikin sakwan biyu ta gama mishi kallon duka, cikin sanyin murya tace don me yasa”? yace “kishi nake, ina kishin ki sosai masoyiyata, kallon da na miki yanzu ya kara tabbatar min lallai ni mai sa’a ne a rayuwa, domin ke ba kalan matar talaka mai aiki a karkashin wasu bane suheer, plsss duk tsanani karki gujeni domin komai na iya faruwa dani matukar kika gujeni, a take muryarshi yayi rauni.
A hankali ta kuma cewa wani irin magana kake haka habeebi, meyasa zan guje ka bayan gobe ne daurin aurenmu, habeeb yace komai na iya faruwa suheer zuciyata tana yawan fadamin kamar za’a rabani dake,” shiiit tace mishi tana daura yatsa akan bakinta, kana tace bamai raba ka dani insha Allah iam yours forever and ever okay?. Da haka ta samu ta rufe bakinshi har suka iso hall din dazasu gudanar da taron, taro yayi taro isowar amarya da ango kawai kawai ake jira, suna isowa kuwa dj ya sauya sauti zuwa kidan amarya da ango, a hankali suke taka dogon carpet din da aka shimfida musu tun daga bakin kofar hall din har zuwa hightable, tapi kawai kakeji rap rap rap ta ko ina har suka iso suka zauna, hall di cike yake da manyan mutane mata da maza ga kuma manyan yan mata da gogaggun samari wanda suheer ta rasa ina aka samosu dan sam basuyi kama da abokan habeeb ba, kuma tasan fareeda bazata gaiyato irin wadannan ba.