AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Can na hango mama asabe uwar ango anci goggoro sai zufa take hadawa, tun shigowar habeeb da suheer a hankali ta lallaba ta fice daga hall din wani dan lungu ta samu ta takure kana ta fara daddana wayarta kirar burin kwaila ta kara a kunne, ringin biyu aka daga daga daya bangaren, da sauri tace hello ban gane ba fa naga abu sai kankama yake banga wani yunkuri ba, kuma ba haka mukayi daku ba, karfa ku yaudare ni da bazan taba aminta da wnn kwamacalar ba, daga daya bangaren aka ce mata kedai kizuba ido kiga abunda zai faru karkiyi gaggawan yanke hukunci, dan haka ki jirayi nanda mintuna kadan, kiit aka kashe wayar, tana share zufa tace da dai yafi kam, ta juya ta koma cikin hall din,………Bayan kamar minti talatin, wata hadaddiyar mota ce fara kal ta yi parking a bakin hall din, kafafunshi dake sanye cikin bakaken covers ya zuro kafun ya fito gaba daya sanye yake cikin wasu tsadaddun coat farare tas da necktie baki, hannunshi sanye da agogon fata shima fari, yau dai anyi sa’a baisa hular tashi na jaraba ba, sai baki wuluk din gashinshi masu nadi nadi wanda yasha gyara sai walkiya yake zubawa, kare wa hall din kallo yayi yana iya jiyo kide kide da hayaniyar mutane dake tashi a ciki, yamutsa fuska yayi hade da furta “disgusting.”…. Cikin taku mai cike da kasaita da kuma izza ya nufi mashigar wurin taron…..

????????????Auren Fansa????????????

Book Two.

        By 

Ummu Fadeela.

Typing????

Page 43 / 44.

Cikin takun kasaita ya nufi cikin hall din, cakk ya tsaya lokacinda ya rage baifi taku biyu ba ya shiga, sakamakon jin sunan boss, da yayi buba yana ambata.

Da sassarfa buba ya iso wajen yace “boss meza kayi anan kuma? tunda naga fitowarka na kasa samun nutsuwa har saida nabi bayanka dan kar kaje kayi wani aika aikar a kan hanya,” “good job”, cewar Rasheed kana yayi gaba ya barshi a wurin, cike da izza yake taku har ya isa cikin wurin taron, caaaa idanun yan mata sukayo kanshi, kowa kokarinta a wurin rasheed yasan da zuwanta. Kikam ya tsaya a jikin wani pillar dake tsakiyar hall din yana karewa suheer da habeeb dake kan hightable kallo, kai da ka gansu kasan ba karamin farin ciki suke ciki ba. ba abunda ya fado masa a rai sai kalamanta, a kansa,

( I promise i will get you to punish, sai doka tayi aiki a kanka, sai anmishi adalci,). Da dai sauran abubuwan da ta ringa fada. Rumtse ido yayi tunawa da yadda yan sanda suka sa masa ankwa a gaban dubban masoyanshi, kana a ka jefa shi a cell, na tsawan kwana biyu, sannan aka kuma rankaya wa dashi kurkuku shima sati biyu, what a disgrace, ya furta a hankali yana cigaba da kallonta, tana murmushi kasa kasa, saboda maganar da habeeb yake fada mata, rasheed a ranshi yace kiyi farin cikin ki na karshe a duniya SUHEER LAMIDOOOO.

Hango anty hafsa yayi da ta cakare cikin wani uban sun lace fari ta kafa bakin gwaggoro tana tahowa wurinshi, ammi ne dake can karshen hall din ta takure waje daya dan sam bata so zuwa wurinba a cewarta na yara ne, amma hafsa ta dage saida tazo, itace ta fara hango rasheed din, dan haka tace da hafsa tazo ta sama masa wurin zama.

Isowarta yayi daidai da kiran da mc yayiwa amarya da ango, ana bukatarsu a tsakiyar fili, cikin nutsuwa tace “sannu da zuwa yallabai, ga can wajen zama in bazaka damu ba,…Dan rusunawa rasheed yayi yace barka da dare anty, dama na tura can gidane a sanar da fareeda cewa ta shirya gobe za afara bukatanta a location, to sai dan aiken ya dawo yake sanar min ai ba kowa gidan yau ake bikin kanwar ta, wama take da suna, yayi maganar with carelessness, shiyasa nace to ni bari inyi gaban kaina inzo tunda abun ba gaiyyata.

Anty hafsa tace” aiya kayi hakuri abubuwa ne suka sha kanmu shiyasa ba kowa yasan da bikin ba, amma munji dadin zuwanka, plsss ka iso ga wurin zama.

Rasheed ya sake sunkuyar da kai kamar muminin gaske yace ” a babu komai anty, bari inyiwa amarya Allah sanya alkairi zan wuce domin ina da abubuwan yi dayawa, murmushi anty hafsa tayi tace amma da ko ruwa zakasha ai,” yace “ba komai anty”.

Gyada kai buba yayi a ranshi yana cewa “bravo”. sai a lokacin fareeda ta dauke idanunta daga kansu, domin tun shigowar shi ta gansu saidai ba yadda zatayi ta matsa a inda take domin ita ce na hannun daman amarya.

Cikin takun kasaita ya iso inda suke, wanda yayi daidai da tashin suheer da habeeb dan amsa kiran da mc ke masu su fito tsakiyar fili, tafiya yake cike da takama kasancewar filin cike da yan mata da samari an fara rawa hakan yasa ya kutsa ba tare da yasha wahala ba, suna tsaye ana masu liki wani abokin habeeb dake gefe ne ya ke mishi magana amma baiji ba, hakan yasa gaba daya ya maida hankalinshi wurin abokinnashi, daidai isowar rasheed kusa da suheer, ya matso dab da kunnenta yadan rankwafa daidai tsawonta, ya kuma karkacewa bakinshi ya zama saitin kunnenta, cikin rada da wani salo ya furta mata “CONGRATULATIONS amarya” a cikin kunnenta, wani irin bugawa kirjin suheer yayi jin magana a kunnenta unexpected kuma da muryar wadda batiyi zato ba, cike da rudani ta juyo da sauri dan tabbatar da wanda take zato, cikin rashin sa’a dogayen karan hancinsu ya hade da juna yayinda dan karamin bakinta ya makale a kan nashi bakin, kyarass, kyarasss kyarasss sautin daukan hoto naji,duka wnn ya faru ne ciki kasa da second biyar, da sauri ta matsa, wanda yayi daidai da juyowar habeeb, devilish smile rasheed yayi yana mikawa habeeb hannu.

A sanyaye ya mika mishi nashi shima yana mamakin me ya kawo wnn kuma nan, rasheed yace “congratulation ango,” murmushin yake habeeb yayi yace, “tanks”.

Komawa gefe rasheed yayi ya harde hannu a kirji, fareeda ne ta samu yin escape daga inda take ta matso kusa da rasheed tana fara’a… Magana sukayi na kusan minti biyu akan shooting nata gobe ciki jin dadi tace anma ranka ya dade gobe daurin auren rabin jiki, rasheed ya jinjina kai yace “ohk ba damuwa zan iya sawa a dage daukan sai zuwa jibi…

Har amarya da ango suka koma teburin su suheer bata fita a shock din da rasheed ya sa ta ba, wani mai daukan vedio ne ya matso gaban amarya da ango yana murmushi yace ” ku gyara zan muku dauka na musamman, hade rai habeeb yayi ganin yadda camera man din keta kallon cikakkun kirjin suheer, kallonshi tayi itama ganin yadda ya tsare gida, murya can kasa tace “habeebi fushi kake yi ko,”?.

Da sauri yace” ehh” suheer tace sorry plss habeebi bani na gaiyaceshi ba, infact ban…… katseta yayi yace ni ba akan abunda nake fushi ba kenan, tace ” to mene”? yace ina fushine akan irin kyan da kika yi gashi maza sai kalle min ke sukeyi, rufe idanu tayi da sauri, camera man dinne yace da habeeb yadan matso kadan saboda hoton yayi kyau, matsowa yayi sosai jikinta har yana jin numfashinta, hakan yasa suheer kasa jurewa ta dan juya fuskar ta gefe tana murmushi, jin abinda habeeb yake fada mata kasa kasa.

Caraff idanunta ya fada cikin na rasheed dake tsaye har lokacin yana harde da hannuwa akan faffadan kirjinshi, tuni camera man yadan karkatarda idon camerar shi.

Murmushi irinna masoya rasheed ya jefowa suheer, kana ya hada babbar yatsar hannunshi da kuma manuniya wuri daya sai kuma ya ware sauran ukun yana nunta dashi, wato alamar you look so good, duk yadda suheer taso janye idanunta daga kanshi kasawa tayi tsabar mamakin da ya sata a ciki, hakan ya bawa rasheed damar sake kai hannunshi baki yayi masu kiss kana ya huro mata, wato blowing kiss, da sauri ta rumtse ido ta kuma budewa, yayinda mai daukan video yake ta aikinshi anbar habeeb da sakakken baki, duk abunnan dake faruwa ba wanda ya ankara dasu sai buba kawai dake ta aikin gyada kai kamar kadangare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button