AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Juyawa asabe tayi da nufin komawa cikin dakin taron bayan tafiyar rasheed, turuss tayi ganin kulu kanwar baban habeeb tsaye tana ta girgiza, kokarin boye mamakinta asabe tayi tace”haaan kuluwa me kike a waje bayan gacan jama’a cike a ciki?, kulu tace “so nake insan me kike aikatawa asabe don nasan tsabb da wani munafurcin da kike kullawa tunda aka fara bikinnan nake lure dake,” asabe tace “to yau naga sabon salo ni jikar mutum hudu, kuluwa bikin habibun nawa kika sawa ido ko me kike nufi, to ahirr dinki wllh wato kaidin naku irinna dangin miji zai biyo ta kaina knn to nafi karfinki kin sani, banda ma ina rufawa dan uwanki asiri har ke kin isa ki ganni kice lure kike dani, to akan me?.

Wani irin shewa kulu tayi tace “da kyau asabe, da kyau, ke kinsanni sarai kuma kinsan na sanki nima a tafin hannu na kike, zaki fada min me ya hada ki da wannan attajirin har kuke ambaton miliyoyi ko ko saina fasa kwan?.

Wani irin zufa ne ya karyo wa asabe domin sarai tasan kuluwa ba kanwar lasa bace tun dama, balle yanzu da ta zama yar bariki a karkashin gadar legas, tana share zufan goshinta tace duk baikai ga haka ba ai kuluwa idan mun tashi daga nan zakiji komai,” kulu tana tura dankwali gaban goshi tace “da dai yafi”, suka rankaya suka koma cikin taron, karfe goma aka tashi dinner din, gaba daya a gajiye suka koma gida, a bangaren suheer kuwa tunanine ya mata yawa ga wani irin faduwar gaba da take ji, duk hayaniyar da yan mata keyi a dakin bata cewa ko uffan, fareeda ne ta taba ta tace ” what happen rabin jiki, ain’t you happy?. girgiza kai tayi tace “sweetheart haka kawai gaba na keta faduwa na rasa dalili”.

Fareeda tace “fargaba ne, kina fargaban tafiya ne kina tuna gobe warhaka bama tare, saikuma ta rungume ta tace “keep saying Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un duk sanda kika ji hakan, zai dena insha Allah, ammi ne ta leko ta gansu, girgiza kai kawai tayi tace, ” yakamata ku kwanta haka don kun samu tashi da wuri gobe”. Da “to” suka amsa mata dukkansu.

Rasheed saida ya gama gaba daya shafe shafen shi kamar wata mace tsabar kwainane a goge can a shafa can kafun yasa wasu pyjamas masu taushi bakake dogon wando me da riga shima mai doguwar hannu kasancewar ana sanyi kana ya shige cikin lallausan duvet nashi, yana kokarin lumshe ido wayar shi tayi kara alamar shigowar sako, dauka yayi yaga sako aka tura mishi ta wassap, budewa yayi ganin sunan wanda ya turo mishi sakon yasa shi saurin kokarin budewa, ido kawai ya tsurawa screen na wayar shi yana kallon abunda aka tura mishin har ya kare bayan kusan minti biyar, sake playing yayi yana kallo shima har ya kare, kuma budewa yayi kamar wanda bai fahimci meye a ciki ba yana so ya tabbatar, sau hudu yana kallon videon mai tsawon mintina biyar, wani murmushin gefen baki yayi yace “muje zuwa”, kana ya lalubo wata numba a cikin wayar ya ya danna kiraya kara a kunne.

Ringing daya aka daga dama jiran kiran yake, cikin biyayya yace “barka da dare yallabai, ina fatan aikin yayi yadda kake so?.” Dan shafa beard nashi rasheed yayi yana cigaba da murmushi yace “aiki yayi kyau salisu, amma ina son adan kara fara’a a fuskarta, kuma nanda karfe sha biyu ina son a saki bidiyon a duk wani dandalin media, sannan ka tabbatar da ka rubuta duk abunda na fada maka, but make sure ka toshe duk wata kofar daza’abi domin binciko wadda ya saki bidiyon.” cikin girmamawa salisu yace angama ranka shi dade nanda awa biyu bidiyonnan zai zaga duniya gaba daya bawai cikin kano kawai ba. Rasheed yace “good job”, a bayyane yace “wasa farin girki yan mataaa”.

Sha biyu ciff salisu ya saki bidiyon da ya dauka dazu a wurin dinner, saidai ba karamin kwaskwarima yayi wa bidiyon ba, inda bakin suheer ya taba na rasheed bisa kuskure aka mayar kamar kissing juna suke yi, inda ta juyawa habeeb baya daza’a masu hoto har rasheed ya aiko mata da blowing kiss shima aka kara fara’ar fuskarta a wurin kana inda ya rungume ta sam ba’a nuna asabe ta take mata riga ba gaba daya dai abun an yayyanke wasu wurare kana an kakkara wasu.

Maryam kanwar habeeb tana kwance a daki tun bayan dawowarsu daga dinner,wayarta ne kare kunnenta suna hira da saurayinta, kara kankace murya tayi tace ” Allah da gaske nake mama tana maganar da angama auren yaya ba bata lokaci za’ai namu”……….. dan shiru tayi saikuma tayi murmushi tace “da gaske?”…Hira mai dan tsayi sukayi har zuwa shabiyu da kusan rabi kafun suka rabu, juyi ta kama yi akan gadon ganin bacci yaki daukarta kawai sai ta bude datan ta ta hau fesbuk, abunda ta fara cin karo dashi shine ya masifar daga mata hankali, domin tuni bidiyon rasheed da suheer ya yadu sai sharing ake, kana duk wanda yazo zai share da abunda yake rubutawa gwargwadon abunda ya fahimta akan bidiyon, kamar dai yadda mukasan social media take.

Dau biyu tana kokarin bude bidiyon amma yaki, sai ana ikun ta samu ya budu, ido ta zaro da karfi tana kallon cikin wayarta da karfi tace karyace wllh. Duk yaushe akayi wannan alhalin mutane suna cike wurin, wllh wnn hadine, asabe dake ta kokarin inda zata ji dan pimm ta taso harda dan gudu ta nufi inda maryam take tana “ke lafiyar ki? ko dai kinyi gamo ne zaki kama surutai cikin wannan daren. Ba tare da wani tunani ba maryam ta mikawa asabe wayar tace”mama ki gani ga wani sharrin da za’a laka wa amaryar yayaa habeeb, jiki na rawa asabe ta amsa yayinda wasu daga cikin dangi duk sun taso suma suma ta leken wayar, dafe kirji asabe tayi tana zaro ido kamar wacce taga abun tsoro, sauran yan uwa kuwa harsun fara yiwa suheer tofin Allah tsine,, a cewar su uwarta bata iya haihuwa ba, wata daga cikinsu tace “haba koda naji, wai wnn mai kama da balarabiyar ne habibu zai aura ba karamin mamaki nayi ba, to ashe ita din sauran wasu ce, wato su baza su iya aurenta ba, shine ta lallaba ta auri habibu saita koma su ci gaba da harkarsu, to ta Allah ba tata ba habibu baida hakkin kowa akansa, sauran suka caaa suna fadin haka ne yaya habi, kuma bari yaya mamman ya shigo da safe gaskiya wnn ba matar da za’a shigar mana cikin zuriya bane.

Wani irin ajiyan zuciya asabe ta sauke, a ranta tana godewa Allah tunda wayannan bakaken munafukan dangin mijinnata sun riga da sun gamsu to ai shikenan.

A gidan su suheeer dukkan yan matan suna kwance daki kasacewar sanyi ake sai dakin bai musu kadan ba, wasu na wayar dare da samarinsu wasu kuma na chart, wata kawar su salima ce ta zaro ido tace “what” Ashe Suheer lamido da Rasheed Matawalle yaudarar mutane sukayi sudin masoya ne. Da karfi fareeda tace “me”. Yayinda jikin suheer yadauki rawa dama kiris take jira.

Wata kawarsu ita ta kuma cewa tsna ksllon wayar ta” Abun boye ya fito fili tsabar yadda suka saba taba junansu, amarya suheer lamido ta gaiyacci saurayinta wurin dinner din din aurenta a kuma idon mutane suke harkarsu. Ai wnn karin hantsilowa tayi daga kan gado ta nufi kan salma fareeda ma ta nufo su.

Saudat ne ta kuma cewa laaaa, kai da gaske nefa ga wani “Love birds, a young gold business tycon and super star also rasheed ahmad matawalle w……. kafun ta gama karantawa har suheer ta juyo kanta ta wafce wayar tana kallon me suke gani, fareeda kuma wayar salma ta karba, a tare suka fasa ihun da duk jama’ar gidan saida suka garzayo dakin…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button