AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

JUMMA’AT MUFEEDA MY PEOPLE…..

????????????Auren Fansa????????????

Book   Two.

Page 47 / 48.

……..”What nonsense?” cewar anty hafsa bayan ta gama ganin bidiyon, tace “wannan karyace kawai irinna mahassada wadanda basa son cigaban mutum”, ammi kam banda inna lillahi ba abunda take ambata, cikin daga murya hajiya saratu kawar ammi tace kaida kaga wnn bidiyonma kasan hadashi akayi dan aci zarafin ta.

Cikin muryar lallashi ammi tace da su fareeda kowa yaje ya kwanta yanzu dare yayi zuwa safiya duk zamusan meke faruwa insha Allah…. Hafsa ku kuma muje acigaba da aikinnan kar dare yakumayi, kwanciya kawai suheer tayi amma ita kadai tasan halinda take ciki, gashi sai gwada layin habeeb take baya wucewa.

Washegari da misalin karfe bakwai na safe, lamido na tsaye tsakiyar falon ya kafe wayar dake hannunshi da ido kirjinshi sai bugawa yake, yayinda iyalannashi suke zagaye dashi. sau uku yana kallon bidiyon kafun yayi gyaran murya irinna manya yana kokarin calming kanshi yace yana kallon idon suheer, “garin yaya hakan ta faru?” caraf fareeda ta amsa tace wllh kawu ba laifin rabin jiki anan domin komai akan idona ya faru, nan ta basu labarin iya abunda tagani…..

Anty hafsa tace “hasbunallahu wani’imal wakeel, na gano abunda ya faru duk yadda akayi wani keson yayi blackmailing Rasheed, karku manta shi waye dole ne yana da makiyan dazasu so bakantashi kota halin kaka, shiyasa akayi amfani da wannan damar, kunsan su celebrities dinnan duk wani motsinsu sai andauka a waya, kai ko tari mai karfi sukayi sai anyada balle kuma ansamu babban labari irin haka, gashi kuma dama jama’a da dama sun san akwai jikakkiya kwanan baya a tsakaninsu shiyasa suka hada wnn bidiyon domin yawo da hankalin jama’a,,”

Da sauri ammi ta gyada kai tace “tabbas nima nayi wannan tunanin hafsa, fareeda tace ” wllh hakane anty, yanzu me abunyi?, suka hada baki wurin tambayar suna kallon lamido dake ta shafa goshinsa. Kallonsu yayi yace ” dole mu nemi mafita cikin gaggawa kafun wannan abun yayi yaduwan da zai riski habibu da iyayenshi, bazan taba burin abunda zai taba rayuwar yarannan ba, ya zama wajibi mu nemi way out nanda awanni biyu kafun lokacin daurin aurennan yayi.

Wani irin numfashi ammi ta sauke, wannan shine abunda ta kwana tunani hakan bai barta ta rumtsa koda da sakwan daya ba.

Da sauri anty hafsa ta mike kamar wacce aka tsikara tana kallon lamido wanda idanunshi sukayi jawur tace ” i found an idea yayaa,” duk ido suka zuba mata, taci gaba da cewa ” mezai hana mu je gidan rasheed mu tuntube shi akan maganar, kasancewar abun ya shafe shima nasan zaifimu daukan mataki da gaggawa, na tabbata bazai so abunda zai taba career dinshi ba, watakila zai fito media ya karyata labarin kaga shikenan yarmu ta fita a zargi, watakila kuma yadau wani matakin, maybe ma ya hada da shariya tunda ai bata masa suna akayi”, ta karashe tana murmushin samun mafita, dukkansu sun amince da bayaninta, fareeda tace ” shawara mai kyau anty, na tabbata zai dau mataki akai, koma watakila ya riga da ya dauka tunda ai sunada masu kai musu rahoto akan abunda ya shafe su.”

Lamido yace” cikinku wayasan gidansu rasheed din?” hafsa tace ahaff ai ba boyayyen wuri bane cikin anguwar nasarawa fa yake ai duk dinmu mun sani, yana kallon suheer yace “tafi ki dauko hijabinki muje, zaki gane gidan aiko?”

Gyada mishi kai tayi ta tashi a hankali ta nufi daki, ammi tana kallonshi tace amma kawunsu yau ne daurin auren fa, baikamata ta fita ba da dai kunje da fareeda,” wani kallon mamaki lamido ya mata kana yace “amma adama, idan ana cikin tashin hankali manta wa da batun al’ada ake. sannan wani karatun bai bukatan fassara.

Suheer ta fito sanye da hijabinta har kasa mai hannu kalar maroon, sosai ya haska farar fatarta dake ta sheki tsabar gyaran daya samu a dan tsakaninnan. kallo daya zaka mata ka gane bata cikin nutsuwarta, riko hannunta fareeda tayi tace ” you don’t worry rabin jiki, ba abunda zai faru ki saki jikinki dan Allah, anty hafsa tace ” bawai kuma kije kina jan jiki salalo salalo ba kamar talo talon da rashin lafiya ya kama baki zaki bude kiyi magana mai kyau kina jina ko?” jinjina kai tayi, hafsa tace ” to maza jeki yana jiranki a waje ki kula da kanki sosai Allah ya tsare. Da ameen ta amsa a ranta.

Habeeb na tsugunne gaban iyayenshi kanshi a kasa idanunshi sun kada sunyi jawur kamar garwashin wuta, ji yake kamar tafasashen ruwa suke watsa mishi a duk sanda sukayi mar magana, how he wish hawaye zai zuba daga idanunshi watakila daya samu sasaucin azabar radadin da yake ji a kirjinshi, shi baiga bidiyon ba, kuma baison kallo domin yasan bazai jurewa kallon ba, but what he believes is karya ne, yasan karya akeyiwa suheer, yasanta yasan abunda zata aikata da wanda bazata aikata ba, “bada habibu nake magana ba?” cewar malam mamman.

Da kyar ya dago kanshi da yai masa nauyi yace “baba wannan labarin karya ne fa, kawai makiya ne suka shirya hakan don kawai aci zarafinta, amma baba suheer bazata aikata hakan ba. Asabe tace ” iyye lallai ka tabbata dannan wai me yarinyar nan ta baka ne haka? wato karya mu iyayenka muke maka kenan,?” ….. Yace “ba haka nake nufi ba mama ku fahimce ni mana, yanzu saura yan awanni a daura aurennan ku bari sai bayan daurin auren ayi binciken kamar yadda kuka bukata, mamman yace “habibu inkai ka makance ne to mukam rass idanunmu suke dan haka dole a janye daurin aurennan sai angudanar da bincike, domin bazamu yarda da bara gurbi cikin zuriyar muba, kanin mamman ne yace “amma yaya da andubi maganar yaronnan ta yiwu fa magauta ne kawai keson rabasu, kasan dan yau, mamman yace “banason zancen banza rabi’u ko bada kai mukaga bidiyonnan bane yanxu, dole ne ma a daga daurin auren har sai mun tabbatar da gaskiya.

Da gudu maryam ta shigo gidan tana zare idanu jikinta na ta rawa duk ta firgice, gaba daya daga saman kanta har zuwa kan kafofinta kullin wake ne yama ta wanka, a rude asabe da wasu mata yan uwa dake zazzaune filin sukayo kanta, asabe tace “ke lafiyarki kam badai kullin kosai din kika zubar mana ba kam? kinsan dai dashi za’ayi kumallo gadai mutane zazzaune ke ake jira, hannunta na rawa take nuna hanyar waje amma ta kasa magana,.. Da mugun tsawa asabe tace “wai bada ke nake magana ba, maryam tayi karfin halin cewa “wasu matasa ne su dayawa suka biyoni wai wai wai, asabe tace wai wai meye ? kimana bayani mana.

Ganin yadda take rude ne yasa karima kanwar asabe cewa “yaya kibita a hankali mana bakiga a rude take bane, habeeb dai sai kallon kanwar tashi yake, kamo hannun maryam karima tayi tace meya faru kimana bayani a nutse kinga ai kin tsere musu ko, to ba abunda zai faru, maryam tana gyada kai, tace “cewa sukayi wai sai inbisu muje muyi kwana daya a dakinsu don suma su zama cele, tunda gashi ya habeeb da matar da zai aura sun zama cele dare daya, shine na fara gudu suka ma suka dinga bina har daya ya kamoni shine na zuba musu kullun naci gaba da gudu, ta karisa maganar da pashewa da wani kuka. Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un mutanen filin suka ambata, wasu daga ciki suna tambayar yanzu ina matasan suke, maryam ta nuna hanyar waje, a sukwane habeeb yayi hanyar fita, da sauri asabe ta kamoshi tace zauna nan, so kake kaje su illata min kai ko me?, kanaji tace meka su dayawa ne, goshi ta dafe tana kallon mamman tace “kaji balain da ke shirin tunkaromu muna cikin zamanmu lafiya ko? don haka maganin kar ayi to kar a fara, tana kallon dannata tace habibu ina son ka janye batun auren yarinyar nan ko kuma in tsine maka albarka ka shiga duniya, ba habeeb kadai ba hatta sauran jama’an dake wurin saida kirjinsu ya girgiza da jin kalamun asabe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button