AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suheer ke nunawa lamido hanya bayan sun shigo anguwar a haka har suka iso kofar gidansu rasheed, parking mashing nashi yayi a gefe yana karewa tamfatsetsen get din gidan kallo, a ranshi yana cewa masu kudinmu suna hutawa, knocking karamar kofar yayi, mai gadi ne ya leko kanshi yana karw musu kallo, kallo daya ya gane suheer, domin ba’afi minti talatin ba da wani mai bawa fulawa ruwa yazo ya tsegunta mishi abunda ke trending a social media har ma ya nuna mishi video din, lamido da takaici yazo mishi har wuya ne yace zaka tsaya kallonta ne ki zaka yi aikinka,? da sauri mai gadin yace ” wa kuke nema,?

Lamido yace wadda ka gani a tare da ita a cikin videon, yake mai gadin yayi kana ya bude musu kofar suka shiga.

Duk inda suka bi a cikin gidan kallon Suheer ake, kama daga kan kananan ma’aikata har zuwa kan manya dake ta kai komo a tsakar gidan, saida suka iso bakin main building din kafun suka fara tunanin yaza’ai su samu ganin rasheed, wani dan saurayi suka gani yana ta aikin goge mota a bakin parking space, tunda suka tunkaroshi ya tsaida abunda yake ya sake baki yana kallon suheer zuwa can ya fidda wayarshi ya kalla kadan sannan ya mayar aljihu yana kara kallonta, cikin kufula da irin kallon da ake mata suheer ta matso kusa dashi tace ” ehh nidince ko zaka kara dubawa ne malam,? cikin in ina yace ” kiyi hakuri hajiya, suheer tace “taya zan samu ganin oganku,” dagowa saurayin yayi yana kallonta again, hararar da ta watsa mishi ne yasa shi saurin cewa saidai ku jira buba nanda minti kadan zai karaso na sani.

Waje suheer da lamido suka samu suka zauna karkashin wani artificial coconut tree. tsawon minti talatin suna wurin don har lamido ya fara tunanin shiga cikin gidan da kanshi, saiga buba ya shigo yana amsa waya, ganinsu a wurin yasa shi dan dakatawa, saida ya gama amsa wayan kana ya dubesu yana fara’a yace kai wa nake gani kamar suheer lamido barka da zuwa hajiya, sai kuma ya kalli lamido ya maida dubanshi kan suheer yace your dad i guess marabanku, kunsha ruwa ko wani drinks kuwa ya kuka zauna anan, tunma yaushe kuka zo? sai kuma ya juya kan ma’aikatan dake ta kai kawo a wurin yace ya kuka bar baki anan bari boss ya fito lallai zaku yi bayanine, lamido yace ba komai kar ka damu bamu dade da zuwa ba ai yana mika masa hannu sukayi musabaha, sannan yace muna son ganawa da boss nakane dama, buba yace ohh boss to bari a duba ko ya tashi dukda dai banjin ya tashi yanzunnan, ya fada yana nufar entrance na gidan,.

Buba baida shamaki da ko ina a gidan inka cire bangaren ummie, don haka direct ya haye saman rasheed, a bude ya samu kofar don haka yasa kai ya shiga, inda yake tunanin zai sameshi ya wuce wato gym room nashi aiko can ya taddashi yana ta gyming sai hada uban zufa yake, saida ya jira ya gama abunda yake tsawon minti ashirin kafun yasanarda shi yana da baki……Murmushin gefen baki rasheed yayi kana yace i though as much, jeka sa a shirya min breakfast a tebur na kasa sannan ka musu iso.

Lokacinda suka shigo cikin hadadden palon ba kowa sai tashin kamshi yakeyi ga dining table shake da breakfast kala kala, wuri buba ya nuna musu suka zauna yana kokarin haurawa saiga rasheed cikin takun kasaita yana saukowa har ya shigo cikin palon kana ya wuce yaja kujera daya ya zauna yana kallon buba yace bisimillah, buba ya cewa lamido ku iso nan. kujera ya jamusu amma sai lamido yace a a mun gode domin sauri muke yi munzo nan ne domin kabamu koda minti biyu, tsayawa rasheed yayi daga kokarin bude kulan da yake yace ina jinka abba, Amma da kunci wani abu, wnn shine zuwanku gidana na farko bai kamata kuyi minti biyu ba, ya fada yana yafawa fuskarshi murmushin dole, lamido yace ” sauri muke yi ne shiyasa”, yace ok, ya kalli suheer yace dinner dinki na jiya yayi kyau sosai nasan ma abunda ya kawoku, dam dam zuciyar lamido da suheer ya buga a tare, lamido yayi saurin cewa kamar yaya kasan abunda ya kawi mu?, rasheed yayi dariya yace ” nasan kun kawo min katin gaiyatar daurin aure ne, wani ajiyar zuciya lamido yayi kana yace eh kusan hakane amma da alama baka duba social media ko?” rasheed yana cigaba da dariya yace “as super star matukar kana yawaita shiga shafukan sada zumunta tabbas zaka samu hawan jini, shiyasa sai once in a while nake dubawa, wayarta suheer ta daddana kana ta ajiye a gaban rasheed tace watch dis.

Tashin hankaline karara fuskar rasheed bayan ya gama kallon videon ya mike cikin masifa yace what rub ish! ,”they’re cross limit dis time, they’re very keen on critisizing others, sun saba rubuce rubucen rubbish things a kaina, but wnn karon sun ketara iyakarsu, wait and watch how i sue them abba, karku damu, bazan barau ba har sai sun zo sun tsugunna sunne mi yafiyar mu kafun, zaku gani kuma, karka damu abba nasan a matsayin mahaifi, bazaka so abunda zai taba reputation na yarka ba, ga maganar aurenta a gefe, kabani nanda awa biyu zanyi kokarin ganin komai ya daidaita,mika mishi hannu lamido yayi sukayi musabaha kana ya juya yace da suheer su tafi, a hankali ta mika zara zaran hannunta da suka sha lalle amare ta dauki wayanta dake gabanshi, ta motsa labbanta tace “mungode” ciki ciki,

Wani dariya yayi yace karkiyi saurin godiya baby girl. ki bari sai nan da awa biyu,and duk abunda ya faru…..

????????????AUREN~FANSA????????????

BOOK TWO.

PAGE 49 / 50.

……… Da mamaki suke kallon asabe jin abunda ta fada, habeeb da kwakwalwarshi ta tsaya da aiki na wucin gadine ya taso da sauri bayan ya gama fahimtar abunda mamarshi take nufi, kafafunta ya kama a karon farko cikin shekaru hawaye masu zafi suka biyo kuncinshi, cikin murya mai tsananin rauni yace,

“Don girman Allah mama karki rabani da ita, wllh ina sonta! inkuka rabamu zan iya rasa raina, ki taimake ni mama.”

Ya juyo yana kallon sauran mutanen dake wurin yace, “baba kayi wani abu akai suheer itace rayuwa ta, ku taimaka karku rabamu, wllh Allah ina kaunarta,.

Da mugun mamaki asabe take kallonshi baki a sake, tace tana kallon mamman “kaga jaraba ko? ni nasan basu bar min yaro haka banza ba,du du du yaushe suka hadu dazai na ikirarin mutuwa zaiyi idan suka rabu,? to kuwa saidai ka mutu din, amma matukar ni na haifeka to ban amince yau a daura aure da wnn yarinyar ba.

Mamman yace “asabe abun bai kai har haka ba, hukuncin da kika yanke yayi tsauri dayawa, mukara duba lamarinnan, ko wanne bangare zaiyi asara faa, karki manta hatta jere anriga da anyiwa yarannan, ni inaga adan daga dai musamu muyi bincike zaifi.”

Asabe tsalle tayi ta dire tace saidai habeeb ya zaba ko ita ko suheer ta juya ta tafi abunta, da bayan hannu habeeb ya matse idanunshi wadda suka kara rine wa jijiyoyin kanshi sai tashi sukeyi, yana layi kamar wadda ya shawu ya wuce kofar gida. Bayan minti talatin asabe ta fito cikin shirin fita anguwa, tana kallon yan biki tace “wazai biyoni mu amso lefen da dana ya kai can gidan?, take kulu ta tashi tana muzurai, wata addar mamman tace “asabe kibi duniya a sannu kar ki bata goben danki kwallin kwal da kike dashi akan banzan tunaninki bar ganin yana miki biyayya, wllh kiji tsoron ranar da reshe zai juye da mujiya.

Ko kallon inda take asabe batayi ba tasa kai ta fice kulu na mara mata baya,…..Tijara sosai suka zuba a gidan su suheer gaba daya abubuwa sun dagule, domin sun sami hajiya saratu da bata daukar raini ga kuma anty hafsa, baram baram sukayi, ammi dai banda kuka ba abunda take yi don ta ma rasa tunanin da zatayi, yanzu da da wnn yarta zata zauna a matsayin surkuwa? ta rasa farin ciki zatayi da Allah ya nuna mata hakan tunda wuri ko kuma bakin cikin fasa auren yarta sanyin idaniyarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button