AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Anty hafsa ta watso akwati na karshe tana kallonsu tace “to abi wani sarkin kuma, badai wannan ba, mun godewa Allah da bai nuna mana tarwatsewan rayuwar yarmu ba, domin tabbas hada zuriya daku lalacewa ne,” Ku kwashe kayanku kubar mana gida kafun in rasa control nawa” cewar hajiya saratu.wani irin guda kulu tayi tace “ahayye lallai lalacewa yakai na yarku, waya san ma iya adadin cikin da ta zubar na saurayinnata, inba ya gama lalata ta ba meya hana ya aure ta,? wani kukan kura anty hafsa tayi ta cakumi wuyar kulu, da kyar sauran jama’ar dake wurin suka kwace ta. sosai wurin ya hargitse da hayaniya.

Da sauri fareeda ta dau wayarta ta danna kiran wayar lamido domin sanar da shi halin da’ake ciki kozai zo ya dakatar da abun. Ita ta manta ma da inda suka tafi tsabar rudewa.

Tunda suka fito gidansu rasheed ba mai cewa komai, machine din suka hau sukabar anguwar, banda juyawa babu abunda kan lamido keyi, a ranshi yake ayyana dole idan sun koma gida ya sha maganin hawan jininshi domin duk yadda akayi jininshi ya haura,kamar daga sama yaji wayar shi tana tsuwwa, zaro wayar yayi daga aljihunshi da niyar katse kiran, saidai ganin fareeda ke kira yasa shi amsa wayar, kafun yace wani abu muryar ta mai dauke da sautin kuka ya doki kunnenshi “kawu kana ina gashi sunzo daukan kayan lefensu wai sun fasa auren, gashinan sai hayaniya suke mana kazo da wuri kawu.

Calmly lamido yace “me kika ce fareeda? su waye suka fasa auren? auren wa aka fasa?” fareeda tace “mamar habeeb ce tazo wai abasu lefen dansu kuma sun fasa auren gashi sai tara mana mutane sukeyi kazo da wuri kawu.

Wani irin kara lamido yaji kamar karafuna sun hadu sai kuma wani ihu mai karfi kamar da muryar suheer, daga nan komai ya tsaya cikkk bai kara sanin abunda ya faru ba.

Tsawon kwana uku da yin accident din amma lamido bai farfado ba dan ba karamin buguwa yayi ba, don da kyar aka zakulo shi a kasan motar da tabi takan machine din nashi, gwara ma suheer Allah ya takaita mata wahala lokacin da motar tabi ta kansu ita tsalle tayi ta fadi gefen kwalta.

Zaune suke su biyu gaban teburin likitan daka gansu kasan ba karamin galabaita suka yi ba a cikin kwana ukunnan, likitan ya daga kai ya kallesu bayan ya gama duba takardan da suka kawo mishi na hoton da akaiwa lamido, tattaro courage nashi yayi yana gyara zaman gilashin idanunshi yace ” Hajiya majinyacinmu yana bukatan aiki na gaggawa, and iam sorry to say bazamu iya masa wnn aikin anan ba dole sai anfita dashi zuwa INDIA, sannan muna bukatan naira miliyan 40 domin aikin, kana abune na gaggawa, cikin kasa da kwana goma ya kamata a fita dashi idan ba haka ba komai na iya faruwa dashi.” Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, shine abunda ammi da anty hafsa ke ta nanatawa, kana suka hada baki wurin fadin likita miliyan arba’in? likitan yace kwarai kuwa ranku shi dade a hakan ma na kiyasta ne kawai, kuma ina tabbatar muku cewa yana bukatan aikinnan da gaggawa cikin kasa da kwanaki goma.

Jiki a salube suka fito nazari suka fara na hanyar da zasu bi su samu miliyan arba’in, duk wani lissafin su ya kwance, iya nazari da hangensu basu samo mafita ba dan haka suka yanke shawaran saida duk wani kaddara da suka mallaka ,…… duk wani kadarorin su sun hada sun siyar da kayan auren suheer gaba daya da ajiyan da suke dashi a banki da duk wani abunda suka mallaka amma miliyan tara suka hada, wasu abokan lamido ne sukayi karo karo a tsakaninsu suka hada dubu dari takwas suka kawo nan kudi ya doshi miliyan goma, gashi lokaci sai tafiya yakeyi, an doshi kwana na biyar saura kwana biyar. Sosai iyalan ke cikin tashin hankali domin lamido shine bangonsu shine kuma rumfar su.

Rasheed na zaune cikin kantinshi na saida gwala gwalai, yau kuma haka ya tashi da kewar mahaifinshi hakan yasa ya kawo ziyara kantinnasu, duk inda ka wurga idonka gwala gwalai ne tsala tsala keta walkiya, sai binsu yake da ido yana tuna rayuwar shi na baya,… wayarshi ne yayi kara, ya daga ya duba mai kiran kana yasa a kunne, buba ne yace cikin ladabi “boss akwai labari fa akan mutuniyarka “……… Rasheed yace uhummm” yana gyara kwanciyar kanshi akan office chair din, wacece mutuniyata kuma……..kap buba ya zayyanewa boss din nashi halin da gidan su suheer ke ciki.

Dan jimmm rasheed yayi sannan zuwa can yayi dan dariya yace 40millions?, woww i like it…. magana yaci gaba da yiwa buba wadda nidai banji me yace ba, tsawan minti biyu yana magana kafun buba yace “as you wish boss”. katse wayar yayi kana ya gyara zama yana lissafi, shafa lallausan gashin kanshi yayi zuwa beard nashi yana wani devilish smile.

Yau kwana shida kenan asabe batasa habeeb a idonta ba, kuma dai tasan wannan ba dabi’arsa bane duk inda zaije sai ya sanar da ita, koda kuwa bata nan idan ya tafi sai ya kirata a waya,….Abun duniya duk ya isheta, kallon mamman tayi dake zaune gefenta yana jan carbi, tace “nikam ka kula da yau kwana shida kenan habibu baizo gidannan ba, kuma wayarshi bata shiga, anya ba wani abunne ya same shiba kuwa kuma duk inda ya dace induba na duba ban ganshi ba. malam mamman yace “asabe ashe kin damu da rayuwar habibu ne?, tace “kamar ya, karka dawor mana da abunda ya wuce dan Allah ai duk abunda na aikata na aikata ne saboda na damu da rayuwar shi,” malam mamman yace “to ai shikenan sai ki jirayi dawowar shi, yaja bakinshi tsut yaci gaba da salatin da yake yi, wani tunani me ya fadowa asabe, gidan da habeeb ya kama haya har akayiwa suheer jere a can, tabbas bata duba canba, hijabinta ta rarumo tayi waje, girgiza kai kawai mamman yayi a ranshi yace “kadanma kika fara gani ai.” kasancewar gidan ba nisa baifi layi biyi ba a tsakaninsu da kafa asabe ta iso tura kofar durom din gidan tayi cikin sa’a ta sameshi a bude, ba komai gidan sai tashin kamshin sabon penti ya keyi, da shike sabon gini ne akayi habeeb ya kama haya dakine da falo sai kitchen da bayi da dan madaidaicin tsakar gida, kama handle din palon tayi shima ta murda, cikin sa’a kuwa ya bude, zaro idanu tayi kamar zasu fado kasa lokacinda tayi arba da habeeb kwance tsakiyar palon wanwar, tun kayan da yasa ranar daurin aurene jikinshi ga kwalaben maganin tari na ruwa a zube gabanshi a kalla sun doshi goma sha biyar duk babu ko digo a ciki, ga kuma wasu kwayoyi suma tablets an babbala ansha, ga habeeb zube a gefe ba alamun yana tare da mutanen duniya, kamar wacce aka janyo kawai sai gata tsakiyar palon durkusawa tayi ta dago kanshi tama rasa me zata yi guda daya, duk ta rude ta firgice…

Anty hafsa na tsaye cikin kitchen ta gama hada abinci a kwando, duk ta rame ta zabge gaba daya tsabar tunanin halinda yayanta yake ciki, kwala kiran sunan fareeda tayi kusan sau uku, a hankali suheer ta tashi ta fito zuwa kitchen din tace “anty sweetheart tasha magani ta samu bacci ya dauketa” hafsa tace magani kuma bata da lafiya ne? suheer tace “kamar kullum dai anty kinsan in wata ya kama irin wuyar da ta kesha ai” shafa goshi tayi tace ” ya salam to Allah ya bata lafiya, daman abinci na keso ta kaiwa ammi a asibiti kafun inzo, dan akwai wani wurin danaji suna bada taimako wa marasa lafiya idan yayi tsanani shine nakeso inje ingwada sa’ata ko zamu dace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button