AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sunkuyar da kai suheer tayi hawaye har ya fara sintiri saman fuskarta, kullum da wannan tunani take kwana take tashi, ta rasa ta ina zasu fara hada miliyan arba’in, a hankali tace “to anty basai ni inkaiba tunda na warke ai” da sauri hafsa tace “barshi kawai ni nakai sai inwuce daga can”bai kamata ki fita ba bacin ba lafiya ya isheki ba,kai suheer ta girgiza tace “Allah anty na warke ba inda ke min ciwo,beside ya kamata indan motsa jiki na kuma induba kawu da jiki, da kyar tayi convincing anty hafsa ta bata abincin, gyalen abayar dake jikinta ta yafa tasa wani silipas mai taushi ta fito dauke da kwandon abincin, tana tafiya kamar iska zai dauketa ga wani fayau din da fuskarta tayi, a haka ta samu taxi zuwa asibitin, a can ma bata dade ba domin ammi korota tayi ganin tana neman tara mata jama’a da kuka tun bayan da taga halin da lamido ke ciki, fitowa tayi tana share hawayen da suka ki tsaya mata, kamar daga sama taji tsayuwar mota kafun ta ankara taji an bude motar an jefata ciki, tana kokarin yin ihu ne wani daga cikin motar ya jefa mata wani farin hankici,daga nan bata kara sanin inda kanta yake ba…..
Ayi maleji ba yawa.
????????????AUREN~FANSA????????????
NA
UMMU FADEELA
Typing????
Book Two
Page 51 / 52
DAN TSOKACI: Yakamata duk lokacinda zamuyi rubutu, muke hada real life, da kuma reel life din domin samun labari mai ma’ana wadda mutane zasu amfana da darussan dake ciki ba wai iya shirmen soyayya ba………Na rubuta habeeb yasha kayan maye ne because of kaso mai yawa daga cikin matasan da suka fada harkan shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma karuwanci ta bangaren mata, ya samo asali ne ta dalilin hana su auren wadanda suke so ba tare da wani concrete dalili ba kamar dai habeeb ga misali….
Tunda suka jefa mata hankici din bata kara sanin inda kanta yake ba, gudu suka ringa shararawa akan kwalta har suka iso inda aka musu izinin su kaita, horn suka danna mai gadi ya taso ya wangale musu kofar, danna hancin motar sukayi cikin harabar gidan suka samu wuri suka tsaya, na gaban motar ne ya daga wayarshi ya kira wani lamba ya kara a kunnenshi, ringing uku aka daga wayar cikin murya mai amon sauti yace “yallabai mun iso fa, saidai yarinyar tana cikin halin bacci domin taso yi mana gardama hakan yasa muka sumar da ita na wucin gadi, yanzu mu dagota zuwa cikine ko yaya zamuyi”.
Daga daya bangaren akace “a’a karku tabata ku bani minti biyu ganinan zuwa” kiit ya kashe wayar ya dubi wanda ke zaune gefenshi ya daura kafa daya kan daya hannunshi rike da mujalla yana dubawa, cikin yin kasa da murya buba yace “boss sun iso fa, saidai wai sun sata bacci tambaya suke ko su dagota zuwa ciki”.
Tsawan minti biyu rasheed baice komai ba yana ta karanta mujallar dake hannunshi, har buba ya fitar da rai zaiyi magana kawai yaga ya mike yana yamutsa fuska yace a takaice “muje”.
Da mamaki buba ke kallonshi saidai baice komai ba yabi bayan rasheed da har ya nufi kofa, a farfajiyar quest house dinshi suka iske motar kirar peugeout baka wuluk mai bakin gilashi, da sauri mutane ukun dake cikin motar suka fito biyu daga gaba, daya kuma a baya, na bayanne ya bude bangaren da suheer ke ciki, tana zaune dabas kanta kwance jikin kujerar idanunta rufe rufff sai kirjinta dake aikin luguden bugu kaida kagani kasan a tsorace take baccin da ba shiri ya dauke ta.
Rankwafowa mutumin yayi da niyyar daukarta, amma rasheed ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, dan haka yaja gefe ya tsaya, rasheed ya zuba wa fuskarta ido gaba daya ya kode tsabar kukanda takesha a yan kwanakinnan fuskar tayi fayau da ita kamar jijiyar jini bata kawo sakon jini ta bangaren fuskar.
Gyara hannun shirt nashi yayi kana ya sunkuya ya sunkuceta yadda ya tsammaci nauyinta sam ba haka ya samu ba, ji yayi kamar ya dauki yar tsana na wasan yara, ko kadan bata da nauyi, juyawa yayi ya fara tafiya yana murtuke fuska irin bayason wargi dinnan, tafiya yake kamar an masa tilas ya dauke ta, ga wani uban kamshin dake tashi a jikinta wanda yake barazana ga nutsuwarsa, a tare buba da wadanda suka sato suheer suka zaro ido, da dan sauri sauri buba ya sallame su da damin kudi yabi bayan boss nashi sukuma suka samawa motar wurin zama suka fita a kafa, dama motar ta rasheed ce.
A kan doguwar kujerar dake palon ya shimfideta kana ya koma inda ya taso ya zauna ya harde kafa da hannu yana kare mata kallo na dan lokaci, zuwa can yaja karamin tsaki ya maida dubanshi kan mujallar da yake karantawa……… Tsawon minti talatin tana kwance a wurin kafun ta fara motsa hannunta a hankali, ta gefen ido rasheed ke kallonta,… cikin mawuyacin hali ta fara kokarin bude idanunta wanda taji kamar dutsen dala aka daura mata a kansu tsabar nauyin da suka mata, ware su tayi akan P.O.P dake saman dakin amma ta kasa gane menene domin dishi dishi take gani, mikewa zaune tayi niyyan yi amma ji tayi jikinta kamar bishiyar da ta riga ta kafa jijiya a cikin kasa, dan saisaita jikinta tayi kana ta mike a hankali, dafe gefen kanta da ya wani irin sara mata tayi tana furta “Hasbunallahu wani’imal wakeel”.
Duk abunda take yi rasheed na kallonta ta gefen ido saidai ko tari baiyi ba, balle ta san ran akwai wani bil adama a wurin,……..A hankali ganinta ya fara dawowa daidai, idanunta suka fara washewa,sarawan da kanta yake yi ya fara raguwa, juyawa tayi ta sauke idonta akan shi ya harde kafa,, duk da jaridar da ya rufe mishi fuska hakan bai hanata ganeshi ba.
A mugun fusace ta mike tana kare mishi kallo tace “so kai ka sa a sato ni knn, me kake bukata a gareni kuma?, idan dutse yana magana to rasheed ya tanka, haka ta kare surutan ta ko qala baice ba, a fusace ta nufi kofar da niyyar fita saidai duk yadda tayi kokarin bude kofar hakan ya faskara, ga wani irin jiri da take ji yana dibarta, dafe kai tayi ta juyo tana kallonshi, hada ido sukayi ya mike yana tunkarota,duk takunshi daya sai kirjin suheer ya girgiza domin wani irin kwarjini mara dalili ya mata yau din, matsota yake yi tana matsawa har ta dangana da jikin bango ta makale, hannayenshi biyu yasa ya tokare bangon dashi yana kallonta sama da kasa yace “eheennn ki cigaba da abunda kike fada” shiru tayi, bawai dan bata da abun fada dinba sai don irin kusancin da suka samu yayi yawa, tsaki yaja ya koma gefe yace “ki rage taurin kai baby girl, samu wuri ki zauna magana zamuyi ki kama gabanki, domin nima kin isheni a wurinnan.
Harara suheer ta banka mishi kana ta koma ta zauna a kujera domin ita kanta tasan tacigaba da tsayuwa wurin zata iya faduwa. Zama shima yayi yana kallonta with seriousness yace.
“A lokacin da na samu labarin cewa your marriage has been cancelled. kana kun rasa komai naku, all your family fall apart. daga lokacin nace zaren takun sakar mu ya zo karshe, a lokacin na fara tunanin sauke labulen labarinmu, a lokacin nace rasheed zai huta da tunaninki domin burinshi ya cika, kyawawan idanunta ta zuba mishi, ta rasa gane inda maganganunshi suka dosa.
Yayi dan murmushi yace ba lallai ki fahimce ni ba dama, ban tashi gane nayi kuskure ba saida naga irin barnar da bidiyon da aka saki ya jawo min, shiyasa na kiraki muyi musaya inbaki gishiri ki bani manda, ya fada gami da hade hannayenshi wuri daya ya sa a saitin bakinshi yana jiran jin abunda zata fada.