AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shafa bayanta fareeda keyi a hankali alamar rarrashi, zuwa can tana sauke ajiyar zuciya tace, “Rabin jiki ! a tunaninki suwaye mu da Allah bazai jarrabcemu ba,? Allah yana jarrabtar bayinsa ta hanya mabambanta domin ya gwada karfin imaninsu, ubangiji ya jarrabci annabawa da kuma salihan bayi, suwaye mu? ba shakka munga abubuwa da dama a dan tsakanin nan, amma karki manta ubangijinmu ya na sane damu kuma ubangijinmu mai jin kan bayinsa ne, rabaki da habeeb da akayi its part of your destiny, ba rabaku akayi ba kaddararki ce taxo a haka rabin jiki, ki fauwalawa Allah komai and believe in him na tabbata zai miki sauyi mafi alheri a rayuwarki, don’t forgot that Allah’s plan is the best.

Sosai maganganun fareeda sukayi tasiri a kanta don har ta rage karfin kukanta tana kwance lamo jikin fareeda sai ajiyar zuciya take saukewa, shafa bayanta fareeda taci gaba dayi a hankali,…. Bude kofar palon akayi anty hafsa ta shigo tana jan kafa duk binta sukayi da kallo, fuskarta cike da tashin hankali, nan tsakar palon ta yarda mayafinta ta zauna saman kujerar tana lumshe ido, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata,…..Kaiconta da wannan yanayi, yau ga dan uwanta daya tilo abun kaunarta kwance gadon asibiti rai a hannun Allah amma batada yadda zata taimaka mishi, wannan shine babban tashin hankalinta, taje inda aka sanar da ita ana bawa marasa lafiya taimako, amma abunda ta samo bai taka kara ya karya ba, miliyan arba’in ba wasa ba a wannan zamani damuke ciki da kowa ke ta kansa.

( masu kudinmmu kuma kansu kawai suka sani da yayansu, nayi imanin cewa akwai wadanda inda zasu cire miliyan arba’in cikin dukiyar su kamar kasa allura ne a ruwa cikin kofi, ba abunda zai ragu a tarin arzikinsu, amma kashh bazasu iya taimakon talaka mara galihu ba.)

Gefen hannunta tasa ta share hawayen dake shatata a fuskarta, tasowa yan matan sukayi suka sata a tsakiya duk dinsu sunsan damuwarta suma cikin wannan yanayi suke, hadasu tayi duka ta rungume tana kokarin ganin ta tsaida hawayenta domin ta karfafa musu guiwa, and Suheer heart melt, ya kamata tayi wani abu akan lamarinnan amma kuma…….Bude kofar da aka kumayi ne ya tsayar mata tunanin da takeyi, ammi ne ta shigo tayi wujiga wujiga, da ka ganta kasan bata a hayyacinta, kamar dai ba adaman nan kyakyawar balarabiya ba har wani tsufa ne na musamman ya bayyana a fuskarta, cikin tashin hankali duk suka mike domin fuskarya ya nuna musu tsananin tashin hankalin da take ciki, a zabure anty hafsa tayo kanta tana kallonta tace “Adama me ya faru, ina yaya? da wa kika barshi,?… wasu hawaye ne da adama take ta kokarin rikewa suka fi karfin ramin idonta suka sulalo saman fuskarta, bakinta ya fara rawa tana sonyin magana amma ta kasa, dishi dishi hafsa ta fara gani sai kuma ta tunaninta ya fara daukewa a hankali ta furta yayaaa meyasa ka tafi ka barmu,? diffff tunaninta ya tsaya duhu ya mamaye ganinta ta zube a kasa summamiya, durkushewa ammi tayi gabanta tana kiran sunanta cikin tashin hankali, da gudu fareeda ta nufi fridge ta manta da cramps dake damunta ta dauko ruwa da sauri ta nufi anty, and this time suheer heart breaks into thousand’s pieces.

Wani irin ajiyar zuciya anty hafsa ta sauke bayan saukar ruwan sanyi a jikinta, ta bude ido tana binsu da kallo, cikin minti daya ta tuna abunda ya faru ta yunkura ta mike tana cewa “shikenan yaya ya tafi ya barmu, wayyo Allah kaine gatanmu,yi take kamar kwanyarta ta samu matsala, rufe mata baki ammi tayi a hankali tace “hafsa yaya lamido bai mutu ba,! amma yana cikin tsananin bukatar taimakon mu hafsa, na rasa ya zanyi, bansan meye mafita ba, hafsa zuciyata ta kasa jure ganin mutumin da ya zame min gata biyu a duniya kwance cikin halin da yake ciki,….. Dazu likita yake sanar min cewa lallai ana bukatar nan da kwana hudu a mishi aiki inba haka ba tabbas zamu rasa shi, ya tabbatar min da akwai internal injury da ya samu sannan jini yana sauka a kai kadan kadan bansan ya zanyi ba hafsa shiyasa na dawo dan mukara wani tunanin, wani boyayyen numfashi fareeda da suheer suka sauke a tare, hafsa kuwa kallon ammi take yi baki a sake tace “Adama kina nufin yayaa yana raye,? saikuma ta daga hannu sama tace “Alhmdllh Allah na gode maka”.

Nan ta bawa ammi labarin taimakon da taje nema amma ba’a dace ba, ammi tace “last option da muke dashi shine na saida gidannan koda ace kudin bazai isa ba, sai muje mu kara rokar likitan watakila akwai wani hanyar daza mu kuma bi, ammi ta karishe tana cewa kinga sai mu nemi gidan haya koda daki biyu ne kamar dai yadda muke da can baya kafun Allah ya horw mana mu siyi wnn.” Aiko take anty hafsa tayi na’am da shawarar, a gareta rayuwar dan uwanta yafi mata komai.

Cikin sanyi murya suheer tace “ammi, anty, akwai abunda zan fada,” duk zuba mata ido sukayi, duk jikin ammi yayi sanyi ganin yadda yar tata ta sake gaba daya inda ta kama cikin sati daya kacal,amma damuwar da suke ciki bai bari taja ta a jiki ta bata kulawa irin yadda ya kamata ba, tasan duk cikin su zuciyar suheer yafi na kowa kuntata, domin ita zafi biyu ne hade kanta.

Cikin nutsuwa ta fara basu labarin yadda sukayi da rasheed daga farko har karshe ba tare da ta yadda ta hada ido da kowa cikin su ba, cikin taka tsantsan ta basu labarin…….Ta karishe da cewa “nayi kokarin ganin cewa nayi convincing nashi suyi yarjejeniyar da sweetheart tunda ai itace ke sonshi tun jimawa kowa ya sani, amma he insist cewa dani aka mishi batanci bada ita ba, si dole dani zai gyara abunda aka bata na sunanshi,” wani irin kabbara hafsa tayi tana washe hakora tace “Allah mai yadda yaso, yanzu ke tunda zu kina rike da wnn kyakyawar albishir din amma kika yi gum da bakinki lokaci yana ta kurewa?…….Ammi ma da farin cikinta yaki boyuwa tace “Alhmdllh,amma naji dadin maganar nan,”hafsa tayi caraf tace “Adama bana fada miki ba, bawan Allahnnan makiya ne suka nemi tozartashi a idon duniya sai Allah yasa hakan ya fado takan yarmu gashi ta dalilin hakan zai ceto rayuwar dan uwanmu, Allah mai yadda yaso a lokacin da yaso, ammi tace “sosai kuwa” gabadaya farin cikinsu ya kasa boyuwa, zuwa can ammi tace “amma wani hanzari ba gudu ba,

Sai kuma ta juyo tana kallon fareeda dake kallonsu kamar wata sakarai fuskar ta ba wani emotion balle ka fahimci halin da take ciki, ita dai tasan an ambaci rasheed an kuma ambaci suheer sannan taji kalmar aure da kuma kudin jinyar kawu lamido, bata sani ba iya abunda aka fada kenan kodai iya abunda taji ne kawai. ammi tace tana kallon hafsa “ya kamata muji ta bakin fareeda kuma domin duk munsan abunda yar uwar ta fada gaskiy…” Kafun ta kai aya hafsa ta katse ta da fadin “nashiga uku adama wani irin aji ta bakin fareeda kuma? bayan ga magana baro baro a fili, gaskiya dai kibar wnn maganar muyi abunda ya dace, wama yace muku fareeda son rasheed take yi,? inace duk munsan so take ta fito cikin fim tare dashi, to wnn ba zancen fim bane maganar reality akeyi.

Ammi tace “duk da haka dai,” ta juyo tana kallon fareeda tace “mamana kinji abunda muke tattaunawa akai, kin amince yar uwarki ta auri rasheed domin ceto ran kawunku? “.

Jin maganar tayi salam a ranta kamar ruwan randa, bataji komai ba na bakin ciki ko kuma farin ciki, a hankali tace “anything for kawu lamido ammi, zan iya bada komai akan shi matukar na mallake shi balle kuma abunda ban mallaka ba.” zaro ido sukayi gaba dayansu dan ba karamin mamaki ta basu ba, basu tsammaci jin haka daga gareta ba, ganin irin kai ruwa rana da akayi da ita a kwanna baya, amma sai suka alakanta hakan da yanayin da suke ciki, shafa kanta ammi tayi tace Allah ya muku albarka baki dayanku, kamar yadda kuka samu farin ciki Allah yabaku yaya masu jin kanku kuma. Ameen fareeda tace ta mike ta wuce daki ta hau gado ta kwanta, lumshe ido tayi. Anty hafsa ma ta mike kamar zata zuba ruwa a kasa tasha dan farin ciki tace tana kallon suheer “Allah ya muku albarka, ta wuce dakinta fuskarta ya gaza boye how happy she is.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button