AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ammi tana kallon suheer da gaba daya fuskarta yake so moody, tace “dota bakya farin ciki ko? nasan kina cikin tsanani kwanannan amma ina son ki san cewa when everything seems to be lose always have hope have faith that Allah plans something special for you kinji, bazaki taba nadaman wnn sadaukarwar dazakiyi ba, a hankali suheer tace “anything for kawu lamido ammi, zan iya bada dukkan abunda na mallaka domin ceton ranshi”, sai ammi taji maganar yayi mata kama da abunda fareeda ta fada, to me yaran suke nufi?, mikewa tayi itama ta nufi dakin su kwance ta tarar da ita idonta lumshe, zama ammi tayi a bakin gadon tana shafa fuskarta zuwa kan lallausan gashinta tace “Insha Allah nasan bazakiyi nadamar sadaukarwar da kika yi ba fareeda, sakamakon ku duk ku biyun yana ga Allah,……Nasiha sosai ammi ta mata,saidai abinda yadaurewa ammi kai shine ko digon hawaye babu a idon fareeda, saima wani dumin da jikinta ya dauka.
Da daddare suheer ta kwashe lambar dake jikin takardar da rasheed ya bata cikin wayarta, sako ta tura mishi kamar haka “Na amince da bukatar ka, ina fatan Allah ya bani hakuri da juriya da kuma sassauci akan mummunar nufinka”….. ta tura mishi, tana kwantar da kanta,ita dai tasan tabbas ba haka kawai rasheed ya bijiro da wnn batun ba akwai wani boyayyen abu a ranshi komadai menene tana fatan Allah yabata ikon jurewa har zuwa karshen abun tunda yace da zarar ya dawor da martabar sunanshi da aka bata zai sauwake mata.
Yana zaune yana dinner sakon ya shigo mishi, murmushin gefen baki yayi kana yace “good i like it, …..wellcome to the jungle Suheer lamidooo”, sai kuma da sauri yace “awwwwn Suheerr samaila ya fada yana karkata kai gefe……..”
????AUREN~FANSA????
By
Ummu Fadeela.
Typing????
Book Two
Page 55 / 56.
…. Wani aminin mahaifinshi na kut da kut rasheed ya samu da maganar yana son a tambayo mishi auren suheer, sosai Alaji kabiru yaji dadin maganar inda yace “karka damu nanda kwana biyu zan samu shi kanin mahaifinnaka sai muje mu tambayo maka, ina fatan ka sanar masa aiko?.and iam happy for u Abdul-rasheed, Allah yasa abokiyar zaman arziki ce.
Karkata kai gefe yayi cikin magana kasa kasa yana shafa sumar kanshi yace “ammm abba nace dole sai kunje da shi…….Yana kallonshi sosai yace “shi wa kennan” ya fada a takaice,duk da sarai ya fahimce shi amma sai ya basar.
Rasheed yace “shi na can gidan “, yana kare mashi kallo yace “rasheed yakamata kasawa zuciyar ka salama hakanan, kasan ka girmi abunda kake yi, shidin kanin ubanka ne kaga ko dole shi zai jagoranci nemar maka aure tunda yana raye, badon yaso ba yadaiyi shiru.
A bangaren su suheer kuwa, abokan lamido biyu dasuka karbi sadakinta da habeeb wnn karonma su aka sanar ma da batun neman auren, dan haka suka shirya tsap don jiran masu zuwa. Yayinda fareeda kuwa cikin kwana dayan kawai tayi wani irin zuru da ita bata cewa komai, hasalima tunda ta shiga daki jiya bata kara fitowa wai don a zauna da ita ba saidai inta bukaci canza pad, lokacin cin abincin dare ma cewa tayi ta koshi ba tare da tunanin komai ba suka alakanta hakan da yanayin da take ciki don in tana period bata cika cin abinci ba dama, haka har washe gari lokacin breakfast nanne fa hankalin ammi ya fara tashi, koda ta shiga dakin zaune ta same ta, tayi matashi da fuskar gadon idonta bude saidai ba abunda takeyi, tambayoyi ammi ta shiga jero mata kamar, meyake damunki mamana? akwai inda yake miki ciwo ne? ko wani abun akai miki? me kikeson ci in dafa miki? da ire iren su dai amma fareeda ko kala bata ce ba, sosai fuskar ammi ya nuna damuwar da take ciki, a hankali ta bude baki tace “ba komai fa ammina “.
Ajiyar zuciya ammi ta sauke tace “to don Allah ki dena zaman dakinnan da kika tsiro kina sani a kokonton ko baki amince da maganan da mukayi jiya bane”? girgiza kai tayi tace “a’a ammi na amince,” barin dakin ammi tayi ta fito zuwa palo zaune ta tadda suheer itama tayi tagumi alamun tayi nisa a tunanin da takeyi, inna lillahi ammi ta ambata, a ranta tasan wnn lamari babban barazana ne ga rayuwar yayanta, suheer, an fasa aurenta da masoyinta a ranar daurin auren kana yanzu wani zai maye gurbin wancan, wanin kuma abokin gabanta ga kuma rashin lafiyar kawunta, fareeda, auren suheer da rasheed na nufin katsewar cikar burinta ta ko wanne bangare wadda ta ginu akan son cimmawa tun tana yarinya ga kuma rashin lafiyar kawunta, anya sunyi wa yaran adalci kuwa? shin ba cutarwa a lamarinnan kuwa? da sauri wani bangare na zuciyar ta yace “to lamido kuma fa dake tsakanin rayuwa da mutuwa”? .
Karasowa tayi cikin karfin hali ta dafa suheer wacce ta dago kai tace “ku zama jajirtattu kamar mahaifiyar ku da iznin Allah babu abunda zai gagare ku, yanzu tashi kije ki samu yar uwarki nasan tana bukatanki kusa da ita, dago jajayen idanunta tayi tana kallon ammi tace “ammi da akwai abunda ke damun sweetheart dan jiya batayi bacci ba ko na sakwan daya, tambayan duniya kuma na mata ammi amma taki cewa komai,ammi tsoro nakeji kar na zama silar rushewar wani gini mai muhimmanci a rayuwar mu”, ta kare wasu hawaye masu dumi suna silalo mata, ammi tace “ba komai dukkanninku jarumai ne, kunyi sadaukarwa ne kan ceton rai, kuma ran da ya cancanci sadaukar warku……Anty hafsa ne ta shigo bakinnan har kunne sai fara’a take, ta zauna a kujerar da ammi ke zaune, ammi dai sai kallonta take, zuwa can tace “hafsa yaya lamido ya farfado ne?.
Fadada murmushinta tayi tace “adama bai farfado ba amma ya kusa yanzu ma nazo karbar passport naki ne wanda za’a miki fasfo da biza dashi insha Allah jibi zaku daga zuwa india ke da yayaa don sunce mutum daya ake bukata sai likitan da zaiyi jagora, baki a sake ammi ke kallonta kafun tace ban fahimce ki ba hafsa,? kimin dalla dalla.
Anty hafsa tana ta washe hakora tace “adama dazu yaron kirkinnan rasheed yaje asibiti sun tattauna da likitan kuma har anyi komai ya saki kudin har anyi sign na komai, daga can india ma an shirya komai marar lafiyan kawai ake jira, durkusawa kasa ammi tayi takai goshinta kasa tayi sujudul shukr tana godewa ubangijin talikai.
Hafsa ta cigaba da cewa” yanzu mun tsaida magana da likitan cewa dake za’a tafi, kuma shi rasheed din ya tabbatar da zai mana cuku cukun yadda zaki samu visa cikin kwana daga shiyasa nazo da wuri dan ki shirya kije a samu a miki komai akan lokaci.
Cikin farin cikinda yaki boyuwa ammi tace “baza’ayi haka ba hafsa, dake za’a tafi, ke kika fi cancanta da zuwa can, ni kuma zan kula mana da gida sannan bazan taba gajiya waba wurin mana addu’ar samun nasara……..Da kyar ammi ta lallaba anty hafsa ta yarda a tafi da’ita……..Koda alaji kabiru ya samu alaji umar da maganar zuwa nemarwa rasheed aure, ba karamin farin ciki yayi ba a zahiri dan shi dama irin wannan auren yakeso yaron yayi wato kaskantaccen aure, kullum fargabar shi irin matar da rasheed zai aura, kar ya auro wacce zata musu shamaki da dukiyar da sukayi shekaru masu yawa suna farautar samu, a ranshi yace “dan masu taurin ran tsiya, duk shi ya hanasu rawan gaban hantsi da yanzu ba wannan batun ake ba.
A ranar da dare suka kai tambaya da kudin aure.inda aka sa kwanaki uku kacal kamar yadda rasheed ya bukata, haka kuwa akayi waliyanta basu musa ba suka amshi kudin….Cikin kwana daya aka gamawa hafsa da lamido duk abunda ya dace na shirin tafiya……A kuma ranar ne suka je asibitin da dare domin yiwa lamido bankwana, fareeda dai binsu take yi kawai duk inda suka bi, idan ka ganta zaka rantse ba fareedar nan bace mai shegen surutu kamar wadda ta hadiye aku, har suka gama abjnda zasuyi asibitin fareeda bata ce ko uffan ba, zuwa lokacin abun ya fara damun iyayennata sosai. ….Washe gari laraba su hafsa suka lula kasar indiya, tafiya ce ta akalla awa tara da minti arba’in da biyar daga nigeria zuwa india a jirgi, tun hafsa na jin dadin tafiyar har ya fara gundurarta, lafiya suka iso inda suka tarar da ambulance na asibitin ALL INDIA MEDICAL SCIENCES NEW DELHI yana jiransu inda ananne dama sukayi booking suna isa kuwa ba bata lokaci aka wuce da lamido dakin taimakon gaggawa likitoci suka rufu akanshi aka fara aiki, da shike sun riga da sunsan matsalar an tura musu ta intanet, sai muce Allah yabada sa’an aiki kawu lamido….