AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kama hannunta yayi yanzu ma ya jata zuwa gabansu yace oya start counting…Ba yadda ta iya domin wani irin damka yayi wa hannunta kamar zai balla, sai sa,a ma inbai mata targade ba, a hankalu ta fara irgasu har tazo kan na tara kana ya sake ta a karshe yace goma,….Da ga yau kece cikon na goma kin zama ma ‘aikaciyar rasheed i mean daga this very moment yana kallon sauran yace dukkanku na baku hutu daga yau wnn ita ce zata maye gurbin duk aiyukan da kuke yi a gidannan. Da sauri ta dago idanunta ta kalleshi, yace “daina kallo na karki cuceni, kana ya kuma janta suka nufi stairs yace daga yanzu zaki fara aikin daya kawoki gidannan, har sun fara hawa benen bai daina janta ba suheer sai kokarin kwace kanta take amma ta gaza sabida karfin da ya samata ga wani irin gurzarta da kafar benen keyi, da gudu ummie wacce ta sankare awurin tana tunanin aiko karuwa ya kawo gidan bazai disgracing nata gaban maids irin haka ba balle matar sunnah,binsu, tayi ta iskesu yana kokarin janta, tsayar dashi tayi kana ta takarkare ta zabga mishi mari a fuska abunda bata tabayi ba tun yana karami ma balle yanzu, kafun ya fahimci abunda yake faruwa ta kuma dauke shi da wani wawan mari wanda saida ji da ganinshi ya dauke na wucin gadi, kafun ya dawo hayyacinshi ta kuma zuba mishi wani lafiyayyen mari wnn karon saida kanshi ya sauka kan karfen rails na benen, tana huci tace “are you mad? ko ka fara shaye shaye ne ban sani ba? how dare you? suheer dai tunda ta samu ya sake hannunta ta makale gefe jikinta sai rawa yake yi.
Dago kai rasheed yayi yana dafe goshin sa dake zubar jini domin ba karamin buguwa yayi ba, zuciyar shi na tafarfasa ya daga kai ya hango ma’aikatan dake kasa suna kallonsu ido a waje suna kallonshi suka sauke kai kasa cikin tsawa yace get lost take suka fara watsewa, kallo daya yayi wa ummie dake ci gaba da fada kamar zata rufe shi da duka, kana ya juya ya hango buba dake kallonshi shima amma suna hada ido ga sauke kai kasa, a ranshi yana tunanin yau dai boss bai tashi da sa’a ba da farko an kira shi driver gashi yanzu kuma an wulakanta shi a gaban mutanen da ya tara dan kaskantar da wata anya wnn yarinyar ba….Sai kuma yayi shiru,
Ko kala rasheed baice wa ummie dake ta faman tambayan shiba, ya nufi suheer dake makale gefe tana makyarkyata, gadan gadan ya nufe ta kamar wani zaki zuciyar shi tana tafasa……..
????AUREN~FANSA????
PAGE 59 / 60
……Nufota yayi gadan gadan kamar zai tashi sama, bai damu da ciwo da digar jinin da goshinsa yake ba domin ciwon da yake ji a zuciyar shi tafi wannan, ganin yana nufota ne yasa suheer yin gaba da sauri dan tabbas ya kuma mata irin rikon dazu to ba tantama hannunta zai balle,bare ma yadda ta ke hango bacin rai karara saman fuskarshi.
“Ban amince ka kuma tozar ta yarinyar nan ba” muryar ummie ta doki kunnenshi, cak ya tsaya yana hura hanci, sai kuma ya ci gaba da tafiya ita ma suheer tana kara tafiya da baya baya ba tare da tasan inda ta nufa ba haka shi kuma bai fasa binta ba, saida suka iso dan filin da ya raba tsakanin hawa na farko da kuma hawa na biyu ta tsaya dan bata san kuma ina zata shiga ba.
Hannunta ya kama cikin nashi saidai wannan karon bai mata rikon wahala ba kana bai jata ba suka ci gaba da tafiya har zuwa bangarenshi, a bakin kofar palonshi ya sake ta fuskar nan ba annuri yake kallonta itama batayi kasa a guiwa ba wurin kafe shi da kyawawan idanunta a ranta tana cewa “anya wannan zuciyar bil,adam ne a jikinshi kuwa?,
Buge gefen bakinta yayi da yatsanshi biyu yace “daina kallona karki cuce ni,” dafe bakin suheer tayi dan ba karamin zafi taji ba, saidai bata dauke idanunta daga kanshi ba, hannu ya daga zai kara buge bakinta tayi saurin matsawa baya matsota yayi ta kuma matsawa yana binta har saida ta jingina da jikin kofar yasa hannu biyu ya tokare kofar sai ya zama ya mata rumfa da jikinshi babu ta inda zata iya motsawa, turashi ta fara yi iya karfinta amma ko gezau baiyi ba har ta fara gajiya ta saki kukan da ke cinta tun dazu amma tana ta rikewa, fizgo ta yayi hakan yasa ta fada saman kirjinshi, fizge fizge ta fara domin son kwatar kanta saidai ta kasa, ga wani irin bugawa da zuciyar ta keyi,.. dago habarta yayi da yatsa daya yana karewa zara zaran lashes nata da suka jike sharkaf da hawaye kallo, cikin tamke fuska yace “ahaaan ki ci gaba mana wife, idan kika ce taurin kai zaki min iam telling you sai kin gwammaci mutuwar ki akan rayuwa, karki ga cewa anmin wannan akanki ya fada yana nuna goshinsa dake digar jini har yana taba hijab dinta, yace ” you will pay for it wife, sannan karki kuskura ki tsallake abubuwan da na fada miki a downstair daga safiyar gobe zaki fara aiyukan gidan nan gaba daya, sabawa hakan kuma hmmmm,.
Dan sassauta rikon da ya mata yayi hakan yasa ta zille zata fita yayi saurin riko hannunta daya yace “no wife karki yi saurin tafiya, I have a special gift for you” yasa hannu cikin aljihun shi ya zaro wani abu ya daga shi saitin fuskar ta, zaro ido tayi tana kare mishi kallo, siririn sarkar ta ne wanda ta taba bawa inspecta garba ya kawo wa rasheed tun lokacin da ya buge habeeb, saidai wannan an rage tsawon chain din, yana kallonta da kyau yace “nasan baki manta dashi ba sannan baki manta abunda kika fada a lokacin ba,,…..Tun lokacin nayi alkawarin sai kin sa wannan sarkar sau dubu amma na azaba, yana fadin haka ya janyo ta yana kokarin cire mata hijabi nan fa akeyinta domin suheer gaba daya karfin da Allah ya bata ta saka wurin rike hijab nata a ganinta matukar rasheed ya cire mata hijab to ya gama wulakanta ta.
Dan shafa beard nashi yayi yana mamakin ashe tana da karfi,….Duk yadda rasheed yaso cire hijab din abu ya gagara har saida ya sama ta karfinshi juyi da ya ya mata ya janye,ji yayi wani lallausan abu ma’abocin kamshi mai sa nutsuwa ya lullube masa fuska,..ashe ya hado da ribbom nata da ta tufke dogon lallausan gashin kanta dashi hakan yasa gashin watsuwa har saman fuskar shi. wani irin bakin ciki ne ya turnike zuciyar suheer lallai ya tabota inda bazata jure ba, juyowa tayi a fusace hakan ya kara bawa gashin nata daman sauka daga fuskanshi ya kwanta libb saman bayanta. gashin yabi da ido yana mamakin wato yarinyar har gashin doki take sawa,…Karaf ya riko hannun ta da ta daga da niyyar kai mishi mari kirjinta na ta tsallen bacin rai…Yana kallonta strictly yace” this is the greatest mistake da zaki aikata, kana ya watsar da hannun ya shako wuyanta yana zare ido yace “wato kinga hakora na awaje ko? ohk fine, kunce sarkar ya farayi cikin second biyu ya daura mata a wuya wanda sarkar ya mata wani irin shaka har numfashinta ya fara seizing, yana kallonta da kyau yace “wannan shine kazar amarcinki, so enjoy your first night wife. saketa yayi ya bude palon da sassarfa ya shige hadi da banko kofar, wani irin azaba suheer taji ya ziyar ci kwanyarta yayinda ya saka mata sarkar take idanunta suka fara juyawa zuwa jawur, hannu ta saka da niyyar kwance sarkar saidai duk iya kokarinta ta kasa sai wani irin rawa jikinta keyi durkusawa tayi a wurin ta janyo hijabinta duk da azaban da take ciki hakan bai hana ta sa hijab dinba ta dukunkune a wurin tana kiran sunan Allah.