AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummie tace “ka bude sai ka bincika waye”, dan dafe kai yayi sannan ya bude kofar ya dan matsa gefe ta shigo rike da hannun suheer ta tsaya a tsakiyar dakin tana karewa ko ina kallo, kana ta juyo ta kalli suheer tace “tafi ki hau gado ki kwanta,” a tare rasheed da suheer suka kwalalo idanuwa waje, tana kallonta da kyau ba wasa fuskar ta tace “tafi ki kwanta nace” simi simi kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta wuce zuwa kan gadon ta dan dosanu gefe amma ta kasa kwanciya, ummie tace “taurin kai zaki min ne? girgiza kai suheer tayi ba tare da tace ko uffan ba, tace “maza kwanta” a hankali ta zare dogayen kafofinta ta kwanta akan gadon tana kara dukunkunewa cikin hijab nata, matsowa tayi ta kama hijab din ta cire tana kallonta tace “feel free ke ba bakuwa bace nan gidan mijinki ne kuma dakin ki” kana ta ja lallausan duvet din ta rufa mata sannan ta nufi kofa ba tare da ta kalli inda rasheed ke sankame cike da mamki ba.
Har ta kama door knob sai kuma ta juyo tana kallonshi strictly tace “as far as iam the woman who gave birth to you, to ban amince yarinyar nan ta bar dakin nan ba,! ta wuce ta barshi a wurin har ta kuma shigowa rike da akwatin suheer rasheed na tsaye wurin kamar soja, bakin closet nashi ta kai kayan ta ajiye ta fita ta barsu, suheer dai na kwance lamo abunta sai yanzu take nadamar meyasa a yarjejeniyar tasu basu sa lokacin rabuwa ba, zuciyar ta yace mata daga kawu lamido ya warke ae shikenan by then shikuma mugun ya gyara sunanshi dayake ikirarin an bata.
Kwafa rasheed yayi ya nufi closet nashi da niyyar daukar wani bargo ya tafi other room, wani takaici ne ya turnike shi yayinda yayi karo da akwatin ta da ummie ta zube a wurin wani dogon tsaki yaja ya shige ya fito da bargon ya fita…..Saidai cikin dakuna hudun da ke bangaren babu inda rasheed zai iya kwanciya, hasalima ba wani kaya cikin dakunan ga wani uban kura da sukayi dole badon ya soba ya dawo palon ya hau saman doguwar kujera ya kwanta saidai duk inda ya juya ba dadi don tsawonshi yafi kujerar, tsaki kuwa rasheed yaja shi yafi cikin carbi yana cewa mutum da dakinshi da gadon shi ya kare da kwana a palo saboda….Sai kuma yayi shiru a haka dai barci barawo ya sace shi cikin yanayi mara dadi. Suheer ma juye juye ta ringa yi a dakin ga wani tsoro da ya mamaye ta dan bata saba kwanciya daki ita daya ba da kyar dai bacci barawo ya saceta cike da mafarkai kala kala….Sai muce asuba ta gari rasheedsuheer.
Misalin karfe hudu na asuba suheer ta farka kwata kwata bata wani ji dadin baccin ba, yaye duvet din tayi ta zuro dagayen kafofinta kasa ta mike ta nufi kofar da take kyautata zaton bayi ne a hankali ta bude tadan leka kanta waro ido tayi ganin irin haduwar da bandakin yayi, karewa masa kallo take yi bayan da ta shiga tana cewa kamar dai baza a mutu ba, gaban sink taje tana karewa fuskar ta kallo ta cikin mirrorn dake sama sink din wasu set na tooth brush ta gani jere a cikin ma’ajiyarsu na glass a rufe ruf babu ta inda kwayar bacteriya zai shiga tuno da nata brush tooth paste din tayi da sauri ta juya dan ta dauko cikin akwatin ta,..Tana bude kofar ta sako kai daidai shima ya sako kai karapp sukayi karo da rasheed wanda ya kwana ba dadi ji yayi kamar akan dutse ya kwana dan da ya tashi saida yayi press up kadan kafun ya shigo dakin da niyyar yin alwala dan har wani zazzabi yake ji wanda da alama buguwar da yayi jiya ne ya zuba masa zazzabin dan wurin ya kumbura sosai…Bude baki tayi da niyyar zunduma ihu yayi saurin cafkota ya matse ta a kirjinshi hadi da toshe bakin da hannunsa, kokarin kwacewa ta dinga yi tana kokawa dashi dan ba karamin tsorata suheer tayi ba, ganin da gaske ta tsorata ya dan rankwafo daidai kunnenta ya ce “ke nine fa,me kikeyi haka”?
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke da sauri jin muryarshi saketa yayi ya shige toilet din without looking at her, bakin gado suheer ta zauna tana dafe kirjinta sai a lokacin ta tuna bata da hijab faa gashi ya wani riketa kamar….Turo baki tayi gaba ta mike ta dauko brush da maclean nata ta matsa ta zauna rasheed ya jima sosai a bayin dan saida yayi wanka da ruwan masu dumu kuma ya gasa goshinsa kafun ya fito daure da bathrobe fari sol yana zuba kamshin liquid soap kala kala dayake amfani dasu. Kallo daya ya mata yace “damn it! shigaba daya ya manta da akwai yarinyar a dakin da bazai fito a haka ba salon ta raina shi duk an takura mutum shida dakinsa amma bazai sake ba, suheer da kanta ke kasa tunda taji karan bude bayin bata dago ba ta kasan ido ta ke kallon fararen dogaywn sawunshi masu dauke da gargasa kamar baya shiga rana, wucewa yayi cikin closet nashi ya ya shirya cikin jallabiya ya fito ya wuce gaban mirror ya bunka turaruka kana ya wuce masjid dan har an fara kiraye kirayen salla.
Suheer ma brushing tayi ta dauro alwala ta dawo ta shimfida pray mat da ta gani a wurin ta bude jakanta hadi da fiddo wani dagon riga mara nauyi da wani hijab din, bata manta wuyan baccin da tasha jiya ba sakamakon kwana da atamfa, shiryawa tayi ta linke wanda ta cire kana ta kabbara sallar rak’atal fajr sai bayan da ta idar da asuba ta zauna tana askar nata a ranta ta tunano amminta da fareeda ko me sukeyi yanzu, ko suma suna kewar ta? koya jikin kawu lamido gashi bata zo da wayarta ba, wani kuka ne ya taho mata ta toshe bakinta tayi mai isarta ta goge hawaye, zuwa lokacin gari ya fara haske mikewa tayi ta fara gyara dakin duk da ba abunda ya sameshi amma saida ta dan karkade gadon ta goge ko ina wani burner ta gani jikin soket hakan yasa ta debi turaren wuta da ta gani kan mirror tazo ta zuba ta kunna tana mamakin dakin namiji da turaren wuta! take dakin ya dau wani kamshi mai dan karen dadi, bayi ta wuce nanma ta tsafta ce shi duk daba wani datti, sannan ta tube ta yi wanka ta fito tsab abunta ta dauro towel nata da ta shigo dashi ta fito kimtsawa tayi cikin wani dogon rigar again bayan ta shafa roll on nata mai dadin kamshi kana ta fesa bude spray nata na albakhur sannan ta kawo turarenta oud kareemat ta fesa kana ta dau wani abu adan karamin kwalba wanda ban ga sunanshi ba naga ta goga a bayan kunnuwanta take wani masifaffen kamshi ya bade dakin, hakan bai isheta ba naga ta fidda wani shima dan karami ta bude bakinta ta feshe nanfa kamshi irinna strawberry flavour ya kuma tashi, (a raina nace kamshi da kamshi sun hadu kennan don haka sun zama kamshaye????).
Zama tayi a bakin gadon bayan ta zura hijab nata tana ta wasa da hannunta dan bata san kuma me zata yi ba. Har karfe takwas suheer na zaune wurin taji ana kwankwasa kofar tasowa tayi ta bude suka hada ido da ummie sunkuyar da kai tayi tana wasa da ya hannunta cikin nutsuwa kuma ta zame ta tsugunna kasa tace “ina kwana ammi, ummie da tayi mutuwar tsaye ta dago ta tana kare mata kallo ciki da waje tace lafiya yata ya bakon wuri?, suheer bata ce komai ba dan ummie ta tsare ta da ido, ta kuma cewa yaya sunanki, cikin sanyin murya tace “Suheer, ammm Aysha Suheer kara bude ido ummie tayi tana kallonta tace nice name muje ku gaisa da dadynku don zai fita ne,….Binta kawai suheer keyi kanta a kasa amma duk da haka bai hanata ganin kyau da tsaruwar gidan ba, gaishe da alaji umar tayi wanda yake shirye cikin wasu fararen kaya da babbar riga kai da ka ganshi kasan kudi sun zauna masa yace “Allah ya albarkaci aurenku, sai kuma ayi ta hakuri kinji zaman aure gaba daya dab hakuri ne bare ma in an hada ka da mutum irin rasheed, da sauri ummie ta kalleshi amma ya kawar da kai yaci gaba da magana wanda mafi yawanci kushe rasheed ya keyi…..Bayan fitar shi ummie ta kunnawa suheer kallo tace “yata kiyi kallo bari in hada mana breakfast tunda ya kore mana yan aiki jiya, ta shige kitchen, a hankali suheer ta mike ta wuce kitchen din tace “zanyi aikin ai ammi, ummie tace “a’a je ki huta yata, sannan zanyi farin ciki idan kina kirana ummie, dan murmushi suheer tayi ta karbi peelarn hannunta ta fara fere irish din, dole ummie ta bar mata ta kama wani aikin……Aiki sukeyi a nutse ba mai cewa komai saidai lokaci zuwa lokaci ummie na juyowa ta kalli suheer tayi murmushi, bude kofar palon akayi rasheed ya shigo cikin kayan jogging da alama motsa jiki yaje tun asuba din, ya wuce bangarenshi direct ya shige da nufin watsa ruwa turuss yayi a dakin jin wani mahaukacin kamshi yana fita mabambanta woww yace i kike it, sai kuma ya zaro ido yace ina yarinyar nan, nan ya hau dube dube amma bata ba dalilinta, ya dawo palo nanma bata nan, zuciyar shi na bugawa ya sauko kasa da sauri nanma ya duba ko ina bata nan inna lillahi ya furta da sauri ya nufi kitchen jin karan kwanuka yana budewa idanunshi ya fada kanta tsaye take bakin gas cooker tana aikin juya dankali cikin mai, cikin sakwan daya ya juya ba tare da ta ganshi ba, ta dai ji karan bude kofa amma bata ga waye ba, ummie ta fito daga cikin store din dake kitchen din tace “waye ya bude kofa cikin nutsuwa tace “bansani ba ummie….Haka suheer ta wuni tare da ummie har yamma bata barta tayi tunani ba ga ranta cike fal da tunanin yan gidansu, tun da asuba bata kara saka rasheed a idonta ba kuma bata damu ba, Adeel ma yau karfe bakwai bai sameshi a gida ba kasancewar yana da lectures na safe..lokacin girkin lunch ma tare sukayi bayan sungama ne ammi tace mata taje ta huta a sama wucewa tayi zuwa sama sanda tayi wanka kafun ta yi sallah kana ta bude pejin tunani.