AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

     ****************************

Saida fareeda ta kwana har washe gari misalin takwas na safe kafun ta farfado, ammi tayi kuka harta godewa Allah tana ganin kamar duniya ya juya mata bayane ya barta ita kadai cikin kadaici, dan ma hajiya saratu na tare da ita, likita ne ya shigo ya kara duba ta gami da mata wasu aune aune kana ya cire ledan ruwan da ya kare ya daura mata wani ya dura wasu allurai cikin ruwan, ruwan na fara shiga jikinta wani bacci ya dauketa, zuwa yamma jikin fareeda yayi sauki…..ammi na zaune a kujerar dake gaban teburin likitan, tsawan lokaci ya dauka yana rubuce rubuce jikin takardar da zai basu sallama sannan ya dago yana kallonta yace “hajiya zamu baku sallama domin physically patient namu ta warke but mentally…Dan shiru yayi kamar mai nazarin abunda zai fada, zaro ido ammi tayi tace likita me kake nufi? kamin bayani dan Allah,” yace “kafun komai inason sanin me ya haddasa mata sumar da tayi? amma ina son kimin bayani gaba daya, i mean karki boye min komai dan mu samu saukin warware matsalar.

Nan ammi ta warware mishi komai na rayuwar fareeda daga kan burinta na son zama jaruma har kan auren rasheed da suheer wanda shine mafarin ciwonta, ba abunda dactan keyi sai gyada kai, har ammi takai aya.

Cire glasses nashi yayi ya share zufar dake tsatstsafo mishi a goshi kana ya mayar yana kallon ammi yace “yarki was depressed, kuma bincike ya nuna mana cewa ta dade cikin damuwar inaga wannan issue din ya kara tabarbare abun ne,” inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un ammi ta furta tashin hankali karara fuskarta tace “dacta kana nufin fareeda tana da cutar depression?” dr, yace “kwarai kuwa kuma ta dade tana cikinshi kawai dai tasirinsa ne bai baiyana ba sai yanzu,…Wata kila baki maida hankali bane amma da zaki fahimci hakan, with shock ammi ke kallon dr tana tuna irin halayen fareeda a bangare guda kuma tana tuna irin wuyan da tsangwamar da tasha hannun alaji samaila mahaifinta lokacin da tana karama, ajiyar zuciya ta sauke jikinta yana ta karkarwa tace “yanzu dacta me abunyi?, dr yace well, nikam a matsayina na consultant na gama abunda ya dace inyi kuma alhmdllh ta ji sauki yanzu abunda ya rage shine a tura ku kuga therapist shi zai daura ta akan magani kafun abubuwa su baci gaskiya,

Hannu ammi ta daura akai tace inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, dacta faredar tawa ce za atura gun likitan kwakwalwa? “……

JUMMA’AT MUBARAK MY PEOPLE.

Allah ya sada mu da alkhairan dake cikin wadannan kwanuka goma na farkon wata mai albarka watan zulhijjah, da fatan zamu dage da ibada domin dacewa da falala dake cikin ranakun da kuma rahamar ubangiji.

????????????AUREN~FANSA????????????

                     NA

  ASMA'U    MAI   ANGUWA

            (Ummu  Fadeela)

PAGE 63 / 64.

Dr. Yace karki damu hajiya zata samu lafiya insha Allah, akwai wani likitan da zan hada ku dashi kwararren therapist dr. ne muna ji dashi sosai a nigeria asalin dan nigeria ne amma mazaunin ingila, saidai yana yawan kawo ziyara sosai asibiti mabanbanta cikin fadin kasar nan, yanzu haka muna san ran zuwan shi asibitin nan next week, so zan hada muku appointment dashi kedai wayarki ya zama available kawai, karki daga hankalin ki…….,

Misalin karfe biyar Suheer ta sauko downstair hannunta rike da bucket, tsakanin jiya da yau kawai har ta gaji da hawa da saukan nan, abu sai kace aikin ibada,…Sanye take da wani material mai dan rawa ruwan toka mai ratsin purple riga da siket, siket din ya kamata daga sama daga kasa kuma ya baje, dankwalin material din yana da girma sosai sai ta yafa shi kamar gyale dan hijab biyu aka samata a kayanta kuma duk sun yi datti dayan dashi ta wuni yau dayan kuma ya baci da jinin rasheed jiya da dare, don haka ta wanke su neman inda zata shanya su take hakan yasa ta saukowa, ummie na zaune palo hannunta rike da remote control tana canja tasha, jin taku yasa ta juyowa kure suheer tayi da idanu tana jinjinawa ubangiji bisa kyawun surar da yayiwa wannan baiwa tashi. Sunne kai kasa suheer tayi bayan ta tsugunna tace “an wuni lafiya ummie?” tana murmushi ta amsa da “lafiya lau yata, ya gajiyan aiki?” shiru suheer tayi tana wasa da hannunta, zuwa can tace “dama hijabs nawa zan shanya kuma bansan inda zan kai ba. Ummie tace “ha’aann mai ya kaiki wanki ke kuma da akwai masu wanki ai karki sake wahalar da kanki kinji ko?, shiru tayi nanma, ummie tace jeki backyard akwai igiya a wurin saiki shanya, ta nuna mata hanyar kitchen tace “kibi ta kitchen zai fi sauki.

Fili ne yalwatacce ta gani bayan ta fito ta kofar kitchen din, shanya hijabs nata tayi kana ta ajiye bucket din a gefe, wani dan dogon hanya ta gani ba tare da wani tunani ba tabi hanyar haka kawai taji sha’awan zagayen wurin dan sosai ya dauki hankalinta.ciyayi ne kwance koraye shar, ga wasu bishiyoyi kanana amma kuma suna da yaya duk wani dangin fruit akwai shi a wurin, ga kukan tsuntsaye masu kwantar da hankali sai tashi yake a wurin, ga iska mai dadi da kamshi yana ta busowa, lumshe ido tayi ta bude tana karewa wurin kallo, swimming pool ta hango ruwan cikinshi kwance lib gwanin kyau iska yana ta kadashi ga hasken rana dake shirin faduwa ya haske cikin ruwan hakan ya bashi wani kala mai daukan ido, karasa wa tayi kusa da ruwan cikin nutsuwa ta fara tattare kasan siket nata, zaro ido rasheed yayi yace “what is she doing?” yana zaune akan kujera a cikin garden din ya juyo da wani kujerar ya mike kafarshi akai,laptop zaune bisa cinyarshi yana aikin dannawa ya hango ta tana tahowa ba tare da ita tasan yana wurin ba.

Zama suheer tayi bakin ruwan bayan ta gyara siket nata yadda zata ji dadin zaman, farare tas din kafafunta ta sa a cikin ruwan tana dan wasa da shi, bata tsammaci ruwan zai kasance mai sanyi ba saida taji a kafanta, wasa take da kafofinta cikin ruwan wanda inka kalleta zaka gi tunanin cikin nishadi take saidai sam ba haka bane zuciyar ta cike yake da kewar ahalinta da tunanin wane hali suke ciki, me sukeyi yanzu? me yasa basu zo ba kamar yadda suka mata alkawari cewa za su zo?” wasu hawaye ne suka surnano daga idanunta ba tare da ta share ba ta cigaba da lila kafafunta cikin ruwan bangare guda kuwa tana ci gaba da yiwa kanta tambayoyi marasa amsa, rasheed barin aikin da yake yi a laptop nashi yayo ya juyo ya maida hankalinshi kacokam a kanta,….Tsawon minti biyar suheer ta mike tuno ummie na iya nemanta, takalminta ta saka kana ta sauke siket nata tana ta juya ta fara tafiya, arba tayi da wasu kyawawan mangoro jajawur dasu akan bishiyar su, take suka shiga ranta dan jujjuyawa tayi bata ga alaman abunda zata iya ciro mangoron dashi ba, hakan yasa tayi tsalle tunda iccen baida wani tsawo amma ta kasa kamowa, tsalle ta kuma yi nanma bata kamo ba, kamar abun jaraba suheer ta dage sai ta ciro mangoron amma yaki, duk tsallen da tayi sai jikinta yayi rawa musamman kirjinta da bayanta.

Lumshe ido rasheed yayi kana ya bude,ya taso cikin tafiyar shi na kasaita kamar wani basarake ya nufo inda take, tsalle ta kumayi a ranta tana cewa yau saita cire mangoron nan, baya baya suheer ta dawo saura kadan ta fadi kasa yayi azamar rikota ta fada jikinshi, rumtse idanu tayi dan ta gama sadakarwa cewa kasa zata fadi saidai akasin hakan jinta tayi jikin mutum,…Da azama ta juyo dan ganin waye duk da dai kamshinsa ya sanar mata shine a wurin amma batayi kasa a guiwa ba wurin kokarin zillewa hakan kuwa yaba gashin kanta wanda dankwalin ya zame sakamakon faduwar da ta kusa yi bazuwa saman fuskarta, saketa yayi ta kuma yin baya baya zata fadi ya riko waist nata yana karewa gashin kanta kallo, gaba daya rasheed ya shagala da kallon dogon gashin kanta wanda a yanzu ne ya tabbatar ba wig bane gashinta ne, buge hannunshi dake rike da waist nata tayi cikin bacin rai tace “malam sakeni, you dont have right da zaka dinga taba ni duk sanda kaso kamar…..” kafun ta karasa ya saketa ta matsa baya kadan shima ya matso yana daure fuska tamau babu alamar rahama tattare da fuskar tashi, matsawa ta dinga yi yana binta har ta mannu da jikin bishiyan mangoron, dafe bishiyar yayi da hannu daya ya dan rankwafo kanta kadan yace “say that again”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button