AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru suheer tayi ta kasa cewa komai saboda kusancin da suka samu yayi yawa, yace “Bayan kin wulakanta ni gaban dubban mutane, kin tozar tani gaban masoyana, kinsa an kulleni na tsawon lokaci, and kinsa an mareni mari mafi muni gaban ma’aikatana kinsa wadanda suke karkashina suna min dariya a boye,.. Bayan duka wannan me kike tunani? eyye?.
You know what Ayshha?. da wannan tunanin nake kwana nake tashi, taya zan rama abunda kika min bayan ke ba kowa bace a wurin rasheed, first nayi tunanin in batar dake, na kuma yi tunanin in bata miki fuska ta hanyar zuba miki acid, ko kuma in kawo karshen labarin ta hanyar rufe ki a babin rayuwata kana in manta dake na har abada, but no. ya fada yana matsawa daga kusa da ita, Idan na aikata haka then dani da roadside criminals bamu da bambanci, Rasheed is a hero, not a lowly villain. Dan numfashi yaja kana yaci gaba da fadin “gangar jikina ya ce in barki, amma zuciyata tace a’a, idan na barki kinci bulus kenan bayan lokaci kadan zaki manta da waye rasheed bayan shi kin barshi da tabo na har abada, zaki je kiyi aurenki da wannan talakan yaron ki haifa masa yaya ki shayar dasu kuyi farin ciki tare da shi, sannan mahaigiyar ki da wannan jabun baban naki suyi farin ciki suma cewa yarsu tayi aure,.. Zuwa lokacin idanun suheer sun kada sunyi jawur..Yaci gaba da fadin “that’s why naje na auro ki domin in sa full stop a rayuwarki, yanzu akalanki yana hannuna sai yadda naso zan juya ki, kiyi kuka, kishiga tsanani, ki fuskanci wahala da wulakanci nikuma inyi dariya wannan shine burin Rasheed Matawalle kuma ya fara cikashi. Sannan maganar tabaki kuma karki manta sadakina ne akanki, inba don haka ba ba abunda zanyi da wannan kazamin jikin naki.
Dago kyawawan idanunta tayi wanda suka kada sukayi ja tace “Mr Rasheed Matawalle, burinka ka wulakanta ni, kasani a wahala, inyi kuka kai kuma kayi farin ciki, yes kasamu wannan, amma na rokeka ta hada hannayenta wuri daya, dan Allah karka kara sako iyayena cikin al’amarinka, and my habeebi shidin yafi ka alheri sau dubu, domin zai iya sadaukar da komai nasa akaina koda ko rayuwar sane domin inyi farin ciki, kaga ko kuna da banbanci, sannan ina kara jaddada maka karka kuskura ka kara taba min wani bangare na jikina, domin gaba daya jiki da zuciya ta mallakin habeeb ne, ehh shi talakan dai da ka raina shidin nake so kuma shike da hurumin taba ni ba kai da bakasan darajar kanka ba bare wanda yake tare da kai.aurenka kuwa kafi kowa sanin na wucin gadi ne don haka karka kuma.
Wani irin harbawa zuciyar sa keyi jin irin abunda take fada masa ba tare da tsoro ko kuma shakkar sa ba, takowa ya yi zuwa gabanta ya ran kwafo daidai fuskar ta ya zuba mata ido, na yan dakiku especially llips nata da suka dinga jero maganganun sannan yace “come again, banjiki mai kyau ba,” tace……Zaro ido suheer tayi jin saukan bakinshi cikin nata, wani irin kiss yake bata with passion, tsawan lokaci ya dauka yana kissing nata har saida yaji ya fara rasa garkuwar jikinshi inda tayi nasarar tureshi jikinta na rawa kamar mazari. Yana kallonta da rinannun idanunshi bakinshi na dan rawa yace “ki ka kara kuskuren ambatar wani banza a gidannan da aure na akanki saikin gane shayi ruwa ne, and daren yau zan tabbatar miki cewa akwai aurena a kanki kana gangar jikinki bana wancan wawan bane a karkashin iko na yake. Ya juya da sassarfa ya bar wurin ba tare da yabi takan phones da laptop nashi dake zube kan kujerar da ya tashi ba, daura hannu suheer tayi a kai bayan ta dawo daga unexpected shock din da ya sata ta zauna dabas a kasan wurin ta rasa ihu zatayi ko me…..
????????AUREN~FANSA????????
NA.
Ummu Fadeela.
Page 65 / 66.
Tsawon lokaci ta dauka zaune wurin gaba daya kwalkwalwarta ya toshe, ta ka sa sanin wani irin tunani zatayi, da kyar daga karshe tayi kardin halin mikewa zuwa cikin gidan.
Tafiya take tana jin kamar iska zai kadata tsabar rashin karfin da jikinta ke dashi ga kuma bakin cikin wulakanci da rasheed ya mata tana ganin wannan shine wulakanci mafi muni da wani ya taba mata, how dare him zai hada bakinshi da nata, da sauri ta tofar da yawu tace “disgusting” tana kyabe fuska. Lallai rasheed ya wuce limit nashi kuma zata nuna mishi ita ba yar iska bace, sai yayi regretting abunda ya mata.
Lokacinda ta shigo palon ba kowa ummie ta tashi, bangarensu ta wuce da sauri dan bata son haduwa da ita, dakin yana nan yadda ta barshi ba wanda ya shigo ta hau gado ta dukunkune cikin bargo hadi da rufe ido gam, duk ta tuna abunda rasheed ya mata saita kara matse idonta tana jin wani irin faduwar gaba, nan magariba ya same ta da kyar ta tashi tayi sallah, tana zaune har akayi isha nan ma ta gabatar da shi.
Ummie da taga shiru shiru suheer ba ta sauko ba sai bata nemeta ba, ita kadai tayi girkin dinner har ta gama tana cewa dole ta kira ma’aikatan da rasheed ya kora dan baza ta iya aikin ita kadai ba, jere abincin tayi bisa tire hadi da ruwan gora da lemo duk da tasan akwai a can sama, dauka tayi zuwa part din su,….Suheer na kwance lamo taji ana knocking kofa, wani irin zabura tayi kamar wacce aka tsikara,don a lokacin ba abunda ya fado mata sai kalaman rasheed na dazu.
“yata kinyi bacci ne?” jin muryar ummie yasa ta sauke wani irin ajiyar zuciya kana ta taho ta bude kofar, zuba mata ido ummie tayi na dan lokaci ganin alamar tayi kuka, tace “ya maki wani abun ko?”.
Girgiza kai tayi, tace “to me ya sa ki kuka?” take wani kukan ya balle mata cikin kuka tace “kaina ke ciwo”.
Ajiye tiren tayi ta kamo ta suka fito palon tace “eyya sorry, me yasa baki min magana ba da na baki magani ai, maza zo kici abinci saikisha magani kinji ko, yi shiru abunki…..Da kyar ta dan tsakuri abincin kadan don bakinta ba appetite sam, paracetamol ummie ta ballar mata da kyar tasha dan suheer ta tsani magani ba kadan ba.
Har daki ummie ta maida ita saida ta shiga bayi ta kuskure bakinta da listerine sannan ta fito ta samu har ta fitar mata da wani kayan bacci daga cikin akwatin ta, tana kallonta tace meyasa baki shirya kayanki a ciki ba? ya kamata ma ki samu wasu karin kayan inaga ko zuwa gobe sai mu fita mu duba ko?.
Ita dai bata ce komai ba,saida ummie ta tabbatar da ta shirya yadda ua kamata ta kwanta sannan ta rufa mata duvet kana ta rage mata AC tace Allah ya sauwake ko yata,zuwa safiya dr. Zai shigo ya dubaki kinji.
Tana kwance har wurin karfe goma amma bacci barawo yaki saceta, tunanin gida kawai take yi, a bangare daya kuma abunda rasheed ya mata yaki barin ranta, juyawa tayi ta murguda baki a fili tace “mtssssw dan iska kawai.”
Daidai lokacin rasheed ya shigo palon, zama yayi saman doguwar kujera yana dafe kanshi, tun bayan faruwar incident din har yanzu bai dawo normal ba, dan iska ya huro daga bakinshi, gashi yanzu yana so ya kwanta amma bazai iya kwanciya saman kujerar ba dan ba karamin wahala yasha jiya ba, “tsoronta kake ji ne da baza ka sata ta saukar maka a gado ba?” zuciyar shi ce ta fadi hakan.
Mikewa yayi yana gyada kai ya nufi dakin, hannu yasa kan switch ya kunna wuta take dakin ya gauraye da haske kara matse jiki suheer tayi tana jin yadda bugun zuciyar ta ke sauyawa tun shigowar shi, kallo daya ya mata ya nufi kan mirror ya zube wayoyinshi a wurin kana ya wuce bathroom.