AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da hanzari ta mike zuwa kan mirror din ta dauki waya daya ta bude taga da security, ta duba dayan ma still da security, cikin sa’a ta daga na ukun sai ta samu babu password da sauri ta fita waje inda ta rufe kofar a hankali dube duben inda zata zauna ta farayi kamar munafuka, daya daga cikin kofofin dake palon ta kama a zatonta daki ne, wani iska mai dadi ne ya buso ta bayan ta fito, hadadden balcony ne, akwai rug a wurin da kuma kujerun silba guda biyu, takowa tayi har bakin railers dake wurin ta kama ta rike tana hango sauran gidajen anguwar a can kasa, tace “hmmm ba dole ku ringa taka mutane yadda kuka ga dama ba kuna ganin mutane a kasanku, zama tayi kan daya daga kujeru biyu dake wurin ta harde kafa, numban ammi ta zuba cikin wayar kana ta danna kira.

Cikin sa’a bugu biyu ammi da ta gama ba fareeda magani yanzu ta daga, ba tare da tasan waye ba, sallama tayi jin muryarta yasa suheer fashewa da kuka, sosai jikin ammi yayi sanyi jin muryar ta tana rera kuka mai taba zuciya, cikin sheshsheka tace “ammi me yasa baku zo ba? kuma bayan kunce zaku zo, kun barni nikadai inata kewanku, ina sweetheart,? ya jikin kawu lamido,?.

Ajiyar numfashi ammi tayi cikin aro jarumta don bata son yar tata ta fahimci halin data ke ciki tace “ya kuke a can hope dai komai lafiya ai ko,? goge hawaye suheer tayi cikin sanyin murya tace “eh ammi komai lafiya”,

Daga jin muryarta tasan tana cikin damuwa don haka tace “kina jina dota, kiyi hakuri da yadda rayuwa tazo maki, ki kasance jajirtacciya akan lamuranki, rayuwar amminki ya zama darasi a gareki, kamar yadda ta fito wani dare damke da hannun yar uwarki, dafe da cikinki na kimanin watanni bakwai kana rike da naira dari da hamsin kacal, ta fita ba tare da tasan inda zata je ba amma hakan bai hana ta yin nasara ba saboda ita din ta kasance jajirtacciya, haka nake so ki zama a gidanki…..Sosai ammi tayi mata nasiha mai shiga jiki har saida taji ta fara dariya kafun ta barta.

Cikin sanda ta kuma komawa dakin, cikin sa’a kuwa har lokacin bai fito daga bathroom ba,ajiye wayar tayi inda ta dauka bayan tayi deleting layin ammu ta koma ta kwanta tana tunano irin maganganun da suka yi da ita.

Saida rasheed ya gabatar da uzurinsa akan toilet kafun ya zo ya yi wanka wanda ya dauke shi tsawon lokaci kamar mai shirin canja fatar jikinsa, lokacinda ya fito kwance ya ganta ba alamar ta motsa, shirya wa yayi bayan shafe shafe da gogen shi kamar wata mace, sannan ya nufo gadon….., wani irin yunkura tayi zata sauka gadon bayan ya zauna cikin zafin nama ya cafko hannunta dabas ta dawo ta zauna yana kallonta strictly yace “ina zaki?, wato ga stranger ya hau gadon ko?, to karki manta nan gado nane kuma ina da ikon hawan shi duk sanda naso,” sake hannunta yayi ya dau kananan pillows dake kan gadon ya jera su a tsakiya ya kwanta yaja duvet.

Maganar shi ya kular da ita sosai don haka cikin turo baki tace “dadin ta nima dai kasan ina da gadon a inda ka dauko ni, sannan inba don darajar ummie ba da ba abunda zai sa ni kwanciya kan wannan gadon ta fada tana buga katifar.

Dago kanshi yayi yace “really” ? tace “yess”, da gudu ta dirka daga gadon ganin abunda yake kokarin yi ta fita palo hadi da rufe kofar bamm ta tsaya tana sauke numfashi, murmushi mai kyau rasheed yayi yana shafa lallausan gashin kanshi ya koma gadon ya kwanta abunshi hadi cewa “now bawa zaiyi bacci ba tare da takura ba.

Suheer na zaune wurin kusan minti biyu amma kirjinta bai daina bugawa ba, ga wani tdoro da ya mamaye ta wannan ma palon ta ko ina haske ne, a haka tana zaune tana kulla wasikar jaki bacci ya dauke ta.

Rasheed ne ya fara farkawa da asuba wani irin kamshi yake shaka mai dadin gaske, a hankali ya gama bude idonshi ya sauke a kanta tana baccinta peacefully, dogon karan hancinta yabi da kallo har zuwa kan pink lips nata rufe ido yayi ya bude yana tuno yadda ya dauko ta daga palo da dare,kana ya matsar dakanta a hankali yana zare hannunshi dan da damtsen hannunshi tayi filo, yana mamkin ko ina pillows din da ya jera a tsakiyan gadon? can ya hango su a kasa kuma da alama shiya je inda take dan gaba daya ya bar inda ya kwanta, mikewa yayi zuwa bathroom don dauro alwala.

Lokacin da ta farka da asuba mamaki mai hade da tsoro ne ya diran mata ganinta kwance kan gado bayan tasan a palo ta kwanta, bata gama fita daga firgicin da ta ke ciki ba rasheed ya fito daga toilet hannunshi daya rike da karamin towel yana goge kanshi….Zaro ido suheer tayi ta fara tattaba jikinta dan tabbatar da ba abunda ya sameta. Ta gefen ido yake kallon duk abunda take yi saidai baice mata ko uffan ba har ya gama shirinsa ya zura jallabiya ya tafi masjid….

Yau kwanan suheer hudu a gidan rasheed, tsaye take a kitchen da safe tana taya ummie girkin breakfast ita kuma ummie tana zaune kan daya daga kujeru hudu da suka kewaye wani babban tebur dake tsakiyan kitchen din tana kallon yadda suheer take aiki cikin nutsuwa,….Murmushi tayi jin abunda suheer ta fada tace “ina jinki ki tambaye ni duk abinda kike son fada nidin mahaifiyar ki ne ai.

Tsunkuyar da kai tayi a hankali tace “ummie meyasa baya gaisheki,? kuma ko kin masa magana baya amsawa saidai inga ya tsaya kawai, ko bai san hakan ba kyau bane ?. Take mood na ummie ya chanja wasu kwalla masu zafi suka gangaro mata, tana kallon suheer tace “kashe gas dinnan ki matso nan yata,yau zan fada miki waye rasheed yau zaki san dalilin da yasa baya gaisheni, ba tare da yayi binciken komai ba ya daina min magana a matsayina na wacce ta haife shi, baisan cewa nayi hakan ne for his own good ba, rumtse ido rasheed dake bakin kofa yayi yana jin zafin zuciyar shi yana karuwa, yazo shiga kitchen dinne da niyyan daukan sweeper da mop dan share balcony dinsa yana son yin wani aiki a wurin tunda ya kori masu aikin gidan wurin bai kara ganin tsintsiya ba, caraf kunnenshi yaji tambayar da suheer tayiwa ummie hakan yasa ya dan saurara,.

Ummie ta share kwallar da ya ki tsayamata ta ja wa suheer kujerar dake kusa da ita tace “zauna” ba musu ta zauna, dan shiru tayi kafun ta fara ba suheer labarinsu kamar haka………

Alhamdulillah. masoya Auren Fansa ina godiya a gareku kan yadda ku ke jimirin bin wannan labari duk da ba kullum nake samun yi muku update ba, hakan ya faru ne saboda sabgogin da suke kaina sun min yawa,……Ina mai baku hakuri yanzu ma zaku jini shiru har zuwa bayan sallah idan ubangiji ya bamu aron rai da lafiya, kuci gaba da hakuri da kuma juriyar bibiyar alkalamin Ummu Fadeela na gode da fatan zamuyi babban sallah lafiya…

????????AUREN~FANSA????????

Page 67 / 68.

…..Malam Abdullahi, Wanda aka fi sani da mala audu mai guga. Haifaffen garin kano ne unguwar dorayi.Ya samu sunan shi na mala audu mai guga ne sakamakon sana’arshi ta wanki da guga wanda shima gadar sana’ar yayi daga wurin mahaifinshi.

Mala audu mai guga yana da mata biyu da yaya hudu, ba laifi talaka ne irin sosai dinnan,uwar gidanshi mairo wadda yara ke kiranta mama tana da yaya uku maza biyu da mace daya, sadisu shine babban su ana kiranshi sadi, sai talatu mai bi mishi suna kiranta addatu,sai auta umaru.

A bangaren amarya larai kuwa da daya Allah ya mallaka mata a duniya Ahmad wanda suke kira matawalle da ya ke sunan kakansu wanda ya haifi ubansu yaci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button