AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nifa manyan kuɗi nake magana a kai ba irin wannan ba. murmushi malam idrisu ya kuma yi kana yace” ta yaro kyau take bata ƙargo, idan har kuɗi kake so da gaske tashi zakai ka nemo su ta hanyan da ta dace, tunda ba kana kwance za’amaka ruwansu daga sama ba.

Don haka daga yanzu na baka gona ta na shinkafa, bana kai zaka noma ta, sannan na baka gonar da ke bakin kogi kayi noma rani a wurin, noma zaka yi na gaske da gangar jiki da zuciyar ka zaka samu arziƙi da gumin ka na halak.”

Wannan shine mafarin shigar sama’ila harkar noma, cikin lokaci kadan Allah yasawa abun albarka yazama duk yankin ba wanda ya kaishi samun amfanin noma rani, da damuna. cikin shekaru huɗu ya mallaki manyan gonakin da yake noma duk wani nau’i na kayan abinci, a gefe guda kuma ga dabbobi irinsu shanu, tumakai ,awaki, da kuma kaji .

Lokacin da sama’ila ya gama gina ƙaton gidanshi ginin bulo da ba mai irinsa duk ƙauyen kamar yanda yayi buri sai yazowa mahaifinshi da batun sonyin aure, malam idrisu ya nisa yace” naji daɗin wannan tunani da kayi domin kamalar mutum bai cika sai yanada aure, walau mace, ko namiji, yanzu akwai wacce ku ka daidaita ne kodai can gida zamuje a duba maka a dangi?

Sama’ila ya sunne kai ƙasa yana sosa ƙeya yace” baba anan na samu itama na gida ce” “ah to madallah yar waye s garinnan sai in samu babanka yusha’u muje muga iyayenta”.

Sama’ila yace ” ae habiba ce yar gidan baba yusha’un”

Da farin ciki malam idrisu yace masha Allah kace tuwo na maina zs’ayi kenan , wannan abu yamin daɗi tashi kaje zan samu babannaku muyi magana Allah ya muku albarka.” da ameen ya amsa kana ya miƙe ya tafi.

Koda idrisu ya samu amininsa da batun,yayi matuƙar farin ciki shima nan take a ka fara shirin biki domin ba’a samu tangarɗa daga bangaren kowa ba , ranar wara jumma’a jama’a suka shaida auren sama’ila da habiba (tabawa).

Shekara guda da aurensu amma tabawa ko ɓatan wata bata taɓa yiba wannan abu yana damunsu, domin wani irin masifar kaunar ƴaƴan da Allah ya ɗorawa ssma’ila, sun yi maganin gargajiya har sun gaji amma ba wani sauyi, hakan yasa suka garzaya asibiti ,gwajin farko ya tabbatar musu da cewa tabawa ce mai matsala nan aka ɗaura ta akan magani

Aiko suna dawowa gida sama’ila yayi tsalle ya dire yace lallai lallai aure zai ƙara domin yana son ganin ƴan ƴaƴa shima, ganin tabawa ta tada hankalinta har tana ƙoƙarin tafiya gida ne yasa sama’ila kwantar mata da hankali da cewa” duk wacce zan auro a bayanki take tabawa, ke kinsan wannan ke ce uwar gida na sai yadda kikaso za’ayi, ganin maganganunsa suna tasiri a kanta ne yace “kuma hajjin bana dake za’ayi nan take farin ciki ya lulluɓe ta ta manta da wani batun aure.

Haka kuwa akayi cikin wattani uku sama’ila ya auri wata ƙaramar bazawara sakun wawa mai suna balki,domin wattani bakwai da aurenta suka rabu da mijin.

Bayan wata biyu da tarewar balki gidan sama’ila, al’ummar yankin goruba suka wayi gari da mummunan labari na rasuwar sarkin noma bubakari sakamakon ɗan gajeruwar jinya da yayi.

Wannan rasuwa shi ya zamo silar faruwar komai na rayuwar gidan sama’ila dalilin son zuciya irin nasa da kuma mummunan aboki.

Bayan anyi sadakar bakwai na sarkin noma sai rikici ya barƙe akan waza a bawa sarautar sarkin noma, dayawan mutane sun zaɓi sama’ila matsayin sarkin noma, amma wasu daga mutanen ƙauyen sunyi watsi da batun a cewar su sama’ila baƙon haure ne dan haka baƙo bazai riƙe musu wnn muƙami ba, hankalin sama’ila ya yi mugun tashi domin yaga samu yaga rashi irin wannan damar ya daɗe yana yana nema amma gashi nan rana tsaka wasu zasu hana shi.

Rikicewar da yayi ne yasa bala abokinshi tun na ƙuruciya yimasa tayin zuwa wajen wani hatsabibin boka a jihar taraba,

“kasan Allah abokina aikin wannan boka kamar yankan wuƙa yake, zaka sha mamaki inmunje kaf ƙauyennan sai abunda kace za’ayi a ɓangaren noma, kaidai kuɗi kawai zaka fitar mutafi gobe gobennan.

Haka kuwa a kayi sama’ila da bala suka tafi jihar taraba bayan kwana biyu da tattaunawar su ,( suka tafi neman yardar wanin ALLAH, akan mulki da arzuƙi dai wadda ya lalata zuciyoyinmu, babu babba babu yaro, kowa so yake ya zama shine shugaba, baga babban muƙami ba ba ga ƙarami ba, kowa so yake yazama shike mulkar jama’a a ringa binshi ana masa fadanci, bana birni ba na ƙauye kowa so yake ya zama shike bada umarni sauran jama’a su zama masu bin umarninsa, Ya Allah ka iya mana badan halayenmu ba).

Bayan sauƙar su a jalingo babur mai kafa biyu suka hau suka nausa wata hanyar, tun sama’ila na ƙirga kauyuksn da suke wucewa har ya gaji, a ƙalla sunyi tafiyar awa biyu da rabi bisa babur kafun suka sauƙa a wani ɗan karamin ƙauye. washhh. gaskiya tafiya yankin azaba, cewar sama’ila yana baza idanu da tambayar ina gidanne bala?

Ɗan murmushi bala yayi kana yace “da saura ae, a iya nan babur yake iya tsayuwa ,sauran tafiyar na ƙafa ne.”

Ido ya zaro yace ” Ban fahimta ba bala”
“zaka fahimta ne” cewar bala yana miƙar hanyar dake gabansu. da sassarfa sama’ila ya bishi, saida suka ƙara shafe a ƙalla awa guda suna tafiya akan ƙafafunsu cikin ƙasurgumin jejin kafun wani dan bukka ya bayyana a gabansu ,” mun iso” cewar bala,

Samaila ya dubi gabas da yamma kudu da arewa ba wani gida ko alamun motsin yan adam sai jeji baƙiƙƙrin sai kuma wsnnan bukka da ke gabansu yanzu, a hankali suka nufi cikin bukkar wanda ba komai cikinsa sai dakin gizo gizo da ya cika ko wanne angle na dakin, hakan yasa tsikar jikin samaila tashi, bal…da sauri bala yakatse shi daga maganar da yayi niyyar yi, inda yamasa alamar kayi shiru ba’a magana,

Wata iriyar mahaukaciyar dariya aka kece da shi from no where wanda yasa ɗakin ya dara jijjiga kamar zai balle take kasar wurin ta fara tsagewa wanda hakan yasa ka sama’ila sakin fitsari a wando yayinda suka maƙale juna tare suna cigaba da jijjiguwa lokacin da dariyar ta lafa kasar wurin ta dare saiga wani m………..

kuyi hakuri da typos bansamu nayi editing ba.

LIKE COMMENT AND SHARE

comment naku shizai ƙara min karfin gwiwa one love guys…
Bismillahir Rahmanir-Raheem.

????????????AUREN FANSA????????????

            NA 

ASMA’U MAI ANGUWA
(Ummu Fadeela)

TYPING????

BOOK ONE

Page 6&7

……A hankali dariyar ta tsagaita kana bukkar ta koma ta tsaya cib tamkar ɗaukewar ruwan sama,sai kuma tsakiyar bukkar ta dare wa a hankali ta bude saiga wasu matattaka sun bayyana, “ku shigo”a kafaɗa cikin wata iriyar murya marar daɗin sauraro,

Bala ne yayi ƙarfin halin sakin sama’ila wanda a lokacin daza’a tsaga jikinshi baza’a samu koda ɗigon jini ba,tsabar firgitar da yayi. kana yaja hannunshi suka nufi stairs ɗin,

Sake baki samaila yayi ganin sun bayyana a wani makeken fada mara kyan gani ,(mamaki yake yanxu wannan a cikin ƙasa fa suke), duk inda ka wurga idonka kasusuwan kayukan mutane da na wasu hallitunne a sarƙafe, kana ga wasu jajayen kyalle a ɗaɗɗaure, sai kuma wasu rubutu da aka yisu da akayi su da jini wanda na kasa fahimta sai dai yafi kama da rubutun mutanen CHINA.

Wani jibgegen mutumne,baƙiƙƙrin, mai jajayen idanu tamkar attaruhu, kana da wasu wadatattun hanci tamkar kofar shiga gari, jikinshi ba kaya sai wasu tabka tabkan layu dake ɗaure kowacce kusurwa ta jikinshi sune a madadin sutara,zaune yake a kan fatar damisa, kai da ka gansa kaga wakilin shaiɗan la’anannen Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button