AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Soyayya da tarairaya ba irin wanda batool bata samu ba tsakanin mijinta da umma, saidai tana fuskantar kalubale nan da can a wurin mama, amma da shike wayayya ce ta iya zama da kowa, cikin haka ta samu juna biyu, nan fa tarairaya da kula ya karu, umma ta daura gaba daya burinta akan wannan ciki kasancewar bata da yaya matawalle kam ba’a magana, duk abunda ya gani na baby siya yake tun cikin bai yi wata uku ba.

Haka sukayi ta renon wannan cikin da tun ba haifeshi ba ya gama shan gatan duniya, lokacinda cikin yayi wata tara, wata rana batool ta tashi da nakuda cikin dare, ranga ranga aka nugi asibiti da ita cikin awa daya ta santalo kyakyawan jaritinta mai kama da ita sak,ba abunda yaron ya manta na uwarshi,saidai da alama zaiyi irin jikin uban, duk wanda ya ganshi sai ya kuma kallo tsabar kyau kai zakayi tunanin duk uwa da uban larabawa ne.

Ranar suna yaro yaci sunan Abdulrasheed, sai aka yanke ake kiranshi Rasheed kawai. Ba irin gatan da rasheed bai samu ba daga wutin umma da abbun shi, ummie kam sai nade hannu tayi ta zuba musu ido dan wata rana shan nono ne kawai yake kawoshi wurinta. Daga karshe ma hada mishi kayanshi tayi ta mayar wurin umma,aiko duk dinsu sunji dadin hakan.

Saida rasheed yayi shekara uku cur kafun ummie ta shirya bisa rakiyar matawalle suka je morocco ganin gida iyayenta sunji dadi matuka ganin yadda yarsu tayi shar da ita ga kuma soyayyar da mijinta ke nuna mata a gaban kowa, saidai daga wannan zuwa ne ummie bata kara taka kafarta zuwa gida ba har tsawon shekaru nan.

Bayan dawowansu daga morocco aka dawor wa matawalle gold nashi daga kasar NEWZEALAND, inda aka sarrafashi zuwa kayan ado da qawa na mata dangin dan kunne da sarka,aworworo,zobe, agogo, abun hanci. Ba abunda babu ya bude babban kanti ya zuba su ciki, wasa wasa abun ya karbe shi cikin lokaci kadan ya zama wani hamshaki,a hankali ya fara bude branch na kantin shi ba iya nigeriya kawai ba harda kasashen ketare.

Kana ya fara gina tampatsetsen gidanshi hawa biyu dake nasarawa inda suke a yanzu,at the same time kuma ya biya wa duk yan gidan makkah harda matar sadi da su umaru da addatu da mama,umma ummie sukaje suka sauke faralli.

Rasheed na da shekara bakwai ga kyau ga ilimi ga gata yaro ne mai fara’an gaske da son mutanr hakan ne ma ya bashi farin jinin jama’a wanda yake binshi har yanzu, rasheed ya taso da sha’awar wasan kwaikwayo tun yana yaro hakan yasa da ya girma ya shiga harkar fim badon a biyashi ba saidon cika buri,saigashi duk fim din daya fito a ciki a take yake karbuwaa har ribibin zuwa cinema ake kallon rasheed.

Yanadan shekara bakwai abbunshi ya samu mukamin ministern albarkatun kasa na nigeriya, ya salam likkafa taci gaba yayinda hatred na mama da yayanta musamman umaru ya karu fiye da farko,sunsha alwashin kota halin kaka sai sun mallaki dukiyar matawalle.

Rasheed yana da shekara goma a duniya wata rana sundawo anguwa da ummien shi suka tadda abunda ya girgiza su,abunda ya rudasu ya bar musu tabo na har abada a rayuwarsu ya dauke fara’a daga fuskokinsu.

Wuta duka samu yana ci bal bal a bangaren umma ga ihu da salatin umma da abbu na tashi a ciki saidai ba mai iya tunkarar wurin tsabar karfin wutar, ihu rasheed yake yi yana kiran abbu umma ku fito wuta wuta, fizge wa yayi ya nufi cikin wutar da karfi wani irin iska da hucin wuta yayi sama da shi ya turo shi baya saiga rasheed a kasa farin fuskar shi yayi bakikkirin.

Kukan neman dauki ummie take yi amma shiru da alama ma gidan ba kowa hatta security dake bakin get sai yanzu ta tuna bata ga ko daya ba.

Daga rasheed tayi tana ci gaba da jiyo ihun umma da abbu ta nufi bangaren mama, dan dakatawa tayi zuciyarta na bugun uku uku hin abunda ake fada, umaru ne tsaye tsakar palon hannunshi rike dakan wayar landline irin na da yana magana da dan karfi karfi, mama kuwa tana zaune bisa kujera ta daura kafa daya kan daya.

Rasheed da yaji duk abunda ake fada a wayar shima ya wage baki da nufin kurma ihu, da sauri ummie tasa hannu a bakinshi ta matse iya karfinta…

Barkanmu da sallah my people. Da fatan Allah ya karbi ibadunmu ya nuna mana wasu shekaru masu albarka cikin imani da tsoran Allah.

Kuma dama kowa ta kullo min suya na ????????
????????AUREN~FANSA????????

Page 69 / 70

…..Tamqe bakin rasheed ummie tayi da kyau ganin ya na ta fizge fizge,daga ciki kuwa alaji umaru ya ci gaba da fadin.”aikinku yayi kyau fa bangiss karku damu nan ba da jimawa ba zaku ji alert na saura rabin kudin….Sai kuma dayan assignment din”, dan shiru yayi kafun yace. “Eh matar da danta.,.. to shikenan”. kallonshi mama dake hakimce tayi tace. Amma ina ganin ba amfanin kashe batool kawai abunda ya kamata……Rada mishi magana tayi a kunne wanda nidai banji mi tace ba,wani irin dariya suka bushe dashi a tare, yace “good idea mama”.

Da sauri ummie ta juya zuciyar ta na bugun tara tara yayinda rasheed ke ta zaro ido ya na kokarin kwace kanshi saidai ba karamin riko tai mishi ba.

Fitowar su yayi daidai da shigowar motar yan kwana kwana sakamakon kiran da mai gadi yai musu, shima dawowar shi kenan daga aiken da hajiya mama ta mishi duk da baiso ba amma saida ta tilasta mishi, haka tabi duk securities dake gidan ta aikesu kafun su aiwatar da kudurinsu.

Da kyar yan kwana kwana suka samu nasarar rage karfin wutar har aka shiga a ka fito da umma da kuma matawalle wanda zuwa lokacin sun kone kurmus tamkar gawayi.Kallo daya ummie ta musu ta fadi kasa sumammiya. Rasheed kuwa da gudu ya tafi ya rungumesu duk kuwa da yadda jikinsu ya zama,duk yanda yaso yin kuka kasawa yayi sai wani irin numfashi da ya ke saukewa da sauri sauri ga wani irin jawur da idanunshi suka yi,…tunda ga wannan lokaci da rasheed yayi arba da gawar abbunshi da umma yasa wa ranshi kowa ma ya mutu kawai da wannan ya yi kuruciyar shi har zuwa girma.

Da kyar aka bambare shi daga jikinsu aka kwashe su gaba daya har ummie zuwa asibiti.Bayan gwaje gwaje aka dawor dasu gida aka musu sutura kana aka mika su gidan su na gaskiya.Ummie kuwa admitting nata akayi saboda har lokacin bata farfado daga doguwar sumar da tayi ba..

Lokacinda ummie ta gama takaba ne ta nemi komawa kasarsu,kukan munafurci mama ta saka tana fadin.”yanxu shikenan dan kasa ya rufe idanun larai da ahmadu sai in kasa rike zuriyarsu?”. Babu inda zaki yannan anan zamu zauna.

Rikicewa ummie tayi ita dole sai ta tafi,ganin rarrashi bazaiyi amfani ba yasa mama fito mata a mutum cikin zare ido tace. Kifi ruwa tafiya amma ki sani babu inda zakije da wannan yaro mai jajayen kunnuwan kuma ko sisi bazaki samu ba cikin gadon ahmadu,saidai ki tafi yadda kika zo domin rasheed dai mune dolensa ba dangin uwarshi ba.Sosai ta sille ummie soso da sabulu.

Ba karamin kaduwa ummie tayi ba da jin kalaman mama, duk da cewa ta san halinta dama, amma a ganinta barin rasheed a hannun wadannan azzulaman shine mugun abu da zata aikata a rayuwarta ta kasa yafewa kanta.

Ummie tayi alwashin kota halin kaka saita bar gidan tare da rasheed da kuma dukiyar sa tunda ubanshi ne yayi wahalar tarawa ba wani ba.Dole ne tayi iya kokarin ganin ta tsarewa matawalle dukkan abunda ya bari a wurinta rasa mijinta shi ya fi tabata fiye da dukiyar sa, inda ace ta sadaukar da dukkan abunda suka mallaka akan Ahmad da umma su dawo tabbas zata sadaukar,saidai ina alkawarin Allah ba ya fasawa saidai ta tunkari abunda yake gabanta yanzu.nan ta hau kulle kullen way out, yayinda a nasu bangaren suma suke ta wani shirin da sunga ummie zata basu ciwon kai ba yadda sukayi tunani ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button