AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kwana biyu umaru ya shigo bangaren ummie ya sa me ta zaune ta rabka uban tagumi tunanin yan uwanta da kewansu ke damunta, dama matawalle ke kira mata su ta landline din wani abokinsa dake can morocco kasancewar lokacin wayar tafi da gidanka bai shigo sosai ba, gashi kuma bata san numban abokin nashi ba.

Dan kallonta yayi suna hada ido taga ya koma mata sak matawallenta,dan gyara zaman abunda ke kasan harshensa yayi kana kai tsaye yace. “Batool ina son muyi aure da ke domin mu rike rasheed da kuma abunda yaya ya bari.Duk yadda ummie taso masa musu kasawa tayi bata san lokacin da bakinta ya furta ba sai jin sautin kawai tayi tana mai cewa to na amince.

Da haka akayi auren umaru da ummie wadda take mishi biyayya tamkar ranta ayayinda rasheed ya fahimci halin da ake ciki ba karamin kaduwa yayi ba,har saida yayi jinya tamkar zai mutu Allah yasa yana da tsawon kwana, a haka suka kaura suka koma sabon gidan da abbun rasheed ya gina suna gab da komawa ya rasu.

Daga lokacin rasheed ya dena yiwa ummie magana duk abunda yake son yi shi zai wa kansa, kozata kwana tana mishi magana bazai tanka mata ba,kana bazai matsa daga wurin ba.Shi a zatonshi d gangan tayi auren kamarma da hadin bakinta a mutuwar abbunshi tunda bai wani jima da rasuwa ba tayi aurenta ta manta dashi.

Wata rana wata yar matashiyar mata ta kawo yaro dan kimanin shekara biyu da haihuwa ta direwa alaji umaru a gabanshi da fadin “ga danka nan na dawor maka, kaci gaba da kula da shi” ashe danshi ne ciki ya dirka wa wata budurwar shi ta haifi adeel, haka ya tilastawa ummie rikeshi,wanda har gobe adeel yake ganin ummie a matsayin itace uwarshi.

Bayan wata daya da tarewarsu wani safiya aka wayi gari mama bata fito ba, koda aka shiga aka duba ashe kwana sun kare ta rasu itama, ta tafi inda dukkan mai rai dole sai ya je, ta tafi ta taradda abunda ta shuka.
Allah ya kare mana imaninmu,tayi fafutuka ta hanyar sabawa mahalliccinmu domin kawai ta mallaki dukiyar wani ,ashe itama kwanakin kadan gareta.

Koda aka kaita asibiti dan tabbatar da shin ta mutu ne da gaske? nan likitoci suka tabbatar da ta mutu sanadiyar bugawar zuciya.

Ummie tana share hawaye dake shatata saman fuskar ta tace “rasheed nawa baiyi bincike ba baisan komai ba,kawai ya hau gaba dani,baisan cewa ba abun da nafi so da kauna a duniyar nan sama dashi ba,baisan yadda nake kwana da bakin cikin rashin kulani da yake yiba, zuwa lokacin kafafun rasheed sun gaza daukarsa zaman yan bori yayi bakin kitchen din, saidai duk yadda yaso yayi ko digon hawaye ne hakan ya faskara.

Ummie ta ci gaba da fadin “ya dauka nayi aurennan da son raina ne, baisan auren kariya nayi ba,nayi ne dan in kare shi aysha, ya dauka ina cikin farin ciki ne, baisan duk dare sai nayi artabu da azzalumin kanin mahaifinshi ba.Tinda na gano da asiri ya aure ni na fara neman dabarun da zan daura rasheed akan dukiyar mahaifinshi na tura shi makatantu masu kyau na addini da na boko,yayi karatu mai zurfi da inganci,inda a hankali na rika amfani da buba wurin nuna mishi dukiyar nan nashi ne kuma alhamdulillah nayi nasarar hakan saidai…Kuka ne yaci karfinta tashi suheer tayi tazo ta rungumeta suka cigaba da kuka mai sauti aka rasa mai lallashin wani.zuwa can ummie tace, saidai na rasa yan uwana bansan ta yadda zan same su ba,na manta komai dangane dasu,idan na yawaita tunaninsu sai inji kamar kaina zai pashe don dole nake hakura.

Rumtse ido rasheed yayi yana jin zuciyar shi na gudu fiye da kima, da kyar yayi karfin halin mikewa don kukansu yana barazana ga lafiyar dodon kunnenshi da kuma zuciyar shi.

Steps bibbiyu yake hadawa har ya isa bangarenshi zama yayi kan bed side ya dafe kanshi, tsawon mintuna yana a haka, karar wayar shi ce ta dawor dashi hayyacinsa.Dagawa yayi ya kara a kunne ba tare da ya duba mai kiran ba.

A hankali ya furta ” oh my God, i just forgot james,”…Dan shafa fatar goshinsa yayi yana tattatara shi wuri daya yace, “ok two minute am on my way”.

Tashi yayi yana jin kamar iska zai kadashi tsabar rashin karfin jiki bathroom ya shige kimanin minti talatin ya fito daure da bathrobe da karamin towel a hannunshi.

A tsanake ya shirya cikin wani wando mai dan fadi kalar baki da wasu jajayen layi bibbiyu a gefe da gefen wandon, kana yasa rigar wandon shima mai dan fadi baki a gaban rigar an rubuta SPORT da jan kala, kana ya gyara kyakyawan sumar kanshi hadi da zura wasu slippers samfurin gucci masu dan karen taushi. Wani jakar adidas ya daga daga kan gadonshi ya zuge zip din kana ya goyashi a bayanshi ya zari car keys da phones nashi ya fita yana ta zuba kamshi, saidai ko na sakwan daya tunanin ummie da suheer bai bar ransa ba, yana fitowa direba ya taso da sauri, cilla masa makullin yayi ya shige bayan motar bayan driver ya bude masa, a takaice yace “airport” daga haka drivern ya dauki hanyan airport ba tare da ya ce komai ba.

Ammi ne zaune a reception na asibiti ita da fareeda wacce ke zaune shiru tana ta wasa da bakin hijabinta.Tun daren jiya likita ya kirata akan cewa babban dr da yace zai hadasu ya iso tazo yau din, bayan sunzo anyi duk wani cuku cuku an tura file nasu office nashi yanzu jiran kira kawai suke yi.

Gaban ammi ne ya fadi lokacin da aka kira sunan fareeda alamar su shiga, cikin sanyi ta kama hannun fareeda suka nufi office din,daga kai fareeda tayi tana kallon wani dan katako mai walkiya wanda aka kafe shi saman kofar office din an rubuta DR.A.S.M, da manyan haruffa. Ba abunda office din keyi sai tashin kamshi mai dadin gaske yana zaune bisa office chair dinshi sanye cikin wasu bakaken suit wuyanshi daure da jan necktie farine sol kyakyawan gaske, duk da girman shekarun dake tattare dashi hakan bazai hana ka ganin tsantsar kyawun dake gareshi ba, dan gayu ne na fitar hankali.akalla zai iya kaiwa shekaru 48 zuwa hamsin a duniya.

Kusan minti biyu da zaman su ammi amma kanshi yana duke kan file na fareeda da ya ke dubawa, gyara zaman gilashin fuskar shi yayi bayan ya dago ya kalli su ammi da fara’a kamar yadda ya saba cikin muryar shi mai dadin amo yace. hajiya barka da zuw…..Maganar shine ya katse bayan sun hada ido da ammi kallonta kawai yake yi without blinking, da kyar yayi gathering courage yana nuna ta da biron hannunshi yace “youuuuu!”…..

????????AUREN~FANSA????????

Page 71 / 72

Yace “you,…Kamar ke ko?, kallonshi kawai ammi ke yi yayinda take mamakin a ina ya santa, ita dai bata taba ganin mutum mai kama dashi ba,gashi kuma babban mutum,sai taji wani iri a jikinta, dan this is the first time da wani daban ya nuna ya santa a tsawon rayuwarta,take taji hawaye yana kokarin cika mata idanu.

Cikin nutsuwa ta nuna kanta tace “ni kuma? a ina ka sanni? maybe dai kama ce.”

Zare gilashin idonsa yayi jin sautin muryarta tabbas itace but where is the… Tunaninshi ne ya katse jin ta kuma cewa “ga marar lafyar da zaka duba nan”. Kana ta daure fuska don ita a tunaninta irin yan iskan likitocin nan ne.

Saisaita nutsuwarshi yayi yana kallon fareeda da murmushi saman fuskar shi yace ” My friend ya akayi? me ke damunki?, shiru fareeda tayi tana ta wasa da yatsun hannunta, juya kanshi yayi yana kallon ammi yace “zamu daura ta kan medication amma kuna bukatan zage dantse wurin ganin ta sha magungunan yadda ya kamata da kuma debe mata kewa don mu samu nasara akan cutar, and karku manta cuta da sauki duk na Allah ne, shike daura wa bawa kuma shike yaye masa, mu namu bada magani ne da shawarwari.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button