AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi ummie tayi tace “koma menene dalilinshi na yin hakan na san khairan ne insha Allah…..Misalin karfe shida na yamma komai na cikin garden din ta gefen swiming pool ya dau decoration mai shegen kyau da daukar hankali, party ne da gawurtattun mutane suka shirya shi so dole wurin ya zama very unique, Duk inda ka kalla walkiya ne ke juyawa saboda anyi anfani da fitulu masu kala kala..
Turo kofar palon akayi wata daga cikin maid na gidan ta shigo da sallama hannunta rike da wani jaka akwati mai dan girma kana wata yar matashiyar yarinya na biye da ita,amsa sallamar suheer tayi hadi da mikewa,maid din ta sunkuyar da kai tace “maam yallabai ne ya turo mu da wannan ita zata miki make up wannan kuma shine kayan da zakiyi amfani dasu for party.
A fusace suheer ta nuna musu kofa tace “i don’t want it,ku fice min daga daki.” sumi sumi suka fita ganin yadda ta hade rai ta kama kofar ta rufe kafun ta cire hannunta aka turo kofar da karfin da ya sa ta matsa da sauri. Rasheed ne ya shigo shirye tsaf cikin wasu shegun suit da kallo daya zaka musu ka fahimci irin kudin da suka lamushe,bakake ne kirin masu matukar walkiya,yayinda rigar ciki ya kasance ja.Fuskarshi yasha gyara sai daukan ido yake yi,kana yana ta zuba kamshin turaren oud kareemat da kuma oud wood,fuskar nan tamau ba alamar annuri, da hannu yayiwa maid din alama ta ajiye akwatin,ajewa tayi suka fita.
Matsota yayi tana matsawa har zuwa jikin bango kana ya tokare hannunshi daya da bangon,zuciyarta ne ya tsananta bugu, yace “ina son ki shirya cikin 30minutes ki sauko inba haka ba….katse shi tayi ta hanyar fadin “inba haka ba me mr rasheed matawalle, na fada maka wannan auren kwantiragi ne, so babu yadda za’ayi in barka kayi ta wulakanta ni nima ina da yanci don haka zan kara maimaita maka cewa bazan je wani prlartyn da ka shirya b… Shiru tayi jin yadda ya matse bakinta da hannunshi, yace “baki isa ki bani kunya a gaban abokai na ba,karya kike kuma wllh wllh ki ketara lokacin da na baki kiga ikon Allah” sannan contarct da kike magana akai kuma only me and you muka san dashi,a idanun duniya da ma iyayenki da nawa ke din halastacciyar matar rasheed ce,shiyasa zanyi fulfilling wannan duty din a gaban dubban jama’a yau, ma’ana husband duty, ya sake ta ya fita….Buba ya samu downstairs ya mishi magana kusan minti biyu sannan ya fita daga main house din gaba daya yana mamakin taurin kai irin na yarinyar, a ranshi yace “wannan idan ta samu wani dan dama kadan ba karamar FEMINIST zata zama ba a nigeriya da anyi magana bakinta cakwai cakwai wai ina da yanci nima, wani dogon tsaki yaja kana ya wuce bangaren bakinshi..
Ummie ne ta shigo dakin hannunta dauke da wani dan box mai fadi, bayan buba yaje ya mata wani bayanin da ban san me suka ce ba, dafa kafadar suheer tayi wacca ke zaune ta zuba uban tagumi, cikin sanyin murya ummie ta fara magana, “bansan me zan ce miki ba,ban kuma san ta inda zan fara ba,amma na tabbata kedin diya ce mai tarbiya,tunda kika shigo rayuwar dana kika fara chanza min shi,he is totally change because of you Aysha, wai yau ni rasheed ya roka in masa abu,koda dai ba kai tsaye yazo ba amma naji dadi,bayan shekaru ashirin yau ni rasheed ya yiwa magana,ya roke ni ta hanyar buba da inxo in sa ki ki fito partyn nan, plsss aysha alfarman farin cikin da na ke ciki yau kimin alfarman fita wurin taron plssss….Ummie na zaune har aka gama tsarawa suheer kwalliyar da ya kawata mata fuska kamar ka saceta ka gudu, ita da kanta kallon kanta take yi a mirror,saidai ranta ba dadi ko kadan takaici ne fal ranta amma tasan bazata iya yiwa ummie musu ba.wani dogon gown baki mai walkiya aka fitar cikin akwatin iya haduwa rigar ta hadu ci kadai rawa yake yana walkiya,lokacinda suheer ta saka rigar ba abunda ummie ke ambata sai Fatabarakhallahu ahsanul khaliqeen,rigar yayi masifar zama a jikinta tamkar a jikinnata aka dinka shi, ya kamata daga sama har zuwa kan guiwa yayinda kasan yake bude sosai,yana dauke da doguwar hannu kana wuyanshi rufaffene, jan head aka daura mata mai dauke da wasu jerin stones a gaban kusan layi uku gashinta daya sha gyara ya sauko har kan bayanta,kitse jelar gashin mai make up din tayi karshen jelar ta daure shi da wani jan band mai kama da rose flower. ya salam komin sanin da kayiwa suheer dole ta bace maka a lokacin, wani dogon takalma shima baki mai walwali aka fitar daga cikin jakar tana yamutsa fuska tasa kasancewar tana da tsayi bata cika mu’amala da heel shoes ba.Tasowa ummie tayi cikin farin ciki ta bude box din da ta shigo dashi wani hadadden sarkar gold ta fitar mai fadin gaske ta makala mata a wuya kana ta saka mata dan kunnensu hadi da zobuna guda biyu take suheer ta kara daukan wani walkiya,rungumeta ummie tayi tana jin wani irin dadi a ranta……
Lokacinda suka iso wurin taron wuri yayi wuri duk inda ka wurga idanunka mutane ne hadaddun yan mata da samari masu ji da kansu da kuma naira kowa yana jin kanshi a wurin,kowa yana rike da abun sha cikin irin kofunan glass doggin nan,wani irin ajiyar zuciya rasheed ya sauke lokacinda ya hango ta cikin yan matan da suka dauko ta, ta zama tamkar zara a cikin taurari, da hanzari ya mike ganin yadda gaba daya idanun jama’ar wurin ya koma kanta, ga wani irin juyawa da jikinta keyi duk wani motsin da tayi,… Matsowa yayi kusa da su kana ya mikawa suheer hannunshi cikin murya kasa kasa da murmushin gulma a fuskar shi yace “darling wife karki yadda ki bani kunya”,
Mika mishi hannunta tayi badon taso hakan ba,take wurin ya dau tapi rap rap rap, cikin takun kasaita ya juyo da ita gaban jama’a hadi da cewa ladies and gentlemen wannan ita ce mrs rasheed matawalle so cheers for my bride, nan yan mata da samari suka daga kofunansu hadi da furta cheeers.
Cikin kwarewa marar hayaniya aka ci gaba da gudanar da taron har misalin goma da rabi kyautuka kam suheer tasha su na fitar hankali abu na karshe da za’a gudanar shine yanka cake,wani katon cake aka turo zuwa gabansu mai hawa biyu kalan pink and white dauke yake da hoton ango da amarya anyi rubutu mai kyau a jiki.
Firr suheer taki tashi domin yanka cake din sunkuyar da kai yayi yana mata magana kasa kasa amma taki sauraranshi, daga karshe mikewa yayi kamar mai fita kawai tajita anyi sama da ita kokarin kwace kanta ta fara amma riko mai kyau ya mata a gaban cake din ya ajiyeta kana ya manna ta da gefen cikinsa yana jin kamshinta kamar zai fasa masa kwanya,tapi yan wurin suka dinga yi dan sosai salon ya kayatar, kamo hannunta yayi da nashi ya hada gami da daukan wani pink knife dan karami a tare suka yanka cake din ba abunda ke tashi wurin sai tafin mutane ji kake rap rap rap, daukan yankan yayi hadi da nufar bakinta ganin da gaske bazata bude bakin ba ga mutane duk sun zuba musu ido yasa shi chukling dinta a gefen ciki, aiko ba shiri ta bude bakin baiyi wata wata ba ya tura mata da iya karfinta ta turo cake din da nufin tofarwa rasheed da baida zabi kawai ya hade bakinsu wuri daya ihu jama’an dake wurin suka dauka,bashi ya sake ta ba saida ya tabbatar da ta hadiye cake din gaba daya har ma da yawunshi kafun ya koma baya yana sauke wahalallen numfashi, wani irin takaicine ya gauraye zuciyar suheer jin yadda mutane ke ta ihu alamar abun ya basu sweet ga kuma hasken cameras na waya ana ta daukarsu…..