AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan sun gama dinner fareeda tasha magungunanta bacci ya dauke ta dan drugs din suna sata bacci sosai, nan suheer ta zauna ta labarta wa ammi irin wahalar da rasheed ya bata from day one..Sai dai ta boye abunda ya faru bayan kare party, tace “ammi ni bazan koma ba kuma, mutumin da ya min irin haka a gaban mutanen party Allah kadai yadan abunda zai iya min nan gaba, ta fada tana turo baki gaba…

Kwance yake kan doguwar kujera a downstair idanunsa a lumshe kamar mai bacci amma a zahiri ba baccin yake ba, ummie ne ta fito daga kitchen rike da bowl mai dauke da fruit salad ta iso kusa dashi, a hankali tace “son,”. Bude idanunshi da sukayi jawur yayi ya daura su akan ummie saida ta dan zabura ta ajiye bowl din da sauri ta matso kusa dashi,kanshi ta daga ta zauna a wurin kana ta mayar da kan nashi kan cinyarta, tana shafa lallausan sumar shi da ya taru kamar baisan hanyan barbing saloon ba,ga wani irin hucin zazzabin da ya ke tashi daga jikinsa amma yaki a kaishi asibiti cikin nutsuwa tace “son ka daure kaci wani abu sai muje asibiti su dubaka, kaga dr jameel yace kana bukatan asibiti,”.

Cikin shagwaban da ban san rasheed dashi ba yace “a’a ummie ni dai kawai ki barni yazo nan yamin duk abunda zaiyi, bazanje asibiti ba,…Dan shiru tayi tana ci gaba da shafa kanshi tace “to yanzu ya kake son ayi? yace cikin rauni da damuwa mai tsanani “kina gani fa ummie,ta tafi kuma ta ce bazata kara zama dani ba, kuma kuma sai yayi shiru, ummie tana dan murmushi bata son dariyarta ya kubce tace “kuma me?”

Wani abu ya hadiye da kyar zuciyar shi na harbawa yace “kuma tace ban dace da ita ba wai ni mugu ne ummie,kuma wurin dan kauyen can zata koma suyi aurensu, ya fada yana nuna kofa kamar habeeb yana wurin, sai kuma ya mike da sauri yace “wllh ummie da gaske take kuma in sunyi aure haifa masa yaya masu kama da ita zatayi su yi ta farin ciki, kyabe fuska yayi yaci gaba da magana “Wllh Allah bazan barshi ba, sai na sare masa kafafu biyu” ya fada yana kokarin tashi,

Riko hannunshi ummie tayi da shike baida karfi take ya koma ya zauna dabas dariya ne yake cin ta a ciki sosai amma ta dake tana mamakin yaushe rasheed ya zama haka. daure fuska tayi tace “son ni banga abun damuwa dan ta tafi ba, ina ce ka aurota ne dama dan ka dau fansar abunda ta sa a maka, kuma ka dauka ni nan shaida ce na irin azabar da ka gana mata daga shigowarta gidannan,” da mugun mamaki ya juyo yana kallonta, gira ta daga masa tace “yess” buba ya sanar min komai,..Kodai bayan fansa akwai wani abu kuma,” shiru yayi,tace “to tunda ba komai i see no reason da zaka takurawa kanka dan matar kwantiraginka ta tafi, kawai ka rubuta mata takardar sakinta ka tura mata, tana da wadda take so dama kuma shima yana sonta kaga kawai sai tayi aurenta na soyayya ta haifa masa yaya masu kama da ita. Gingirigim rasheed yaji a kansa baisan lokacin da ya mike ba yace “na rantse da Allah banga wani banza kazamin da zai ketara iyakar dana ketara ba.galala ummie tayi da baki tana kallonsa kafun tayi karfin halin cewa, “ikon Allah son ko dai kana sonta ne dama can?” shiru yayi na dan lokaci yana juya kalmar ummie kodai kana sonta ne dama can? ba tare da ya bata amsa ba Ya juya da sasaarfa yana hada steps biyu uku ya haura sama. Dariya ummie ta sake tayi mai isarta, tun bayan da buba ya bata labarin abunda ya faru tasha alwashin saita kwato wa suheer yancinta ganin alamar dan nata ya fada da yawa.

Tsawon sati uku kenan yanzu da tafiyar suheer, zuwa lokacin rasheed ya gama fita a hayyacinsa, idan ka ganshi bazaka ce shine wannan dan gayu mai girman kan tsiyar ba gaba daya fuskarsa ya tara kasumba yayi wani wujiga wujiga dashi, yana iya kokarinsa na ganin bai bayyana damuwa saman fuskar saba tun randa ummie ta tambayesa kodai yanason suheer ne, amma a hankali damuwar zuciyar sa ke cinye sa har yayi nasarar kwantar dashi, sosai ummie take tausaya masa gashi yaki a kaisa asibiti saida family dr nasu yazo ya masa yan dabaru a gida, ba ya yadda yaci komai sai uban drip da ake narka masa kullum, yau dai ummie tayi alkawarin zuwa gidansu suheer domin jikin rasheed yana kara tsananta.

Ammi na tsaye kitchen tana girka lunch, the house was so silent baka jin motsin komai kamar ba mutane a ciki, karar wayarta da taji a palo ne yasa ta wanke hannunta hadi da gogewa da dan towel dake rataye kana ta fito, dan murmushi tayi ganin mai kiran nata….Da barkwanci irin wadda ya saba tun tasowar sa har girma ammar yace “surkata barka da rana” da fara’a ammi tace “barka dai surkina” bayan sun gaisa sun dan taba hira akan yanayin sauyin da ake samu akan jikin fareeda, ya nemi da ta ba fareedar waya dan yayi ta kiranta bata dauka,…Bayan ammi ta kaima ta wayar suna zaune ita da suheer kamar masu hira amma ba hiran suke ba, kowa da abunda ya dame ta,kira ya kuma yi wannan karon video call yayi, bayan fareeda ta amsa ganin video call ne yasa ta hade fuska tamau kamar bata taba dariya ba, cikin sakin fuska ammar yace “a’a giwa ta fushi ake dani ne, haba danyi dariya mana kar in kasa bacci yau ganin fuskar ki ba wargi, dan leko fuska suheer tayi tana mamakin wa ye yar uwarta ta samu haka.

Daga mata hannu yayi , hadi da cewa “hii” itama ta daga mishi tace “hello” yace “rabin jiki, i guest”! suheer tana murmushi tace ka canka daidai, nan hira ya barke a tsakaninsu tamkar sun jima da sanin juna, yawancin hiran yana rokonta ne akan ta rokar masa fareeda ta soshi koda rabin wanda yake mata ne,…Juyawa suheer tayi baki har kunne tana kallon fareeda bayan sun katse kiran tace “woww sweetheart a ina kika samu wannan hadadden sugar dadyn”?

Bata rai fareeda tayi tace “me ya sa baki tambayesa ba,kin sake baki yen yen yen sai zuba kike kamar kurna bayan da aure a kanki, dumm suheer taji ita tunda ta dawo ta wani manta da batun aure akanta sai yanzu da fareeda tayi maganar, basarwa tayi ta kuma tambayarta, fareeda tace “shine dr da yake dubani, kuma ina ga suna dangi da ammi dan sun san juna wai tun muna yara, suheer tace “you’re so lucky rabin jiki, haka ake so namiji ya ringa rawan jiki akan mace wallahi idan kin aure shi zaki huta ke baki ga yadda yake sonki ba, kar ki bari ya kubce miki maganar gaskiya kenan dan ta ko ina ya hadu,” turo baki fareeda tayi tace “ke bakiga tsoho ne ba”.

Wani irin dariya suheer tayi gami da fadin “dallah can ke yaushe zaki waye ne, irinshi ake yayi ai yanzu, kawai ki mana wufff dashi, Allah irinsu akwai bada kulawa, yana kallonki a matsayin yarinya duk tsiyan da kika tsula a yarinta zai dauka……Bayan kwana biyu ummie ta shirya don zuwa bawa iyayen suheer hakuri ganin yadda rasheed nata al’amarinshi yake kara gaba,… Tunda buba ya sauke ta kofar gidan take jin faduwar gaba sosai, haka ta daure ta shiga cikin gidan,saidai kafun ta iso entrance na shiga jinta take tamkar wacce tayi gudu tsabar yadda numfashinta yake sama sama,a haka ta iso ta kwankwasa kofar gami da tsayawa gefe tana ajiyan numfashi,…Suheer na kwance bisa kujera wani irin kasala yake damunta kwana biyu amma na yau yafi yawa fareeda na kama mata gashinta da ya dade a kunce kusan tunda ta dawo gidan a kunce yake,…Jin bugun kofa yasa ta sakin kan ta je ta bude hadi da matsawa gefe ganin wata hadaddiyar mata,shigowa tayi cikin palon hadi da sallama da sauri suheer ta mike jin muryar ummie Hakan yayi daidai da fitowar ammi daga daki cirko cirko duk sukayi a wurin gaba dayansu zuciyar su na dukan tara tara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button