AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin wani irin rawar jiki ummie ta nuna ammi tace ” Aysha!ko ba ita bace”?.

Girgiza kai ammi tayi hawaye yana kawowa idanunta jin murya sak irin na babanta, gashi matar ta kirata da sunan mamanta, ammi tayi karfin halin cewa ba ita bace ” jin muryar ammi ya kara rikita ummie ta kara bin ammin da kallo, idanunta ne ya sauka kan dan yatsan ammi na tsakiya wadda ke dauke da zobe, bata san ya akayi ba kawai sai ganinta tayi a gabanta ta kamo hannunta da sauri tana dubawa, wani irin kuka ta saki hadi da rungume ammi tana fadin ke jini na ce ,ke jini na ce, koba Aysha bace to jininta ne wannan zoben daga ni sai yayana muka mallake shi ke jinin yayace,sosai ammi ma ta pashe da kuka tana kara rungume ummie jin abunda take fada.

…….Bayan komai ya lafa ne ammi tana share hawaye ta bawa ummie labarin duk abunda ya faru bayan sun fito nemanta ita da babanta da mamanta,daga farko har karshe, …Nan ummie ma ta ba ammi labarin komai na abunda ya faru, ta kare da cewa yanxu nan adama ce ta girma harta tara zuriya?Allahu Akbar. Ashe rasheed da suheer yan uwane Allah mai iko…Tsabar farin ciki ummie manta abunda ya kawota gidan tayi, nan ta dage sai ammi ta tattara kayanta su tafi gidanta amma ammi taki a cewarta sai su hafsa sun dawo sunji irin abun farin cikin da ya sameta, ba don ummie ta so ba haka ta koma gida har wurin sha daya da rabi na dare tamkar kar su rabu, mamakin suheer da fareeda yaki karewa…

Washe gari bayan anyi sallan isha suheer ta fita da niyyan siyan bread a shagon anguwansu, tun safe take kwadayin cin bread haka kawai, ta ishi ammi hakan yasa ta bata kudi taje ta siya dan babu bredi a gidan, wata bakar mota ta gani pake kofar gidan, cike da mamaki tayiwa motar kallo daya ta dauke kai dan yayi kusa da kofar gida koma waye ya ajiye mota a wurin to da gangan yayi hakan, kafun ta gama tunani taga anfito daga driver seat an damki hannunta, wani irin tsorata tayi ta bude baki zata yi ihu ya rike bakinta hadi da bude backseat ya sata ciki shima ya shiga, kamshin da taji cikin motar yasa ta gane waye, cikin sanyin murya bayan ya sake mata baki yace “waya baki izinin fita daga gida na,”?

Jin yanayin yadda yayi maganar yasa suheer dagowa tana kallonshi, ya salam, muryar dai na shi ne,amma kamannin is totally different,this is someone else not rasheed, zuciyarta ya fada mata, muryar shi ne ya kara dawor da ita hayyacinta, da dan tsawa yace “ba magana nake miki ba”? murguda baki tayi tace “dan na gama aurenka, bazan kara zama da kai ba, kai din mugu ne, wanda baisan darajar dan adam ba, ai a kwantiraginmu bamuyi da kai zaka…..Sai kuma tayi shiru, yace “rumtse idanu yayi yana jin zafin kalamanta suna karasa ruguza sauran karsashin da ya ke dashi, janyo ta yayi yace “aheeen go on, bamuyi dake zanyi me ba,?…Shiru tayi batace komai ba, hakan yasa ya karasa jawota ya rungumeta tsam a kirjinsa kana ya kwantar da kai kan headrest gami da rufe idanunsa rufff yana jin faduwar gabansa yana karuwa, mutsu mutsu ta fara amma ba rikon wasa yayi mata ba,hakan yasa ta kwantar da kanta itama hadi da lumshe idanu tana jin yadda bugun kirjinsa ke tsananta kamar zai fito waje. A gefe daya kuma kamshin da ke tashi a jikinsa ne ya dau hankalinta, kara shige masa tayi ba tare da tasan tayi hakan ba, hannu yakai cikin gyallen abayar dake kanta yana shafa lallausan gashinta da fareeda tayiwa kananan kalabar cikin nutsuwa kana bugun kirjinsa da kuma faduwar gabansa suna kara yawa.cikin cool voice yace “Ayshhha! ni ba muvu bane kamar yadda kike fada, pllsss ki…..Zaro ido yayi ganin ta tashi da sauri tana toshe baki da hanci,…Kafun ya gama fahimtar abunda ke faruwa suheer ta fara kelaya masa amai a jikinsa ba kakkautawa gaba daya jikinsa ya baci da amanta daga sama har kasa, tun tana kakari abu yana fita har ya zama sai kakarin kawai ba abunda yake fita, take jikinta ya dau rawa, rikota yayi cikin rashin sanin abunyi sai aikin sorry da yake mata, da kyar ta samu kakarin aman ya tsaya, da azama ya rikota ganin zata fadi daga zaune ya daura kanta saman shoulder dinsa kana yana shafa bayanta a hankali, gaba daya motar ya dau karnin amai rasheed kuwa ba inda aman bai taba ba a jikinsa, cikin wahalalliyar murya mai kama da shagwaba tace “bread zanci, ni bread nake son ci”.

With much suprise yace “bread kuma at this hour”?

Kuka ta sake hadi da gyada masa kai…

????????AUREN~FANSA????????

         BY

UMMU FADEELA

TYPING…

PAGE 77 / 78.

Duk da irin tsabta da kamshi na rasheed haka ya fita jikinsa sai karnin amai yake ya tafi nemo biredi ganin irin kukan da take wai ita biredi zata ci yanxu,…Dubu dubu sababbi dal guda biyat ya zaro a aljihunsa ya mikawa mai shagon yana yamutsa fuska yace bread da ruwan gora zaka bani. Jiki na rawa mai kantin ya sa masa bread kusan leda hudu a babbar leda kana ya jawo katon na ruwan faro yana tura masa, da hannu rasheed ya masa nuni da guda daya ya isa, zaro gora daya yayi ya mika masa yana fadin “yallabai kudin ai sunyi yawa”.Hannu rasheed ya daga masa a dakile yace “ka rike sauran”.

Taimaka mata yayi bayan ya dawo ta wanke fuskar ta da ruwan da ya zo dashi kana ya rike hannunta daya hannun kuma yana rike da ledan biredi, duk yadda suheer ta so tai masa musu kasawa tayi dan jikinta ba karfi, har bakin kofa ya kaita sannan ya sake ta yace “kodai muje asibiti ne wife? naga jikin ki ba karfi, dama baki da lafiya ne,?.

Harara ta watsa masa tace “I am not your wife, wanda zai kirani wife yana zuwa bada jimawa ba, kuma nasan ka sanshi, i mean kasan waye shi, yafi ka da komai and shi ba mugu bane, tuni idanun rasheed ya kada yayi jawur, bai san lokacin da ya fizgo ta ba, yana kallonta da jajayen idanunshi strictly yace “kika kara kira min wani wawa da aure na a kanki sai ranki ya baci, ba tare da shakka ba suheer tace “wani auren? kace dai da kwantiraginka a kaina, kuma shima takardar saki na ke jira kuma bazan taba yaf…..Gammm ya rungumeta a kirjinsa zuciyar sa na bugawa yayinda idanunsa suke kara sauya kamanni,shiru suheer tayi a jikinsa harda lumshe idanu, bayan wani lokaci ya sake ta ba tare da ya yarda sun hada idanu ba ya juya ya shige motar sa ya bata wuta, kwafa suheer tayi ta rarumi ledan biredinta ta wuce cikin gida tana gunguni…

Bayan kwana biyu, sosai gidan ya kacame da soye soye da kuma gyare gyare, tunda hafsa ta sanar da ammi cikin sati mai zuwa zasu dawo domin jikin lamido ya warke ammi ta rasa inda zata tsaya dan dadi, a bangaren fareeda da suheer ma hakan take dan ma wani irin ciwon jiki da yakr damun suheer yana dan hanata sakewa amma duk da haka sosai take karfin halin aikace aikace, farin ciki suke yi mara misali, kusan kullum sai ummie tazo gidan anan suke wuni ji take kamar ta mayar da ammi cikinta, har ta gama musu planing daga lamido ya dawo zasu je morroco ko Allah zaisa a samu wasu a dangi.

Ranar asabar da misalin karfe bakwai na dare jirgin su lamido ya yi landing a aminu kano international airport, a hankali passengers suka fara saukowa lamido na gaba hafsa tana biye dashi a baya, tana mamakin sunba india da misalin sha daya na dare gashi sun iso nigeria karfe bakwai na dare, kuma duk asabar dinne , Allahu akbar Allah daya gari bambam.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button