AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kwana biyu hasken amarci da rahamar aure ya bayyana a fuskokin lamido da ammi,tun ammi najin kunya har ta ware abunta, ba karamin kulawa yake bata ba a zahiri da badini, suma sauran ganin abun suke normal tunda tun tasowar su haka suka gansu, bambancin kawai yanzu daki daya suke kwana. yanzu shirin auren fareeda ne a gabansu wanda aka saka bikin kusa kusa kamar yadda ango ya bukata wato sati biyu, kuma basa bukatan komai na kayan daki domin gaba daya bikin a kano za’a gama shi su wuce london da amaryarshi,dan haka ammi take ta hidima yayinda kawayenta su hajiya saratu suka fara gyara fareeda saidai duk abunda aka mata na gyara sai anyiwa suheer wadda sam bata jin dadin abubuwan da ake dirka mata bata musa musu ne kawai amma wani lokaci ko an bata zubarwa take yi.Cikin lokaci kadan suka dawo kamar wadanda aka bare a leda tsabar walkiyar da suke yi.

A bangaren rasheed kuwa yana ta kokarin ganin bai bar abunda yake zuciyar shi ya fito ba, kullum sai ya kira suheer a waya itama kullum saita fada masa sakinta take jira taje ta auri mai sonta duk sanda ta fadi masa haka wani abu yake ji ya soki kirjinsa kamar kibiya. Gashi ummie kwatakwata taki nuna kulawa akan maganar shikuma baison mata maganar balle taga kamar yana son suheer ne kamar yadda ta taba fada,a bangaren ummie kuwa sun riga da sunyi magana da ammi da kuma kawu lamido da hafsa akan sai rasheed ya horu tukunna, yadda zaisan darajarta nan gaba yadda bazai na ganin auren a matsayin na fansa ba ko na contract.

Yau ake shirin kamun fareeda, tun safe suheer ke kwance dan karfin halin ma yau kasawa tayi, gaba daya jin kasusuwanta take kamar ana kwankwatsa mata su sai juyi kawai take a kasa,sallah kawai take iya tashi tayi, ammi ne ta shigo tana mata fadan ta tashi ta ci abinci ta shirya itama dan har mutane sun fara taruwa, “tun yaushe nake binki ki tashi kici abinci amma kin kasa wai wani irin haki ne kika tsiro wa mutane dashi haka ne”? suheer tace Allah ammi bana son cin abincin kuma bana jin yunwan ma,”

Sosai ammi take fada har ya janyo hankalin anty hafsa dake wucewa ta shigo dakin,jin abinda ammi ke fada yasata matsowa kusa da suheer tace “tashi a kasan nan dota kar sanyi ya kamaki kinji, tunda bakya son abinci yanzu me kike kwadayi? a hankali tace “kilan biredi mai yanka yanka”. Tace “to yanzu kuwa zan samo miki, a ranta tana kara tabbatar da zarginta. Dogon tsaki ammi taja tace “daurewa karya gindi, ni bansan wannan salo kuma daga ina ba.

Wani yaro ne ya shigo misalin biyar da rabi na yamma,”wai ana kiran suheer” fareeda dake tsaye tana rike da karfen tap waya kare kunnenta tace “wa ke kiranta? ” yaron yace wani farin mutum ne mai farin mota kuma ana kallonshi ma tb, dariya fareeda tayi wai ana kallon shi a tb, ta fahimci rasheed ne saidai abun mamaki ko dar bata ji a zuciyarta ba, zuwa yanzu ta yadda ubangiji ya kan jarrabci bayinsa da son wani Abu, sai wannan Abu kuma ya zamo ba alkhairi ba a wajensu, amma idan sukayi hakuri suma Roki Allah zai musanya musu da wanda yafi zama alkhairi a wajensu,tana kallon yaron tace “kace masa tana zuwa”.

Kwance ta tadda ta a daki, fareeda tace “rabin jiki din Allah ki leka waje akwai sakon da aka kawo ki karbar mana plsss, dan turo baki tayi tace “kai sweetheart wallahi na gaji fa ke kije mana” zaro idanu fareeda tayi tace “kin gaji fa kika ce, to lallai akwai matsala nidai ko tsinke banga kin daga ba yau a gidan nan, ciki kunkuni ta mike tana fadin ba sai kin min gori ba ai ta zura babban hijab ta fita tana jin kamar iska zai kadata.Ta cikin tinted glass din yake hango ta, ta narka jiki abunta ga wani glowing da jikinta ke yi na musamman kamar dawisu.Cikin nutsuwa ta kariso jikin motar da ba tasan dashi ba, a hankali rasheed ya balle murfin motar yana jin bugun zuciyar shi na karuwa duk sanda ya kalleta,

Zaro idanu tayi bayan sun hada idanu, aguje ta juya zata koma cikin gida yayi azamar danko hannunta, tana turjewa tana komai amma saida yayi nasarar jefata bayan motar shima ya shiga, cikin muryar marasa lafiya yace “me kike fada min a waya jiya da dare,”ba shakka tace “takardar sakina nake jira, domin habeebi….Cak maganar ya tsaya sakamakin jin warm lips nashi kan nata, bayan wani lokaci ya zare bakin yana sauke numfashi,,bai ankara ba yaji suheer ta mishi wanka da amai mai shegen karni from head to toe, amai kawai take kwararawa kamar pampo,sosai abun ya daure masa kai,ya ma kasa taimakonta sai mamakin meke damunta yake, jingina tayi da motar tana sauke numfashi bayan aman ya lafa mata. Cikin cool voice yace “wife meke damunki ne haka,? kodai muje asibiti ne.? dagowa tayi tace “ni ba matar ka bace,ka dena kira…..Kafun ta karasa wani aman ya kuma taso mata nan ta ringa kwarara wa har karfinta ya kare.Rasheed yace “you see?baki da lafiya amma bakinki bazai yi shiru ba, ni ba matar ka bace bla bla bla bla. Ba tare da yabi ta kanta ba ya fita zuwa gaban motar ya dau bottle water ya dan goggo ge jikinsa da hankerchief kana ya shigo ya dan shashshare mata itama ya jika wani hankin dake aljihunsa ya dan share mata fuska, ita dai bata ce komai ba sai dan rawar da jikinta keyi, ya kuma komawa gaban motar ya mata key ya bar layin anguwar sanin zata iya masa tijara yasa shi dannawa motar lock. Har suka iso wani hadadden private hospital bakin suheer bai yi shiru ba dukda jikinta na rawa,…Baki kawai rasheed ya sake yana kallon likitan da ke zaune saman kujera yana murmushi,yayinda suheer kuwa kwakwalwarta ya daina aiki na wucin gadi, da kyar rasheed yayi gathering courage yace “dacta dama mace na iya samun juna biyu daga haduwa daya kawai, murmushi dactan yayi yace “congratulation man, you are a great shooter, wani gingirigim suheer taji da sauri ta mike tana kwalalo idanu waje rawar da jikinta keyi ya tsananta, tana nuna rasheed da yatsa tace “God forbid, Allah ya sauwake in haihu da kai,karya ne wallahi yayana ba naka bane,kayi nasarar sace min budurci na ta hanyar zalunci irin wadda ka kware a kai wanda nake tattala shi wa masoyina amma yaya kam kayi kadan, duk yadda zanyi sai na tabbatar da cikin nan ya shiga kwandon shara, ta juya tana hada hanya zata fita, rasheed da yayi mutuwar tsaye ya damko hannunta da sauri yana kallonta da idanunshi da sukayi jajawur a take jijiyoyin kanshi sunyi rudu rudu makoshinsa sai hawa da sauka yake, yace “wallahi am giving you my word, matukar wani abu ya samu cikina sai….Fizge hannunta tayi da karfin gaske tace, sai me?me ya rage da ban gi haddar shi ba a zaluncinka, ka dade bakayi abunda zakayi ba mr rasheed, ina mai tabbatar maka yau cikin nan bazai kwana a jikina ba insha Allah watch and see.Ta juya da gudu ta fita, da sauri ya mara mata baya saidai ko kurarta bai gani ba kamar wacce tayi layan zana,nan suka bar likita da sakakken baki.

Kamar kar suheer ta koma gida,a tsakiyar palon su ta fadi ta suma, tsabar tension da zazzabi da kuma amai din da ta ringa kelawa a cikin napep din da ya dawor da ita, da gudu yan biki sukayi kanta, nan aka ciccibeta anty hafsa da wasu mutane biyu suka wuce da ita asibiti.

Ummie na zaune palo cikin shirin ta na zuwa gidan biki, rasheed ya shigo, a firgice ta mike ganin yanayin shi tace “Son! lafiya kam meke faruwa? bai bata amsa ba sai rungume ta da yayi ya fashe da kuka, subhanallah nan ummie ta kuma rikicewa rasheed da kuka abun ya bata tsoro, da kyar yayi shiru yace “ummie wai tace saita zubar da cikin,wai bazata haihu dani ba ni azzalumi ne ummie do something ummie ina son babyn and i like her too, no i love her ummie, plsss help me karta cire cikin nan ina son abuna. Ummie da ya gama riki tata tace waye mai cikin kuma waye mai cire cikin and wa kake so din, da sauri yace ummie ayshhha, bata da lafiya na kaita asibiti ance she is pregnant shine tace sai ta cire cikin wai, wani irin farin ciki ne ya lullube ummie, amma saita boye tace “to son dama me zatayi da dan contract, ai auren soyayya ake haifa ma yaya ba auren fansa ba, ko ka manta a’a ni gaskiya banga laifinta ba, cijin hanzarin rasheed yace “no ummie i love her ina sonta sosai i love her from the very moment idanuna suka sauka akan nata, all what i do is because i love her i don’t want to loose her, plsss ummie help me, karta taba cikin nan.Wani irin hawaye ummie taji yana son zubo mata amma ta daure tace nidai ba ruwana ai lokacin da ka auro ta ba haka ka nuna mana ba a gidan nan, sake ta rasheed yayi ya nufi stairs da sauri steps uku uku yake hadawa mistakenly yayi missing step aiko wani irin juyi yayi kanshi ya bugu da karfe ya fara gangarowa wani irin ihu ummie tayi ta nufi rasheed da ke kwance wanwar a kasa jini yana fita ta bakinshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button