AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk mai rai mamaci ne, kowa da silar ajalinsa, ba shakka alaji sama’ila ya zamo silar mutuwar balki da abunda ke cikinta a dalilinsa na son zuciya. kamar wanda aka ja da magnet sai gashi a gabansu ya durkusa yasa hannu a saitin hancinta a da sauri ya cire hannun zuciyar shi na bugun tara tara, ya kuma ɗago hannun ya ɗaura saman fuskar ta ya shafa a hankali idanun suka lumshe..wani uban ihu tabawa ta kwala wadda kaf makwafta saida suka jiyota, kuka takeyi tun karfi domin kuwa balki mutum ce, yarinya ce mai hankali da biyayya sunyi zama idinna ya da kanwa ne ba kishiyoyi ba, dole ne tayi kukan rashin ta.
A ɓangare guda kuwa alaji na jingine da bangon dakin, duk hangenka baza ka gane yanayin da yake ciki ba, domin wani irin mixed expression ne fuskar sa.
Kukan da tabawa ke cigaba da zabgawa ne ya janyo hankalin mutane zuwa gidan, cikin kankanin lokaci garin goruba yaɗau zancen rasuwar balki amaryar alaji sama’ila sarkin noma, kafun wani lokaci cikin gidan da kofar gidan ya ɗinke da jama’a. wanka da sutura aka mata mutane masu dimbin yawa suka sallace ta aka kaita gidan ta na gaskiya aka barta daga daga ita sai abunda ta shuka. ( yan uwa mu kasance masu aikata alheri domin riskar alherin a kushewar mu.)
Zaman makoki a kayi har na tsawon kwanaki bakwai kafun kowa ya kama gabansa a ka ci gaba da harkoki, shikenan an rufe babin balki kuma.
Kaɗan kaɗan mutuwar ke shiga jikin alaji, duk dare baya wani bacci kirki da zaran ya rufe idanunshi sai ya ganta kwance cikin jini ta kafe shi da manya manyan idanu wasu kala, kamar kuma wanda aka rufe wa baki da salatif yaƙi faɗawa kowa koda kuwa amininnasa wato bala. cikin wattani uku da faruwar abun, amma an kwantar dashi asibiti sau huɗu, da kyar da addu’ar iyaye yasamu sauƙi . Alaji sama’ila bai ƙara bi ta kan aure ba duk kuwa da irin jarababben son ƴaƴa da yake ji a lokacin, idan yaga yaran mutane na gilmawa jiyake kamar ya sace su.
Sai bayan shekara uku curr kafun yakuma auren wata bazawara mai suna hauwa, cikin wannan shekaru dukiyar sama’ila ya ninninka sau ba adadi don ba iya goruba kawai ba har cikin birnin yola yana da wasu manya manyan gidan gona guda biyu wanda suke karkashin kulawar alaji MANGA baban twins.
Hauwa macece mai ɗan zafin zuciya sam bata barin ta kwana kana fada mata zata mayar maka,
bayan wattani kadan da auren itama sai ciki a haka dai rayuwar take tafiya har cikin ya tasa itama ya lallaɓa ta yakaita gwaji, domin zuwa wannan lokaci zuciyar shi ya riga da ya bushe saboda irin arzikinsa da yake daɗa bunkasa tamkar wutar daji. bayan yan dube duben da likitan yayi a allon kwamfutar dake gabansa, ya tabbatar wa alaji cewa ƴaƴa mata ne har biyu a cikin matar shi yana murmushi ya faɗa masa , congratulation matar ka na ɗauke da gimbiyoyi har guda biyu, watakila matar shugaban kasa ne da kuma matar babban shehin malami ya faɗa da barkwanci.
Wannan karo ba ƙaramin tsorata sama’ila yayi ba , duk da haka ya yi gathering courage ya dubi likitan yace” likita ka taimaka ka cire mata cikinnan” a tare likita da hauwa suka ɗago jin abunda yace, cikin mamaki hauwa tace” alaji ban gane hausan a cire ciki ba? ba farin ciki zaka yi ba da Allah ya baka wannan kyauta mai daraja wanda kudi baya sayeba sai kace a cire, kasan iya adadin bayin Allahn dake neman haihuwa ido rufe a cikin wnn duniya amma basu samu ba? kasan iya wadanda zasu iya sadaukar da duk abunda suka mallaka domin samun ƴaƴa amma babu? mukuma da Allah ya bamu ba tare da ko sisinmu ba irin kalar godiyar daza mu mishi knn. To wllh bazai yiwu ba banga wani ja’irin da zai cire min ciki ba Allah ne yaba ni kuma na gode masa ehe” ta karisa tana girgiza jiki irin sai dai komai ya faru ɗinnan.
Alaji dai kallonta yake with suprise, don bai ɗauka yarinyar ta iya masifa haka ba can yace ” baki isa ba dake da abunda ke cikinki duk a karkashin iko na kuke, dan haka dole ne kibi duk decision dana yanke , ya faɗa gami da matsota kamar zai doketa .” karya ne wllh baka isa ba, baka isa kasa a cire min ciki ba, da kake ikirarin cewa a karkashin ka nake, kamanta cewa ba bu biyayya ga halittace gurin saɓawa mahallici? au na manta ashe bakaje islamiyya ba domin da kasan wani abu daga cikin dokokin ubangijinka da ba za ka aikata wnn ba koda ko ace cikin shege ne balle kuma na halak. this is shame on u. ok yanzu na fahimta wato duk damuwar da kake na rashin ƴaƴa a gidanka farfaganda ce kawai to wllh Allah banga wani katon da zai……kafun ta kai aya taji ya shaƙo mata wuya da iya karfinshi, idanunshi sunyo waje bakinshi har wani kumfa yake yana “faɗin baki isaba sai an cire cikinnan’! baki isa ki haifo min sanadin bari na mulki ba, baki isa ki haifomin silar talauce wata ba. yana magana yana haki kamar wanda yayi tseren formula1
Kokawa hauwa ta shiga yi da numfashinta dan ba karamin shaka ya mata ba , da farko baiyi niyyan shiga maganar ba hasalima diramar tasu nishaɗi ya sa shi, amma ganin ana kokarin yin kisan kai a ofishin sa ne yasa likitan azamar tasowa.
Iya ƙarfinsa yasa ya fincike jannun alaji a wuyan hauwa, take ta zube nan ƙasa tana sauke numfarfashin wahala, likitan ya miƙa mata goran faro dake bisa teburinshi, aiko take ta kafa kai ta shanye shi tas. kallon alaji yayi yana yamutsa fuska yace ” zauna zamuyi magana” ba musu ya zauna domin dama jinsa yake kamar wanda ake kaɗawa gangi, dr ya kalleshi cikin bacin rai yace” how can you treated her this badly? in kaji mata ciwo fa? ko ka manta mace ce ?mace macen ma mai juna biyu, wnn bai dace da mutum mai girma da daraja kamar ka ba. abu na gaba wnn abunda kuke yi is an family issue bai kamata kuyi shi anan ba ku bari sai kunje gida , and one more important thing da na ke so kasa ni shine mu asibitinnan bama irin wnn aikin, dan haka kuyi saurin barin min office kafun insa a fitar min ku yanzunnan .tashi alaji yayi yanu na dr da yatsun shi biyu kana ya buga su suka bada sautin kat,kat, kat sannan ya juya ya fita da sassarfa .
Da sauri hauwa ta bishi saidai kafun ta iso har ya tada motar shi yayi gaba, tilas ta ta tafi inda zata samu motar da zai kaita goruba, haka ta koma gida zuciyar ta cike fal da tunanin kala kala na maganganun da alaji samaila yayi dazu, ganin wannan tunani ba mafita bane kawai ta ajeshi gefe ta fara tunanin mafita. ɗan murmushi tayi ita kadai ganin ta samo bakin zaren warware kullin.
Da wannan tunanin ta iso goruba, babur mai kafa biyu ta hau domin isowa gida. ganin motar sa a kofar gida ne ya tabbatar mata da ya dawo da jimawa, ba tare da fargabar komai ba ta kutsa kanta cikin gidan, muryar da taji ne yasata dakatawa kaɗan ta kasa kunne sosai don tabbatar da abunda take ji ba wai kunnuwa nta ke mata gizo ba, ta kara matsowa kusa kadan ta leƙa alaji ne zaune da wnn abokinnasa mai idon marasa gaskiya wato bala zaune a kan fararen kujerun roba suna magana kasa kasa.
Alaji samaila yaci gaba da magana” .yace bala kaji irin abunda ya faru knn ban tsammaci haka da ga yarinyar nan ba . sannsn gsskiya ina tsoron bata irin maganin da muka bawa balki kar in rasa ta kamar yadda na rasa balki haƙƙin zai min yawa. balki! na furta a raina, yayin da zufa ke keto min a duk hudar gashin dake jikina.
dama alaji nada hannu wurin mutuwar balki! Inna lillahi wa’inna ilahi raji’un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha. ita ce addu’ar da nayi ta maimaitawa har naji nutsuwa tazo min.