Uncategorized

MUSAYAR RUHI 11-12

 

*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

 *Page 11 & 12*

*S* akin ajiyar zuciya Hanan  tayi cikin sanyin muryarta tace Ammi babu komifa ay idan dasabo nasaba da halin yaya Hammat ” zame jikinta tayi daga na Ammi  ahankali kai tsaye bedroom tanufa bin bayanta da kallo Ammi da Ansar sukayi cikin sauri Ansar yataso yanufo Ammi cikin damuwa yace

Ammi wai yaushene zamu tafi Skul mubar qasar nan baki d’aya muhuta da zalincin Yaya Hammat ” wata irin ajiyar zuciya Ammi tasauke sabida se yanzu tama tunadacewa Sarki Jabir yasanar da ita maganar tafiyar su Hanan Skul anan kusa gakuma wannan lamarin to yaya kenan duban Ansar tayi cikin kulawa tace ” karka damu nan kusa zakutafi tunda Maimartaba yayi min maganar tun kwanaki dasuka wuce yakumace saura kadan komi yagama kammala ammafa bawaje d’aya zakuyi karatu da Hanan ba ” zaro ido Ansar yayi kafin yasakeyin magana Ammi tadakatar dashi da hannu sannan tanufi hanyar fita daga part d’in Kai tsaye part d’in Sarki Jabir tanufa takuwayi sa’a yana ciki d’ago idanunshi yayi yadubeta sannan ya’amsa sallamarta idasa shiga tayi tazauna gefanshi cikin girmamawa suka gaisa sannan tanumfasa da’alama wani nazari takeyi bai katsetaba kimanin 10 minutes sannan tafara dacewa

” Maimartaba wani babballamari ne yakawoni nikam narasa mafita sabida lamarin yacikaro da wannan babban boyayyan sirrin namu Wanda babu wanda yasanshi daga Allah sekuma ni da Kai Hassan yazomin dawata magana nikuma nayiwata subutar baki akan lamarin Wanda idan hakan takasance tofa yazama dole wannan boyayyan sirrin namu yafito fili fitowar shi kuwa  wata babbar matsalace wadda zata haddasa tashin hankali cikin masarautar nan sannan musamu babbar matsala Ni da Kai wajan Mama shine nazo muyanke shawarar datadace ” 

Miqewa tsaye Sarki Jabir yayi yashiga kaiwa da komowa sannan yadubi Ammi yace ” Hajiya Kilishi tokuwa koma meye wannan yazama dole abarshi dan banshirya shiga cikin tashin hankali ba yanzu lokacin bayyana wannan sirrin  baiyiba idan lokaci yayi nida kaina zan bayayyana komi sanar dani wane lamarine Hamut yazomiki dashi ? ” 

Sake sakin ajiyar zuciya Ammi tayi sannan tashiga sanar dashi wannan lamarin duka sosai Sarki Jabir yashiga kallonta cikin alamar

 tuhuma sannan yace 

” Tayaya hakan zata yiwu hajiya Kilishi ? hmmm kodama babu wani boyayyan sirri tayaya kike ganin Hamut zai iya jure kallon Hamidat a matsayin matar Hammat ta sirri bayan kinfikowa sanin yadda yake azabar sonta inada tabbacin bazai iya jurewaba me kike tunani idan lamarin ya bayyana bayan wani lokaci mai jama’ata zasu d’aukeni karfa kimanta cewa ni Sarki ne ko yaya baikamata asameni dawata ‘barakaba sannan kisan wani abu idan har muka amince dahaka tofa babu shakka wata lalurarce zatakama Hamut badda wadda yake ciki yanzu sannan a qarshe kisani Hanan batadace da Hamut ba idan kikayi duba da wannan sirrin wannan lamarin bazai ta’ba yiwuwaba kibarni da Hamut nasan maizanyi shikuma Hammat dama baso yakeyiba Hanan kuma nanda 1 week zata tafi Skul itada Ansar lokaci d’aya zasutafi amma kowa waje daban Ansar Saudiyya zashi sabida hakan yake ra’ayi itakuma Hanan batada za’bi shine naza’bar mata dakaina ita Turkiya zata dan haka kufarayin duk wani shirye shirye ” 

Daga haka yabar parlour binshi da kallon Ammi tayi tsayin lokaci tana zaune sannan tamiqe takoma part d’in ta tana shiga tasanar dasu Hanan maganar tafiya Skul sosai kowa yayi murna cikin farinciki Hanan tace 

” To Ammi amma maiyasa ba’a had’amu waje d’aya ba ni Turkiya shikuma Saudiyya ? zamufijin dad’i idan waje d’aya muke ”  

Murmushi Ammi tayi tace ” to anki had’aku d’in salon kuji dad’in yin shiririta ko kamar yadda kukeyi nan dubi Ansar yaci ace tuni yarigaki tafiya Skul amma sabida shiririta yatsaya wai shi dole seya jiraki kinga kenan idan aka had’aku shiririta zakuyi ” Ammi nagama fad’in haka tanufi bedroom dede lokacin Hammat yashigo ganin shi yasa Hanan saurin juyawa dakatar da ita yayi dafad’in ” zonan Hanan ” jiki babu kuzari tajuyo tanufoshi zama yayi kafin ta’iso gareshi yace 

” Had’omin abinci kuma saura kiyimin shirme ” babu musu tanufi kitchen abinci kala kala tahad’o mishi dan tasan halin shi kafin yazauna yaci abinci dawuya amma idan yazauna yanaci sosai bakamar Hamut ba dabayason cin abinci mai nauyi cikin natsuwa ta’aje komi agabanshi sannan tashiga bubbud’e mishi cikin sanyin murya tace ” wanne zakaci yaya ” dubanta yayi fuska tamke yace ” yau kuma wata sabuwar fitsararce kikazomin da ita ? zakizubamin abinci ko senayi ball dake ? ” 

Cikin rawar jiki tashiga yin abinda yace faracin abincin yayi cikin yanayi kamar bayaso tsayin lokaci sannan yagama har yakammala cin abincin Hanan tana gefanshi kamar kodayaushe har seyagama sannan takwashe kayan yauma haka bayan takwashe kayan tanufi kitchen Ansar yadubeshi cikin d’anjin shakka yace 

” Yaya Hammat nanda 1 week zamutafi Skul nida Hanan ni Saudiyya itakuma Turkiya sake tamke fuska yayi sosai yamiqe cikin sauri yanufi bedroom d’in Ammi shiko Ansar duban Hanan yayi yace ” zuwa rana irin tayau zamuga wanda yaya Hammat zai dingayima zalinci ” batare da Hanan tace komiba tanufi bedroom Hammat yana shiga Ammi tadubeshi tun kafin yayi magana tace 

” To uban masifa maikuma yafaru ? ” sake tamke fuska yayi yafesar da iska daga bakinshi sannan yace ” Amma Ammi baikamata nasan lokacin tafiyar yaran nan Skul ba sede naji lokaci d’aya kuma asama gaskiya hakan baiyimin dad’i ba ” 

Sosai Ammi take kallonshi cikin mamaki kafin tace ” to ay banice zakayima wannan tambayar ba mahaifinku zakayima tunda shine yashirya komi nima sede naji yace nan da 1 week zasutafi kuma ayni banga dalilin wannan tuhumar takaba tunda kamar kaga hanjin cikin su kakeji ” jin haka yasa Hammat fita rai ‘bace binshi da kallo Ammi tayi afili tace ” ikon Allah wannan hali naka Husain Allah yacanzamaka shi ” 

Cikin tsananin damuwa Hamut yayi sallama cikin part d’in Sarki Jabir gaidashi yayi cikin girmamawa sannan yazauna dubanshi Sarki Jabir yayi sosai yaji zuciyar shi babu dad’i sabida yadda yaga Hamut d’in yayi muguwar  rama kamar wanda yad’auki lokaci mai tsayi yana jinya ajiyar zuciya Sarki Jabir yasauke sannan yace 

” Hamut dukda naga bakadawata lafiya amma hakanan zakayi haquri kajagoranceni wajan wani mihimmin taro wanda za’ayi a Jodan nanda kwanaki 3 zakatafi    amma taron zai d’auki kusan 2 weeks anayin shi bayan angama inaso kazauna acan kahuta kaji idan matar ka zata’iya binka sekutafi tare idan kuma tace a a shikenan bazamu matsamataba amma tafiya da’ita zaifi kodan maganin  wannan matsalar banzar al’adar zanturamaka doctor wanda zaid’inga dubaka acan nasan zakaji dad’in zama a can Hassan kasani  damuwarka tamkar damuwarmuce idan kasakadamuwa cikin zuciyar ka tamkar muma kajefamu cikin damuwarne kad’auka wannan wata jaraftace daga Allah kuma Allah bayajefama bawanshi wata jarafta face se bawan yazama yanada imani idan har kayi imani tofa dele se Allah yajarafceka yagani zaka’iya cinye wannan jarabawar Hassan nasanka akwai haquri dan Allah kaqara akan wanda nasanka dashi ka’aje wannan shawarar da zuciyar ka take rayamaka akan wai Husain yayi auran sirri da matarka Hamidat wannan babu hanyar billewa acikinta kacigaba dayin haquri watarana se labari tashi kaje Allah yayi maka albarka ” 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button