ABDUL JALAL PART 2

Yaya mairo tace
“ke lafiya kuwa? Ina sa’adah take?”
Naja tace
“ina fa lafiya, sa’adah ta jamu gidan wannan Yarinyar mijinta yasa aka kamamu, wai ko seta fadi inda wata take, nima da kyar yayi waya aka sakeni”
Yaya mairo tace
“ke kimin bayani wai ina kukaje akayi muku hakan? Bangane me kike nufi ba”
A fusace Naja tace “Wai meyasa ba kya ganewa ne, nace miki gidan Jalal ta ja mu, yasa ‘yan sanda suka kamamu, ni sun sakeni ita tana can”
“A’ ahh to me kukayi masa? Wani station dinne?”
“dan Allah ki barni in huta, Allah kadai yasan azabar dana sha ta yunwa amma kin uzzuramun da tambayoyi, niki kyaleni da banyi niyyar zuwa gidan nan ba amma ta jani ta janyomin masifa”
Hankalin yaya mairo ya tashi sosai, gashi Naja taki ta tsaya tayi mata bayani yadds yakamata .
Jalila ta kira Hanan suna ta waya tace
“gaskiya Hanan kina wahalar da bawan Allah, yau kice wannan gobe wancan haka akeyi”
Hanan tace
“Jalila duk yadda zan Gaya miki bazaki gane ba seyazo kanki tukuna”
Jalila tace
“ba wani hadda shagwabarki da neman magana”
“wallahi Jalila ina jin tausayin Haidar sosai, bana laulayi se dai bakomai nake iya ci ba shine kullum ke nema min me zanci, Amma ba yadda zanyi ne”
.
“Allah sarki, Allah yarabaku lafiya, wai watan cikin naki nawane?
” wata na biyar “
Zare ido Jalila tayi ” wai har munyi wata biyar da Aure? Amma kina shiga kikayi karo da shi? “
Hanan tace
“ban saniba, da shi naje, ‘yar rainin hankali wallahi satina biyu, naita ciwon kai muna zuwa Asibiti aka ce cikine”
Dariya Jalila ta dingayi tace “angama iyayin, ana zuwa akayi karo, Allah yaraba lafiya”
“Ameen dai, ina mijin naki, fatan dai komai lafiya?”
“yana nan lafiya” Jalila ta bata amsa
Hanan tace “Ina fatan komai Lafiya Jalila, Allah yasa kun daidaita”
Jalila tace “gamu nan dai”
“gaku nan dai kamar yaya? Har yanzu ba kwa shirin ne”
“munayi sama sama”
“Jalila waike wane irin taurin kaine dake haka?”
Jalila tace “ke karki min fada mana, kin dameni fa, se anjima tafi gurin mijinki kiyi masa”. Seda sukayi dan fadan da suka saba sannan sukayi sallama.
Jalila ta tashi ta dauki zuma ta nufi dakin Jalal, yana ganinta da container zuman nan ya hade rai, murmushi ta farayi tana cewa
“meye kuma na wani hade rai, sekace kaga wani abun gudu”
Jalal yace
“nifa nagaji da shan wannnan abar, kullum kizo kiyita bani, ciwon ciki take sani fa”
Jalila tace
“Ai ciwon cikin ba me damu bane, saboda magani nake baka, so nake inyi substituting din giyar da kake sha da zuma, kuma karatun qur:ani ne a ciki, Insha Allah very soon zaka dena shan giya”
Jalal yace
“ko yanzu ma aina dade ban sha giya ba, dan Allah ki dinga kyaleni da zumar nan, kodai wani abun kike zubamun, dan ki mallakewa Mummy danta?”
Yai maganar yana kashe mata ido, tareda yin murmushi
Dariya Jalila tayi tace
“Kai mallake ka wani wahala zemin ne, ai base na baka magani ba idan ina son hakan?”
“Allah ko?”
Jalila tace “Eh mana, yanzu dai karbi ka sha spoon biyu kawai”
Seda ya bata rai sannan ya karba ya sha yana ya tsuna fuska, dan jan dogon hancinsa tayi tace
“barakallahu fik”
Jinjina kai kawai yayi bece komai ba
A shagwabe Jalila tace
“baka fada ba fa”
Yace “Ameen, thank you”
Murmushi tayi ta shafa sumarsa “weldone dear, bari muyi Adhkar seka kwanta ko?”
Jalal yace “yadda duk kikayi”
Jalila tace “yawwa kafin muyi Adhkar bari muyi magana, wai yaushe zaka koma aiki? Kullum kana gida se dai kaje ka zaga gari ka dawo”
“bazan koma aikin nan ba”
“meyasa?”
” bashi da Amfani ina can zuciya ta tana nan, sam bana samun nutsuwa, ga banbancin Al’adu da dabi’u da muke dasu, gashi nika dai nake tafiya babu ke, akwai damuwane gara inyi zamana inta ganinki kullum ina jin dadi”
Jalila tace
“Haba Jalal, dan Allah ka dena wasa, Aikin nan yana da mahimmanci sosai, at least you have something to do, dan Daddy yana baka duk abunda kake bukata, bashi ke nufin kaima bazaka nemi naka ba”
Jalal ya danyi murmushi yace
“waya ce miki Daddy ne kemin komai? Nasan Daddy yana min wasu abubuwan amma da kudina nake komai musamman abunda ya shafi gidana, da kefa mukaje kika ga kamfani na, Daddy ne kadai da wasu daga ma’aikata na suka san nawa nake samu a duk wata a kamfanina, Allah ya alabarkaci dukiya ta fiye da yadda kike tunani, dukda na kasance me sabon Allah, Amma Allah ya hadani da mutanen Arziki masu Amana da suke juyamin dukiya ta”
Jalila tace “Amma in hakane, yakamata ace ko kamfanin ne kaje ka dinga aiki”
“ke bazani ba ki kyaleni kawai”
Jalila tace “to shikenan na kyaleka, amma gaskiya yakamata a ce munje gida ka gaida Mummy, tunda kaga harta fara magana, baka kyauta ba sam”
Maimakon yayi magana ma harararta yayi yaja pillow ze kwanta, tasa hannu ta rike pillow
“Haba Jalal idan kayi hakan baka kyauta ba, iyaye hakuri ake dasu komai girman laifin da sukayi maka sun gama komai tunda suka kawoka duniya”
Sakar mata pillow yayi ya juya ya kwanta,
gadon ta hau ta cigaba da magana
“Please Jalal, dan Allah yakamata kaje wallahi”
Janyota yayi jikinsa ya rungumeta kam a jikinsa, sosai ta firgice da abunda Jalal yakeyi mata.
“Jalal dan Allah ka bari bana so, ana knocking kofar parlor fa”
Cikata yayi ya lumshe ido, dirowa tayi daga gadon takoma gefe tana kallonsa tareda sauke numfashi, ci gaba da knocking akayi, Jalila tace
“Ana knocking fa”
Jalal yace “kije ki bude mana”
“ni gaskiya tsoro nakeji bazan iya budewa ba”
“ni inje in mutu kenan”
“A’a niba haka ba, kaje ja duba dan Allah”
Jalal ya kalli agogo goma saura, mikewa yayi ya tafi budewa tabiyo bayansa tana labewa a baya, yasa key ya bude kofar parlourn, yana budewa yafara sosa kai yana murmushi, matsawa gefe yayi, Abba da Maama ne suka shigo Jalila na ganinsu tayi tsalle taje ta rungume Maama.
“Maama har na fidda ran zakizo wallahi”
Maama tace “to ki bamu gurin zama mana, har kinfara complain”
Gurin zama ta basu tanata murna, Jalila tace “Abba ina wuni”
Abba yace “lafiya kalau Alhamdilillah”
Jalal yace “Abba ina wuninku?”
Maama tace “lafiya kalau Jalal ya gidan?”
“lafiya kalau Abba”
Jalila tace “Abba shine bakuzo da rana ba, seda dare yayi”
Maama tace “yanzunma Allah ne yayi zamuzo, mun fita gaisuwa gidan abokinsa nace masa ya tsaya mu biyo mu ganki”
Nan suka dinga hira, Jalila tace bari ina kawomu ku Abinci.
Abba yace “ki barshi Baby, yanzu zamu tafi”
Jalila tace “haba Abba, ai ba Abinci me nauyi bane, inada cake a fridge”
Maama tace “Ahh in baya ci ni dakko min nayi missing girke girkenki”
Jalila ta tafi kitchen, ta shiryo cake da lemo a tray zata dakko taga Jalal a bakin kofa yana mata dariya.
Kallonsa tayi tace “dariyar me ka keyi ne?”
Ya karaso inda take yace “juya”
Ba musu ta juya, yasa hannu ya ja zip din rigarta ya karasa rufewa, zare ido tayi tace
“kai wai a bude yake”
Jalal yace “eh ba a rufe yake gaba daya ba”
“na shiga uku, kuma sun gani?”
Dariya ya fara yimata Kamar ze fadi, gaba daya tarasa me yake mata dadi, ta harari Jalal.
Jalal yace “ki kai musu Mana dare yanayi fa”
Ta kwabe fuska kamar zatayi kuka tace
“ni gaskiya bazan fita ba kunyya nake ji”
“kunyar wa kike ji?”
Jalila tace “nikam inajin kunya wallahi”
Jalal yace “karki damu basu gani ba fa, nika dai nagani, dauki muje”
Ta dakko tray din ya biyo bayanta.
Maama taja Jalila bedroom
“Jalila ina datan babu wata matsala, kuna zaune lafiya?”