ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Share please
More Comments More typing…………………………

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 3️⃣/ 56

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki, da suka bibiyeni a littafi na farko, Alhamdilillah yanzuma gani na dawo domin kawo muku kashi na biyu, nagode da kulawarku, ku biyoni domin jin yadda zata kaya a cikin wannan littafi naku me farin jini.
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Gmail @ www.humaira17@gmail.com
Facebook real humaira

          _MY FIRST NOVEL _

Daga nan Ilham tai kwafa, ta nufi kan gadonta, tai shiru tana sake2 a ranta.

Jalal kwata2 yarasa abunda yake masa dadi, meyasa Jalila tai masa wannan muguwar tsanar haka, bata da burin da yawuce taci mutuncin sa, tabbas maganganun da take gaya masa sun fara isarsa, dole ya hukunta ta hukuncin da suka hadu seta canza hanya, hukuncin da zata dandani abunda yakeji idan taci zarafinsa, gata kanwar kanwarsa, amma ko Ilham dasuke gida ďaya bata isa tayi masa haka ba, jiyayi zuciyarsa na wani irin zafi mussaman idan ya tuna yadda Jalila take kiransa da namiji mara daraja. Dole ya hukunta ta dai2 da abunda tayi masa, Ilham ma ze gamu da ita, duk yadda yaso ya manta abunda tayi masa kasawa yayi, karshe ma yaji zuciyarsa tayi masa wani irin nauyi haka yaita juyi akan gado.
Jawwad kam be dawoba se bayan la’asar ya gaji matuka, dan haka benemi Jalal ba se bayan, sallar magariba, yaje gidansu ya duba dakinsa yaga baya nan ya duba bedroom dinsa se yaji shi a rufe, be kawo komai a ransa ba yakoma gida, yai trying lambar Jalal amma shiru baya dagawa, haka ya hakura ya nemi abunda zesawa cikinsa, dan yasan maybe Jalal ya tafi nasa yawon, amma ya damu da rashin daga wayarsa da Jalal beyiba.
Nana tana kwance tana waya da saurayinta, Maama ta shigo dakinsu tace dan Allah in tayi salla taje ta karbo mata laces a wajen Mummy dan in anjima hajiya Jamila zata turo yaranta su karba, dan bata fuska Nana tayi “Maama dan Allah ki aiki Jalila baby ne zezo fa, Maama ta dan bude baki” Lallai Nana, wato saurayinki yafi aikena ko? “” murmushi Jalila tayi tace “Allah ya shiryeki Nana, bari inyi sallar magariba ni se in karbo miki Maama” dan gyada kai Maama tayi ta fice

Jalal kam yanajin wayarsa na ringing yai banza dan tunda ya kulle kansa a daki be fito ba, banda jujjuya kalaman Jalila ba abunda yake, ga yunwa yakeji yanzu yana fita Jawwad ya ganshi a haka ze dameshi da tambayoyin me yake damunsa danhaka ya yanke shawarar ya shiga cikin gida yasamu abinda zeci base yaje gurin Jawwad ba. Ya mike daga kan gadon ya fara yin alwala dan sallar asuba kawai yai, gashi yanzu magariba akeyi, yayo alwala yazo yai sallar azahar da isha’i, seyaji ya gaji dan haka ya mike yace yayi magariba da isha’i anjima kokuma gobe da safe, ya bude dakinsa ya fito, cikin gida ya nufa yana shiga palour Mummy suna kallo itada Ilham bebi takansu ba ya nufi kitchen ya zubo Abinci, ya dakko madara ya fito, abun mamaki yabawa Mummy dan kwanan nan yadena cin Abincin su, Mummy ta kalleshi tace “Jalal zo mana” waigowa yai ya kalleta kaman kar yaje kome ya tuna, kawai se yadawo yasamu guri ya zauna a palourn, yafara cin Abincin sa ba tareda yace komai ba, Mummy takuma tattara hankalinta ta kalleshi “yanaga kana cin Abincin mu yau?” Jalal be dago ya kalleta ba yace
“Dame gidan yakawo Abincin yace banda nine? Yabata amsa ba tareda ya kalleta ba ajiyar zuciya Mummy tayi
” A a ni banceba kokunyi faďa da Jawwad ne? “
” No, yau abincin gidan mahaifina nakeson ci” “Hmm hakan yayi kyau dan nima bana jin dadin kauracewa abincin mu dakayi dukda tarin dukiyar mahaifinka amma ace sedai kaci Abinci a wani guri. shi Jalal mamakin yadda taketa lallabashi yakeyi, ya sha madarar sa sannan yace “Serious ashe bakya san hakan, hmm amma kinsan wani lokacin abun hannun Jawwad ya fiyemin abun cikin gidan mahaifina” Mummy tace “kaga ba wannan ba, daddynka ze dawo next week” “munyi waya, yagayamin” yabata amsa a takaice “Yawwa dama sonake in yadawo ayi maganar aurenka, tunda lokaci yayi dayakamata ace daga kai har Jawwad din kunyi aure, aure shine cikar mutum”
Bayan Jalila ta idar da sallar magariba ta fito karbowa Maama aikenta, kaitsaye gidansu Jalal ta nufa ta tsaya suka gaisa dame gadinsu sannan ta wuce, tana zuwa ta tura kofar palourn ta jiyo hargagin Jalal yana masifa
” wakike tunanin ze auri mutum irina, wakike tunanin yabani ‘yarsa, ko sokike in auri wadda zata soni dan dukiyata? Ta aureni dan ta kasheni ta mallaki abunda nake dashi, Wace yar mutuncin ce zata auri ďan da kikayi sanadiyar lalacewarsa da kanki, lalatacce dan giya kamarni Mummy kozanyi aure a rayuwata se wadda zata soni dan Allah badan wani abu nawaba, wadda bazata kyamaci rayuwar da nake ba, meye damuwarki da dole senayi aure, ai aure ba dole bane”
Da sauri Mummy ta katseshi ta hanyar cewa “A a Jalal abun duk be kai haka ba, baga Ilham nan ba, itace me sonka tsakani da Allah meze hana ka aureta ai kanwarka ce” wani mugun kallo yayiwa Mummy “Au Ashe kinada wani ďan da kika haifa bayanni ai ban saniba se yanzu” Mummy ta kalleshi cikin rashin fahimta tace “kamar yaya?” “inba wani ďan ne dake bayanni ba ai kinsan ba amin dole ko? Ya kalli Ilham” Ke! A tsorace Ilham ta waigo ta kalleshi “tunda muke na tabacewa ina sonki” shiru tayi ba tace komaiba, ya kalli Mummy cikin masifa da tsawa yafara mata magana
“wai dan Allah yaushe zaki fara playing role dinki na uwa, kimin adalci a matsayinki na mahaifiyata, ba kya tunanin in shiryu, se kokarin kuma rusa rayuwata domin wanke laifinki a idon wanda kikayiwa, yakamata ki tausayamin ko sau dayane yakamata ki barni na huta haka, please Mummy ki tausayawa rayuwata haka, a matsayina na tilon danki” karo na farko da Jalila taji ya kira mahaifiyarsa da Mummy, itakam tana son sanin tarihin Jalal da mahaifiyarsa, amma waze gaya mata. Jalal kam yana gama fadin haka ya tashi ya bar palourn ya fito fuuuu kaman guguwa, yana fitowa be kula da Jalila ba a gurin ya wuceta, a hankali tabi bayansa, yana zuwa motarsa ya nufa, yana zuwa ya shiga motarsa yana kokarin kunnata, seya fasa kunna motar ya jingina da kujera yayi shiruu, gefen motarsa taje ta tsaya tai knocking glass din, a hankali ya sauke glass din motar kawai yai tozali da fuskar Jalila. Kokarin kunna motar yake, saboda yasan in har ya tsaya ze iya illata yarinyar nan, dan yasan yanzunma ci masa mutunci zatayi, hannu tasa ta dafa window din motar saitin Jalal tana kallonsa, tana iya juyo yadda yake numfashi,
“ABDUL JALAL kaji tsoron Allah kaji, karka mutu mahaifiyarka tana jin haushinka, kome tayi maka kabata matsayinta na uwa, Annabi salallahu alaihi wassalam se da yafadeta sau uku yace abita sannan yace uba, kaji tsoron Allah kadinga yafiya mana, ka tausaya mata kaimata biyayya, kaji dan gidan daddyn sa, ba daddy kawai keda hakki akanka ba, nasan yanzu mashaya zaka tafi, dan ba kunya ce da kaiba naga baka da alamar zaka dena shan giya, kayi a hankali da duniya, sannan ka kiyayi miyagun abokai, u have to focus, ka kiyayi JeJe da Hannah da sauran miyagun abokanka, basa komai banda rusa maka rayuwa, basa nufinka da alkhairi ka kiyaye, jeka Allah ya shiryeka” manyan idanunsa da suka sauya zuwa launin ja ya zuba mata, cikin idonta ya saka nasa, dukda akwai duhu se hasken fitilu be hanashi ganin fararen idanuwan taba masu kama da tana jin bacci, ji tayi kaman an daureta takasa motsawa tabar gurin, itama ta kura masa ido, ji tayi idonta yayi nauyi, ga Jalal yamata wani irin kwarjini, kamshin turarenta duk yacika masa hanci, daurewa yayi, yai mata wani mugun kallo me wuyar fassara, sannaan ya dauke kansa yace
“ki kiyayi haduwata dake, zanyi maganin wannan shishshigin naki, sekinyi dana sanin shigowa rayuwata, zan baki mamaki, bari in tuna miki alkawarin dana taba yimiki, zan maida ke abun kwatance irina, matsa ki bani guri ko in takeki da mota. A hankali ta motsa bakinta, tafara magana a hankali cike da rainin hankali tace
“zaka iya ai, inbaka takeni da mota ba ba sunanka ABDUL JALAL ba, ni bazan fasa fadan gaskiya ba, kome za kayimin, Kuma bazan taba zama abun kwatance irinka ba, dama kwatancen kirki ne da sauki, Allah ya tsareni zama abar kwatance kamar dan giya”
“Haka kikace?” “baka da kunne ne?” Ajiyar zuciya Jalal yayi, ya kunna motarsa, Jalila ta ja dabaya ya ja motarsa da gudun tsiya, Jalila ta juya zata shiga gidansu Jalal, taga Ilham a tsaye a bakin kofa tana mata wani irin kallo na tuhuma, fuskarta na dauke da tsantsar bacin rai, dakuma tsanar Jalila, dan tana hangen abunda yafaru, tsakanin Jalal da Jalila, a hankali Jalila ta karaso, kota kan Ilham bata biba, ta tureta gefe ta wuce cikin palourn, ta tarar da Mummy a palour ta fada mata sakon da aka aikota, Ilham ta shigo palourn taji zuciyarta tana raya mata taje ta dakko wuka ta kashe Jalila ta huta, itako Jalila ko kallon Ilham batayi ba, tacigaba da abunda take.
Jalal kam kaman yadda Jalila ta fada, mashayar sa ya tafi, amma yana tafe tunani kawai yakeyi, yana ta nazarin mezeyiwa Jalila wanda ze bata mata rai, soyake ya bata mata rai yadda zataji zafi sosai fiye da yadda take masa, manyan mutane ma suna shakkarsa, saboda kwarjinin sa, amma yarinya karama tana caza masa kai, wani abun takaicin jinsa yake duk jikinsa ya mutu, kamshin turarenta kawai yakeji, yai kwafa zeyi maganinta ne. Yasamu guri yai parking Ya fito daga mota
Guri yasamu ya zauna, yai shiru dayake ansan abunda yake bukata customer ne sosai, aka kawo masa giyar dayake sha, befi minti shabiyar da zuwansa ba, sega Hannah tazo , dan an kirta a waya an sanar da ita Jalal yazo, guri ta samu ta zauna tana fuskantar Jalal, “Jalal ina kashiga haka, babu ko waya nadena ganinka kwata2 tun a gurin birthday din ka bankuma ganinka ba gashi inason ganinka, nayi niyyar zuwa gidanku amma bani da lafiya ne” kallonta ya danyi yayi shiru ya cigaba da shan giyarsa. Kallonsa Hannah ta kumayi “Jalal ya kayi shiru, kayi magana mana” “mezance miki, inajinki” ta numfasa tace “Jalal dan Allah menene alakarka da wannan yarinyar me iyayin tsiya, ta fadamin sunan ta amma na manta, a zatona itace Ilham amma ranar ta nunamin Ilham tace ita ba itace Ilham ba” ajiye cup din hannunsaa yayi ya kalleta “meyasa kike tambayata wacece?” “ta damu dakai sosai” “hmm ya akayi kikasan hakan?”
“Alamu nagani” “yayi kyau” shine amsan da Jalal yabata, “Jalal dan Allah wacece ita a gurinka” a fusace ya kalli Hannah yace “ke kin isheni, ki kyaleni dan Allah” “meyasa zakace in kyaleka bayan saboda kai nazo gurin nan, Jalal wata alfarma nake nema a gurinka” kura mata ido yayi sannan yace “ina jinki” “Jalal tuba nakeso nayi, na dena abunda nakeyi, dan Allah so nake ka aureni, aurenka ne kawai ze iya cetoni daga halakar danake ciki please Jalal.
” Aurena ze cetoki daga halakar dakike ciki, nikuma ze janyomin halaka, ke kina tunanin zan zabi mace kamarki a matsayin matar aure, Hannah banason yarana suyi irin rayuwar danayi, dan haka uwa tagari zan zaba musu, ina miki murnar shiryuwa da kikayi, naso dan Allah kika shiryu, amma ina miki fatan alkhairi Allah yabaki miji nagari “yana gama fadan haka ya tashi ya tafi. Hanna ji tayi kaman ta fasa ihu, duk tsawon lokacin nan dasuka dauka tare ammaa ace babau soyayyarta a zuciyarsa, anya JALAL mutum ne kuwa? Aikuwa ko karfene a zuciyarsa seya soni sena aure shi, tana cikin wannan tunanin Jeje yazo, yasamu guri ya zauna a kusa da ita ya kalleta “Hannah manyan kasa, mekuma kikazo yi nan?”
“meya dameka dame nazoyi, oppression na fito, na fito farautar abunda zuciyata ke so, kuma zanyi iyayina inga nasamu” “Hannah kenan dazaki zubar da makamanki ki dawo mucigaba da aiki tare gurin ganin munyi nasara akan Jalal”
“Jeje meyasa kanka baya jane, ban gayamaka cewar bazan kara maka aiki ba, kaina nakewa aiki yanzu, kafita daga harkata ko inyi maganinka wallahi” ta dau Jakarta tai tafiyarta, bayanta Jeje yabi da kallon mamaki, gaskiya Hannah ba karamar mara mutunci bace, betaba zaton zata juya masa baya ba, dole yai taka tsan2 da ita dan yasan halin Hannah sarai, inta sawa ranta samun abu setayi duk yadda zatayi ta sameshi, dole yai wani abu akanta.
Koda Jalal ya dawo gida, Gaba daya yau angama dagula masa lissafi, mussaman Jalila, yau an hada masa zafi sosai duk ransa a bace yake, yarasa me zeyi ya huce, kalmar namij mara daraja da Jalila takira shi dashi se yaji wani mugun bacin rai ya kamashi, yayi tunani sosai mezeyiwa Jalila ya huce haushinsa, gani yai yana kara batawa kansa lokaci, dan haka zuwa yayi ya kuma daukan giya
Ya sha me isarsa, seda fita hayyacinsa ya fadi a gurin yana bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button