ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

“ai ba dake take ba, Ilham ce ta tambaya aka bata amsa”

Mummy najin muryar Jalal tace “Yanzu Jalal kayiwa kanka adalci, dama kana nan kana ji amma kaki amsa min waya, tun jiya nake kiranka a waya amma kaki dagawa”

“Duk lokacin da zaki kirani abunda zaki batamin rai kikeyi, zuwana gida bashi da amfani, Daddy baya Gari, daddy ne kawai yakeson abunda nake so, idan nazo ma Zaki yi maganar da ze batamin raine dan haka ba wani amfani kona zo inda kike tunda..
Rufe bakinsa Jalila tayi tana girgiza masa kai idonta duk hawaye
A hankali tace

“Mummy ce fa, karka fadi abunda ze bata mata rai, Allah zeyi fushi da kai”
Tausayin Jalila ne ma yakama shi, yasan tunda yaga tana kuka yasan Mummy taci mata mutunci ne, ajiye wayar yayi yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta.

Jalila Tana tunanin zama da mutumin da mahaifiyarsa ke mata wannan mumunnar tsanar haka, ta tuna yadda mutunci da girmamawane tsakaninta da Mummy Jalal amma gaba daya ta canza mata, ta maida ita makiyyarta.

“kidena kuka mana, ke har yanzu sekace wata jaririya, dukkan tsanani yana tareda sauki, so stop crying” ya karasa maganar yana yatsina fuska kaman zeyi kuka.
Jinjina masa kai kawai tayi, ya cikata ta juya ta bar Dakin.

Jalila a kwana uku tayi saukar qur’ani a cikin zuma da zam2, da safe kafin Jalal yaci komai take fara bashi zumar nan, sam Jalal baya son zumar nan, dan daya sha yakejin kamar zeyi amai, wani lokacin se sunyi fada sosai yake sha. Ga zam2 da take bashi me dauke da saukar qur’ani. Ta dage sosai akan ganin yana Addu’oi. Zaman nasu ba laifi sedai Jalal bashi da niyyar yi mata komai na bangaren Aure shiyasa ta kara sakin jiki da shi sosai.

Jalila ta kai masa zumar da ta saba bashi, ta tarar yana waya da Jalal

Jawwad yace

“Jalal dan Allah ka siyo mana taura da magarya ka kai tasha a kawo mana, Hanan ce ke so, ni kuma ban san inda zan samu ba anan, kuma bazan iya gayawa Maama a siyo mata ba inajin nauyin hakan”

Jalal yace “Tab to ai nima ban san inda ake saida wannan abun ba tunda ba sha nake ba amma zanyi maganar da Jalila se a siyo a aiko muku” sukayi sallama akan haka.

Jalila tace “ga zumar ka ka sha, zanje in kwanta”
Ya yamutse fuska yace ” Nifa bana son abun nan ciwon ciki take sani”

“yi hakuri ka sha mana, spoon daya kawai” sekace karamin yaro seda taita lallabashi sannan ya karba yana ya mutsa fuska

Jalal ya kalleta yace “A ina ake saida magarya da taura?”

Jalila tace “a kasuwa mana”

Jalal yace “wai Hanan ce take so, za’a siya a aika musu”

Jalila tace “gaskiya Hanan tana bawa yayana wahala, yau tace wannan gobe tace wancan, zan gamu da itane”

Jalal ya harareta yace “dan me bazeyi wahala ba, da haka takeyi? Tunda shi yayi dole ya kula dashi”
Ya kuma maze kamar bashi ya fada ba, itakuwa Jalila ji tayi kamar kasa ta bude ta shige dan kunyar abunda ya fada, ta mike tsama tace

“Amma seda safe”
Murmushi yayi yace “tun yanzu, yau baza’ayi Azkar din bane?”

Tace “A’a ni nayi a dakina, kayi kai ka dai”

Tana fita ya kwashe da dariya, yace “Jalila kenan, kema ina jiran lokaci ne, Allah ka cikamin burina akan Jalila yasa ta soni kaman yadda nake sonta”

Yauma weekends ne dyk suna gida ta kammala aikace2, tana kallon bollywood, knocking din kofar parlor akayi dan haka ta tashi taje ta bude, ga mamakinta Naja ce da sa’adah amma ta boye mamakinta ta saki fuska “Ahh manyan baki sannunku da zuwa” ta basu hanya suka wuce suna mata wani irin kallon banza.

Sukaje suka zauna a parlor, Sa’adah ta kalli Jalila tace “Ashe Aure kikayi?”
Jalila tace
“Aiba ashe bane, tunda gaki a gidana”
Naja tayi tsaki tace “aka dai bada sadakarki tunda bashi yace yana so ba”

“to ke abada sadakar taki mana, ai ba kowace mace ake bada sadakarta a karba ba se ishashshiyar mace”

Sa’adah tace “Ke karki cimina mutunci dan munzo inda kike, matsiyaciya kawai”

Jalila tace “aibani na gayyato ku ba”

A fusace Naja tace “ke karki ci zarafinmu dan munzo gidanki”

“aibana cin mutuncin kowa, musamman wanda yazo inda nake sedai da abunda kazomin dashi nake karbarka”

Jalal tun farkon zuwansu yana jin duk abunda sukeyi, yasan Sa’adah ba zuwan Allah ne ya kawo su ba, shikam yana kokari ya toshe duk wata kafa da zata kawo masa tashin hankali a gidan sa.

Dan haka ne ya fito daga daki ba tareda yace musu uffan ba ya wuce ya bude kofar parlor, ‘yan sanda ne suka shigo, gaba daya suka razana dan basu san Jalal yana gidan ba.

Jalal yanunawa’ yan sanda Sa’adah yace “Arrest her” mikewa sukayi gaba daya Jalila tace

“Jalal meyasa? Me sukayi maka?”

Jalal be kulata ba yace “Arrest her har seta fito da inda Kawarta take”

Sa’adah tace “Amma ni meye nawa a ciki, wallahi officer banyi komai ba”

A tsawace Jalal yace “Arrest her, seta fito da Hannah” aikuwa haka ayi suka kama su Naja suka fita dasu.

Jalila tace “Jalal meyasa? Me sukayi maka haka zaka sa akamasu?”

“calm down, count yourself out of this, babu ruwanki”

“Amma Jalal ace daga sunzo inda nake kasa an kamasu why?”

Janyota jikinsa yayi ya kwantar da murya “Jalila duk abunda nakeyi, duk shaye2 na bana yadda in cuci wani, don’t mind me”

Jalila ta mariraice Tace “Amma”

“Shhh bana son musu”

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724

???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣5️⃣108

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

          _MY FIRST NOVEL _

Jalila kaman zatayi kuka tace

“please Jalal, kome sukayi maka kayi hakuri kasa a kyalesu, karka karamin bakin jini a gurin mutane.

Jalal yayi kasa da muryarsa sosai ya kai bakinsa kunenta yace

“ko kowa ya ki ki, ni ina tareda ke kuma ina sonki, duk me kinki Bashi da gaskiya, duk wanda yake adawa dake wanda baya son cigaba nane, kinyi yaki da mutane da dama saboda ni, ina sonki Jalila,”

Gaba daya jikinta yayi sanyi taji tsigar jikinta na tashi, a hankali tace” Amma Jalal…..

“karki kuma yimin magana akan su, akwai dalilin da yasani yin hakan, karki damu kinji my wife”

Yaya mairo ta kira wayar su Naja babu adadi amma sunki dagawa, sun saba da gantalinsu bata damuwa amma haka nan taji yau takasa nutsuwa, har maghariba bata gansu, se wajen Isha’i Naja ta dawo a wahalce, ko Abinci bata ci ba ga yunwa da kishirwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button