ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Share please

More Comments
more typing……………………..

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 57 4️⃣

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680

          _MY FIRST NOVEL _

Yauma Jalila seda sukayi fada da wani lecturer dinsu, saboda dalibai biyu sunyi laifi ya kori daya yabar daya, dayake wadda yabari din sameera wata muguwar fitsararriya ce, ba dalibai ba har malamai tsoronta sukeji, babban abunda yake bakantawa Jalila be wuce, yadda wasu daga cikin yaran talakawan nan kemata shishshigi ba don samun gurin zama, itakuma taita hantararsu tana musu tsawa, tana zaginsu ko haushi basaji kusan duk ajin suna shakkarta, kaf ajin nan aminiyarta dayace wadda batayiwa wannan rashin mutuncin wato saleema, tun zuwan Jalila ta lura da halin kowa, ita saleema itama babanta yana da rufin asiri yanada kudi amma ba kaman Samira ba, sedai yadda Jalila ta kula saleema ba karamar yar iska bace ba kowa ke gane hakan ba saboda ta iya takunta.
Yanzuma samira ce takewa, wata yar gefen seat dinta magana zahra, zahra ta bada attention dinta sosai akan lectures dinta, koda lecturer ya juyo, samira ya gani tana magana amma ya kori zahra sannan yace bata da attendance dinsa na wannan semester gaba daya, ya kyale samira be koreta ba, har ya juya ze cigaba da lectures Jalila tace
“Excuse me sir” ya waigo yana kallon Jalila, yace mata “Ya dai?” “Sir meyasa ka kori zahra, ba ita tayi magana ba, bakaga ba ita take magana ba, kamata yayi ka koresu su biyun, koka kyalesu duka, amma bekamata a kori wata abar wata ba, amma am sorry idan na fadi ba daidai ba” juyowa yan ajin sukayi suna kallon ta, zuwa yanzu sunfara gane halin Jalila, ba karamar kwalluwar mara mutunci bace, yayinda take birge wasu, saboda iyayinta, da fadar gaskiya, malamin yai saroro yana kallonta ya hade rai yace
“waye lecturer tsakanin nidake?” kanta tsaye tace “Sir wannan ai amsace a bayyane kaine lecturer, nikuma daliba”
“dan me zan yanke hukunci kiyi challenging dina? Ke wacece? Ido kika fini banga abunda yake faruwa bane, ke har kin isa inyi magana ki kalubalanceni a gaban students dina, are u out of your sense” nan fa ya dau zafi ze farayiwa Jalila masifa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, yace ta tashi ta barmasa ajinsa, yauma babu batun ta bada hakuri ta dau jakarta zata kara gaba, shikuma yacigaba da zage2 hardace mata mara tarbiyya aikuwa a take tace “Excuse me sir, daga fadan gaskiya zaka fara min fada hada cemin mara tarbiyya, am just your student not your daughter, am sorry for what i did, kayi hakuri in har na bata maka rai, amma karka manta fadar Manzon Allah ne salallahu alaihi wassalam, duk wanda yaga ana aikata abunda be dace ba, ya kawar da hannunsa, in ba ze iyaba yayi da harshensa, in baze iyaba yaki abun da zuciyarsa wanda shine mafi raunin imani, sir be kamata aji tsoronka aki fada maka gaskiya ba, tunda Allah ne kadai abun tsoro, dan kana shugaba ko malaminmu baze hana a fada maka gaskiya ba, duk wanda ya shigo aji ba dan me kudi dana talaka, kayi treating dinsu equally, yazakaji in zahra yarka ce aka hukunta ta akan laifin wani, kasani wannan hukuncin dakayi mata ranar alkiyama sekun tsaya a gaban Allah, wannan abunda kayi mata ya isa ya toshe maka hanyar arziki a rayuwarka, kudena raina daukar hakkin dalibanku ku dinga ganin ba wani abubane ba dan Allah yabaku dama, bekamata kace gaba daya batada attendence din wannan semester dinba, but with do respect sir this is against our Islamic teachings, da na kowame” daga nan ta juya taana wannan takunnata na kasaita tafita waje, koda Jalila ta fito ta tarar da zahra tasamu guri ta zauna tana kuka, kusada ita Jalila taje ta durkusa ta dafata, “Kidena kuka kinji, Insha Allah komai zezama dai2, kidena zama inda wannan yarinyar take kinga ta cazami ki an koreki” zahra ta kalli Jalila dan ko sannu bata taba hadata da Jalila ba a hankali zahra tace “kema ya koreki ne” “Eh korata yayi” nan Jalila tagaya mata abunda yafaru, zahra tace meyasa kikayi masa magana, rannan ma an koreki daga aji, karki jawa kanki matsala “Jalila ta danyi murmushi tace” babu wata matsala, indai ka dogara da Allah ta ya isar maka, be kamata ya kyaleta keya hukuntaki ba akan laifinta, waima tukuna me kikayi mata naga alamun ta takuramiki”
tsit ajin yayi, aka rasa me cewa wani abu, shiru lecturer yayi na wani dan lokaci, sannan ya kalli wani dalibi yace yaje waje ya kirasu Jalila, aikam ya kirasu sukazo, yace sunemi guri su zauna, sukakoma gurin zamansu, bekuma cewa komai ba yacigaba da gabatar da lectures dinsa, koda yafita haka wasu suka cigaba da surutai akan Jalila, samira ce da yan group dinta tace “ina son sanin waye uban yarinyar nan da take wannan gadarar, harni zata kalla tace a hukunta, tasan waye uabana a kasar nan” saleema tace “kedai bari, amma dagani ba yar talaka bace yanayinta kawai zaki kalla kisan hakan, kuma motar da akekawosu ma babba ce, da alama itama babanta wanine, babyn tama hutawa” tsaki samira tayi “duk kudinta tayi na ubanane, saleema inaso ayiwa yarinyar nan warning, sannan kota halin yaya ina bukatar zahra” sameera tai murmushi “yadda kika dama haka za a sha yar masu kasa, sanan kizuba ido kiga wannan yarinyar carry overs din dazata kwasa a school din nan” suka kwashe sa dariya, Jalila ta kalli zahra, “Zahrah baki gayamin ba, meye hadinki da samira ta takura miki haka, kekuma kinkasa daukar mataki” ajiyar zuciya zahra tayi tace “Jalila ina cikin matsala, ni kinga babana bakowa bane ba a garin nan, ni yar talakawa ce, kinga samira da salima yaran masu kudine sannan kuma… Setayi shiru” inajinki cigaba mana wata ajiya zuciya Zahrah takumayi “Jalila samira da saleema, ba kawayene kawai ba yan iska ne, tun suna yara suke tare, daga maza har mata ba wanda basa nema, wannan yan group din nata dayawansu yaran talakawa ne, amma tasasu a wannan harkar tana basu kudi masu yawa, dayawa lectures sun santa, ba wanda ya isa tasa kara ya tsallake, saboda babanta dan siyasa ne suna da kudi, koda anyi niyyar yimata wani abu a makaranta se tayi amfani da alfarmar mahaifinta, in bata gadamaba setasa a kori mutum, da kike ganin ta haka hatta a hukumomin tsaro taana da mutane, kuma harkar da takeyi har wajen kasar nan, mu amalarta hada manyan masu kudi, itada saleema suke wannan abubuwan, shine tace wai tana sona” zahra ta karashe maganar da hawaye, kallonta Jalila tayi labarin ya daki zuciyarta, amma ta dake tace “to kekuma kikace mata me?” “shine nace mata a’a shine taketa bibiyata take takuramin, tace setasa an koreni a makarantar nan, nikuma inajin tsoro saboda, inason inyi karatu” ta karasa maganar tana zubar da hawaye, Jalila tayi tsaki “kekuma saboda wannan shashancin naki dole ta takuramiki, kin nuna kina tsoron ta, tashi muje muyi salla, semuga ya za ayi” suka tashi suka nufi masallaci, a hanya suka ci karo dasu Samira amma, ba wanda ya kula wani, Samira ta kalli saleema tace “sweet heart, bi yaran can, bana son ta shiga tsakanina da zahra, dan haka ki kiramin ita kice ina kiranta” “bakida wata damuwa, bari inje” kafin saleema taje su Jalila har sun kai masallaci, tana zuwa masallacin taga Jalila ta cire hijjabinta tana alwala, tsayawa saleema tayi tana kallon Jalila, yanzu takekuma ganin kyawun Jalila, parkistan ne a jikinta wando da riga, se dogon gashinta irin na fulani, tana tsugune tana alwala, tubarakallahu komai yaji a jikin Jalila, koda Jalila ta idar tai ido hudu da sameera, tsaki tayi tasaka hijjabinta, suka shige masallaci, haka samira tacigaba da jiranta seda ta idar, saleema ta karaso gaban Jalila ta zauna ta kalleta taimata wani murmushi irin na rikakkun yan isaka tace “baiwar Allah dukda kasancewar, ajinmu daya amma bansan sunanki ba, aikoni akayi gurin ki, samira ce takeson ganinki” shiru Jalila taimata ta dauki jakarta tana saka wayarta, ta kalli kalli zahra tace “zahra taso muje department dinsu Nana, muje capteria muci abinci, saleema tace tab lallai wannan yar rainin hankali ce, saleema tace” baiwar Allah, magana nake fa, samira tace tana son ganinki ” Jalila ta kalli samira tace ” bani da lokacin kowace kucaka a school din nan amma zuciyata zata iya canza ra’ayi “
Daga nan taja hannun zahra suka fita daga masallacin, koda sukaje gurin cin abinci zahra tana ta bawa Jalila labarin halin su saleema. Koda suka gama cin Abinci suka koma aji, lecturer be shigo ba, samira ce ta shigo da mukarrabanta, se wani shan kamshi take, tazo seat din Jalila ta zauna a kusa da ita, ta kalleta tace “dukda bansan wace ce keba, hakan baze hana kisan wacece niba, kuma yar wace niba, kisani ba amin shishshigi, baki isa inyi wani abu kice zakisa a hukunta niba, tunda na shigo makarantar nan, naga yadda kanki yake rawa, to kitsaya a iya matsayinki, nan fada tace duk wanda yake ajin nan a karkashina yake, dan haka kitsaya a matsayinki” samira ta mike zata tafi Jalila batace komai ba, sema murmushi da tayi “yaro be san wuta ba seya taka, baki sanni ba ne, amma muje zuwa”
Ana haka lecturer ya shigo wanda yasa kowa nutsuwa, tunda lectures suke shigowa sau dubu inzakayiwa Jalila tambaya shiru zatayi tace bata saniba, hakan yasa aka fara gulmar ko dakikiyace se tsabar fitsara da izza a cikinta, dasuka fito daga lectures, tay8 sallama da zahra tai tafiyarta gida saboda Manu direba bezoba, Nana kuma basu gama lectures ba, Jalila ta tafi gida tanata tunanin labarin da zahra tagaya mata akan su saleema, lallai dole wasu iyayen su hana yara mata neman ilimi, katura yarinya makaranta amma ta lalace saboda abun duniya.
Haka Jalila taje gida a gajiye, tanata tunani daban2 kanta har yafara ciwo, gida ta shiga, tana tura kofar palour taci karo da yaya mairo da Naja da Maama a palour suna hira, seda jikin Jalila yayi sanyi ganinsu a gidan nan, dan ta san bacin rai zata sha yau, sallama tayi ta shiga, ba wanda ya amsamata se Maama itama a ciki ta amsa, Jalila ta ce “ina wuninku” yaya mairo tai saurin cewa “ke dan Allah ki wuce ni banason kinibibin gaisuwarki, wuce kibani guri” Naja tai saurin cewa “tsabar kinibibine wai ita dole ace ta Allah” Jalila batace komai ba ta wuce dakinsu, tana shiga nan ma ta tarar da sa’ada kwance akan gadonsu tana danna waya gefe ga kwanon abincin dataci da jarkokin lemo da ruwa akan gadon duk ta bata gadon, ta zubar da abinci akai, kallo daya Jalila taiwa sa’ada, ta dauke kanta kaman bata ganta ba, ta ajiye jakarta da hijjabinta, ta dau towel ta shiga wanka, tagama ta fito ta zauna a gaban dressing mirror tana shafa mai, sa’ada ta dago kai ta kalli Jalila ta tabe baki “tabdijan anzo an samu guri, se murjewa ake ana yadda aka gadama, Allah ya rufa asiri ba a girma a cikin arna ba da yanzu ko ana gona hakan doya da goyon shege kokuma anayiwa coci hidima”
Ware gashinta tayi tana tajewa, ba tareda da tayiwa sa’ada magana ba, Naja ce itama ta shigo, ta haye kan gadon gefen sa’ada tana tauna cingam, ta kalli Jalila tace “Allah sarki, mukam mungode Allah da yayimu a musulmai, ba arna ba” haka suka ding a yiwa Jalila rashin mutunci suce wannan suce wancan, amma taki kulasu, ta dauki doguwar riga tasaka, halima ta shigo dakin da sauri ta Rungume Jalila, Jalila ta kalleta “leemart saukar yaushe?” halima tace “dazun nan na dawo akace kina makaranta, Aikena akayine se yanzu na dawo” “Allah sarki ya kika baro mutan garinnaku” “kowa lpy kalau Alhamdilillah, nayi kewarki sayyada Jalila” murmushi Jalila tayi “nima nayi missing dinki da hirarki me ban dariya” Naja tace “Ke halima meye haka kike wani rungumeta, kokema kin hada iri da arnan ne, ko kyamarta ba kyaji” saroro halima tayi tana kallon Naja, Jalila tace “leemart dan Allah hadomin madara da sugar a cup ki hadomin da spoon ina son zansha goldenmorn” halima ta gyada kai ta fita, sa’ada tace “tabdijan wayaga basa banba ansamu guri se abunda akeso a keci sekace a gidan ubanki, lallai Allah ya temakeki wai, da yanzu ana can anacin teba a kauyen su tsohuwa, ko ana gona ana bauta” Jalila kam gaban mirror takoma ta shafa turarurrukanta, ta dau mayafin rigarta ta daura akanta, halima ta kawo mata madara, ta karba tayi godiya, seda tagama shirinta tsaf, sa’ada da naja suna gayamata bakaken maganganu, a hankali Jalila tazo gaban su ta tsaya sannan tace
“nan gidan ubanane, inada ikon yin abunda nakeso inci abunda nagadama inyi yadda nakeso, kufa meye matsayinku a gidan, se abunda yakawo ake diba a baku, kokuma ayi amfani da abunda aka farauto a bariki” da sauri Sa ada ta kalli Jalila, Jalila tacigaba da cewa “kukiyayi cimin zarafi kyaleku kawai nakeyi, ranar dana tashi nuna muku ainihin kalata, zakuji babu dadi, a kiyaye” tanagama fadin haka ta tashi ta fito takoma harabar gidan tai zamanta, a inuwar data saba zama, amma me tunani ya addabi zuciyarta, ga tunanin yadda zata sami tarihin waye Jalal, taya ya zata samu mafita akan
al amuransa, ga tunanin labarin da zahra tabata akansu saleema, jikinta yana bata wani abu akan su, amma takasa gane menene? Kai ita wace kaddarar ta kawota kano, tana zamanta cikin kwanciyar hankali da umminta, kaddara ta kawota kano tunani kaman ze haukata ta, ga jarabar dangin mamansu Jawwad dabasa kaunar ganina”Allah sarki Ummi na, Allah ya bayyanamin ke” a hankali ya rike hannunta
“Yar babyna, tunanin me kikeyi hakane, da alama kin gaji sosai kuma akwai damuwa a tareda ke, kinkasa cin abincin naki, kuma ga hawaye a kwance a idonki, abunda nafi tsana ganin hawaye a idonki, gayamin tunanin me kikeyi? ” Jawwad ne a durkushe a gaban Jalila ya hada hannunta da kofin ya rike a nasa, a hankali kwallar dake idonta ta gangaro, Jalila ta dake tareda kakaro murmushi taimasa ” Yaya kadawo ashe? ” ” naki wayon gayamin meyake damunki?
“bakomai fa nagajine kawai” “amma kika kasa cin abinci” ya karbi cup din hannunta ya debo goldenmorn din ya nufi bakinta dashi “bude bakinki” dauke kanta tayi, ta rike hannunsa “A’a yaya Jawwad, karkashiga matsala, kasan su Yaya mairo suna gidan nan, kar ayimaka fada”
Kallonta yayi “Baby, ni ban damu da hakan ba, bana fargabar kome ze faru indai akanki ne, nasan maybe zuwansune ma yasa sukayi miki wani abu daya bata miki rai”
“A a basuyi min komai ba” “Baby hakan be kamata ya dinga damunki ba, kome za ayimin zan iya jureshi indai akankine, komai tsanani ina tareda ke Jalila, bazan iya rabuwa dake ba, nasan Abba ze bamu goyon baya, ina sonki Jalila ” dan tsura masa ido Jalila tayi a ranta tace “Allah sarki yayana, goyon bayan uwa shine, nasan indai dasu yaya mairo to bazasu barmu tareba” murmushi tayi masa “yaya ka tashi ka zauna akan kujera mana” “A a sekin gayamin kema kina sona tukuna” rufe idonta tayi tana dariya
Jalal ne ya turo gate ya shigo ya tunkaro inda su jalila suke

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button