ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Su Jalila suka yi Sallama, Su Daddy ne suka amsa banda Mummy, Hajiya Salma tace “Jalila me yasa kika fito kina ɗanyen jego”

Tuni Jalila ta fara kuka tace “Anty Salma, Daddy dan Allah ku saka baki Mummy ta yafe min abunda nayi mata, dan Allah kar laifina ya shafi Haidar, kwana na goma da haihuwa bata ga abunda na haifa ba”

Har ƙasa Jalila ta zube tana cewa
“Mummy dan Allah kiyi hakuri kidena fushi dani, ki yafemin abunda nai miki kar laifina ya shafi jikan ki dan Allah”

Gaba daya tausayin Jalila ya kama su, ita kanta Mummy jikin ta seda yayi sanyi, ta ajiye kofin hannun ta ta dauke kai taƙi kallon Jalila, A hankali Jalal ya tako yazo gaban Mummy shima ya durƙusa akan gwiwowin sa ya ɗora Haidar akan cinyar Mummy yace “Mummy na, ga Abunda aka haifa min ba danni ba ba dan halina ba ki sawa jikan ki Albarka, koba komai ke kika haifi ABDUL JALAL ɗanki ɗaya tilo, kuma wannan jininsa ne, sannan zanyi Amfani da wannaan dama gurin neman Afuwar ki akan Abubuwan da nayi miki a baya, Mummy na, tabbas Jalila ta fini gaskiya duk abubuwan da kikayi min a baya, be kamata in saɓa miki ba duba da irin wahala da ɗawainiyar ciki da haihuwa ta da kikayi, ban taɓa ƙinki ba ke mahaifiya ta ce, halayen kine bana so, Mummy na kuɗi da ɗaukaka ba komai bane abubuwa ne da suke fararru ƙararru lokaci daya se Allah ya ƙwace abunsa, Amma soyayya da mutunci basa taɓa gushewa indai anyi sune dan Allah, Ki yafemin sannan dan Allah ki dena ƙin Jalila saboda haakan yafi komai cutar da zuciya ta, Mummy Jalila bata da wani laifi da ta aikata miki da ta cancanci ƙiyayyarki, kin manta alkhaiaran ta a gare ki? Kidinga hukunta mutum da alkhairin sa ba sharri ba”

Ƙurawa Haidar dake hannun ta Ido Mummy tayi, sak Jalal lokacin yana Jariri, ta tuna yadda Daddy yake bin ta Jalal yana kuka, Daddy yana haɗa ta da Allah ta shayar da Jalal, kamar Mummy na da Jalal yayi Amfani da ita ya tuna mata yadda In tazo hutu Jalal yake bin ta yana Mummy na dan Allah karki tafi ki barni, dan Allah ki zauna a gida ki dinga bani Abinci. Ta tuna yadda ya taso me biyayya daga baya rayuwarsa ta tarwatse sanadiyar sakaci da kuma kwaɗayin ta, dama Jalal ze shiryu har ya iya durƙusawa ya nemi Afuwar ta? tabbas ita ya cancanci ta nemi Afuwar sa dan tun bashi da wayo ya sha wahalar kadaicin rashin kulawar uwa.

Take taji ƙaunar Jaririn ya mamaye ta, inama da zata dawo, inama Jalal taiwa wannan kulawar lokacin yana kamar Haidar Rungume Haidar tayi ta fashe da kuka.

Daddy yace “ba kuka zakiyi ba, yara na durƙushe a gaban ki, rashin kyautawa dai kinyi ta tunda har seda suka zo suka kawo miki jariri da kansu”

Mummy tace “Jalal ɗina ni namaka laifi tabbas, ba inda yaron nan ya barka a kamanni irinsa sak na haife ka, sedai na gaza cika haƙƙina na uwa akanka, nabi son zuciya, ruɗin duniya da kuma ƙawaye na ajiye ka na tafi neman duniya, ƙarshe ga duniyar ta samu amma Alhakin Mutanen da na ɗauka ya dinga bibiyar ka yanzu kowa ni yake jin haushi kowa laifi na yake gani, Haihuwar yaron nan ya tunamin abubuwa da dama da suka gabata”

Kuma fashewa tayi da kuka tana shafa gashin kan yaron tace “Jalal am sorry forgive your Mum please”

Jalal ya zauna kusa da Mummy yace “Mummy na babu buƙatar ki nemi yafiya ta, wahalar da kika shiga kafin inzo duniya ya isa in duba ta in miki biyayya amma idona ya rufe, Alfarma ɗaya nake nema a gurin ki yanzu”

Ta kalleshi alamar ina jinka

“Mummy so nake ki ɗauki soyayyar da nakewa Jalila a matsayin tawa ƙaddarar kuma sakayya akan abunda kikayi a baya, Mummy ni kaina ban san wane irin so nake mata ba, Amma Mummy Jalila ta cancanci in so ta ne, Mummy kin san waye ni a baya, kin san irin ƙazamar Rayuwar da nayi, amma kalleni yanzu, jajircewar tace ta saka na gane ni me laifine nazo na durƙusa ina neman afuwar ki, baki nasha faɗar Jalila itace silar haske a rayuwa ta amma baki ɗau hakan da mahimmanci ba, Amma zan gaya miki dalilin da yasa bazan iya cutar da ita ba nake matuƙar son ta, Mummy idan duniya da gaskiya be kamata in wulaƙanta ‘yar da Ummi ta haifa ba, dukda ba kya garin nan Daddy yasan komai yasan ita ta maye min gurbin uwa a lokacin da kikayi nesa da ni”

Nan ne ya zauna ya dinga warwarewa Mummy zare da abawa, Daddy yana tuna masa abubuwa da dama, har kawo lokacin da Jalila tazo kano suka haɗu, hatta ɗuren hayaƙin sigari da yayi wa Jalila seda ya faɗe shi, ya bata labarin gwagwarmaya da fama da Jalila ta dinga yi da Ilham akansa da wahalhalun da ta sha da abokan da suke sashi shaye2, Hanan ma seda ta faɗin abubuwan da shi kansa Jalal ɗin besan anyi su ba.

Shiru Mummy tayi ta sunkuyar da kai, ta kasa ɗaga kai ta kalli kowa a falon.

Jalal yace “dan Allah Mummy ki tayani son abunda nake so, idan kikayi yunƙurin rabamu banyi mata adalci ba, ban kyauta wa Ummi ba kuma naci amanar Abee, Mummy Jalila ta sha wahala ta, in dake ta, in zage ta in ranƙwasheta har hayaƙin sigari na bata saboda tana takura min, Amma bata karaya ba, ta cigaba da bani kariya da kulawa, itama in hakane ya kamata ta ƙini saboda abunda nayi mata, please Mum kiyi hakuri ki kyaleni da matata wallahi ina sonta “

Hawaye Mummy ta cigaba da gogewa amma ba tace komai ba.

Daddy yace
“Deejah kiyi magana mana”

“Daddy mezan ce, inajin kunyar abunda na aikata, nayi kuskure masu yawan gaske tabbas sakayya ce tasa Allah ya jarabci Jalal da son matarsa, da a tunani zan iya kaucewa ayimin abunda nayi shiyasa naso in zaɓo masa mace da kaina, Amma ba’ayi wa Allah wayo, Alhamdilillah Jalal ka samu sauyin Rayuwa, ina matuƙar jin kunyar ka da matarka, tabbas matar ka ba ta dukiyar ka take ba, kaine a gaban ta da rayuwar ka, tabbas itada Jawwad sun taka mahimmiyar rawa a rayuwar ka, wanda ni ban sani ba, dan Allah kuyi hakuri ku yafe min”

Murmushi Jalila tayi ta sunkuyar da kai tana share hawaye tace “Nidai Mummy in dai kin yafe wa Jalal shikenan”
Haidar ne yafara motsi zeyi kuka, Jalal yace “Mummy kawo shi”

“A’a Jalal ka ƙyalemin shi mana, zan iya rarrashin sa ai Gani nake kaman kaine lokacin kana jariri”

Jalal yace “A’a Mummy ke ɗanki ya girma, wannaan ɗana ne idan kina so to kimin ƙani”

Hannu tasa ta talle ƙeyar Jalal tace “sannu mara kunya”

Hajiya Salma tace “Masha Allah, naji daɗin faruwar hakan, ina fatan zaki dena zarginmu akan mun aurawa ɗanki yarinya bada izininki ba, ba muyi hakan dan cutar da shi ba, wanda be guje ka ba lokacin mutane suna gudun ka ba, to tabbas shine masoyin gaskiya”

Mummy tace “Hakane kema Salma kiyi Hakuri dan Allah ki yafe min, tawa tayi kyau da Allah be jarabce ni kamar yadda ya jarabci ‘yar uwa ta Saudat ba, Daddy dan Allah ka tayani neman Afuwar family ɗinka, tabbas na aikata kurakurai masu yawa a rayuwa ta”

Jalila tace “Mummy aishi Allah me Rahama ne da jin ƙai babu ruwansa da girma da yawan laifukan ka, indai harka roƙe shi afuwa ze yafe maka”

Mummy tace “Jalila ban san haka al’amuran suka faru ba, na miki wulakanci na ci mutuncinki dan Allah ki yafe min”

“bakomai Mummy abunda yafi komai yimin daɗi be wuce ganin dai daita warki da Abban Haidar ba”

Sosai Mummy tayi nadamar abunda tayi, sega Mummy da kanta take neman yafiyar wanda taiwa laifuka, Sosai take nunawa Jikan ta ƙauna ta ɗauki son duniya da tattali take wa Haidar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button