ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

An samu Jeje ya farko da kyar, ya zubarda jini sosai, dan haka ana bukatar akara masa wani, duk abokan shaye shayensa suka zame sukece bazasu iya ba, suma jinin be wadace su ba, balle su bashi, Jeje yace dan Allah agayawa Jalal yasan ko kowa ya hanashi Jalal ze bashi Jini, sukace dan dai sako zasu gayawa Jalal.

Kusan kwana hudu Jalal be kara ganin Jalila ba, Jalal yarasa yadda zeyi ya ga Jalila, ko gidansu yaje ya dena ganinta, sannan kuma ta dena zuwa gidansu, gaba daya ransa a bace yake, saboda wannan mummunar Asara datayi masa, shiba kudinne damuwarsa ba se wahalar samu da irin wannan giyar take dashi, kuma ita kadaice in yasha yake jin yaji yadda yakeso. Yana zaune yaji karar mota, ya leka ta window palourn sa yaga Daddy ne yafita shida Mummy, jinjina kai yayi, Wayarsa ya dauka ya kira Jawwad, tana fara ringing Jawwad ya dauka, Jalal yace “Kana inane?”
“Maama ta dan aike nine, ya akayi?”
“Kagayawa kanwarka Mummy na nemanta”
Jawwad yace “to bari in kirata zatazo” ya kashe wayar, Jawwad ya kira Jalila a waya yagaya mata, bata kawo komai a ranta ba tace zataje.
Jalila ta dauki gyalen doguwar rigarta ta saka, ta fito ta tafi gidansu Jalal, sam ta manta da tasaka an fita da kayan giyar Jalal.
Koda taje gidan ba kowa, abun yabata mamaki, ta hangi Ilham a kitchen tana hada Abinci, dan haka ta dan Jira Ilham tafito, tana fitowa Jalila tace “Yawwa Ilham, ina Mummy kuwa? Ance tana nemana” A fusace Ilham ta kalleta “Ban saniba matsiyaciya jarababbiya, wallahi senasaki kuka kaman yadda kikemin, saboda kin iya makirci, kikayi min sharri gurin Jalal bayan dukan da kikamin, shima yazo ya shakeni ya kusa kasheni, wallahi in sharri ne gidan kika tarar, sekin gane bakida wayo, ina nan ina shirya miki trape kuma wallahi sekin fada” cikin mamaki Jalila tace “Ke ni ban gane wani makirci na miki ba, shi makircin ba kekika sanshi, dan Allah ina Mummy”?
“Ninake nemanki ba itaba” waigowa tayi ta kalli Inda Jalal ke tun karo ta, tsayawa tayi kaman wata gunki tana kallonsa har ya karaso inda take, A fusace yakamo hannunta yai waje da ita yana janta, Ilham na ganin haka tace “Allah yasa yamata dukan mutuwa” cikin sanďa ta biyo bayansu. Be tsaya da ita ko ina ba se part dinsa a gaban fridge, ya bude fridge din ya kalleta a fusace yace “Ina abubuwan da kika kwashemun a fridge?” kallonsa tayi ido cikin ido, ta dauke kanta tai masa shiru “Magana nake miki ina kayaana?”
“Meye kayan naka?”
“Tambayata ma kike?”
“Eh, ai bansan wani kayan bane gara ka gayamin, idan nina dauka, se ince maka nina dauka inbani bace ba zance bani bace”
“Ke meyasa a rayuwarki, kikeson rainamin hankali ne? Kekika dauka ko kaffara bazanyi ba, ina kayana ko in kakkaryaki yanzun nan” ta kalleshi cike da tsiwa da gadara tace
“Na dauka na zubar a shara, nabayar an fita dashi ansaka a bola” ta kare maganar tana kallonsa up and down, wani mugun takaici ne ya kama Jalal, shi takewa wannan gadarar haka, hannunta ya janyo, sukazo daf suna iya jin numfashin juna sannan yace “Ubanwa yasa ki daukarmin kaya, kekika ajiyemin?”
“ba uban daya sani, nina sa kaina, kaga sakarmin hannu, last week ka hankade ni kakusa karyani yanzu kuma kana kokarin karasamin hannu, cikani” lallai Jalila ta kai makura wajen iya rainin hankali, ta masa laifi kuma tana masa gadara
“Ka cikani nace kobaka jinane, kaikam Allah ya shiryeka, kota lafiyarka bakayi, se tsabar masifa da taurin kai ni cikani….
Wanka mata mari yayi, wanda yasa Jalila dena gani na wani dan lokaci,
“bansan a dadin lokutan dana dauka ba ina miki kashedi akan kifita daga harkata, ke wace irin mara zuciya ce, wace irin uwar shishshigi ce ke? Darajar Ummi da Jawwad kikeci da tuni na kakkaryaki na karya banza, ina ruwanki da mara tarbiya wanda baya ganin darajar iyayensa, ina ruwanki dani? Ke kullum burinki kiyi abunda zaki bata min rai ko?” tuni Hawaye ya wanke mata ido, dan sau daya aka taba marinta shima Hanan ce, kuma seda ta koyawa Hanan din darasi, idonta na kwararar da hawaye, cikin nutsuwa tace
” Hakane na fiye shishshigi, kuma inka karyani ka karya banza, amma da ina cin darajar Ummi da Jawwad koda wasa bazaka mareni ba, dan nasan Jawwad baze taba marin wanda yafito daga ahalinka ba, Nagode sosai da wannan marin da kaimin, bazan taba mantawa ba, Allah yabaka Hakuri, Allah ya huci zuciyarka nadena maka shishshigi Insha Allah, Kacigaba da shan giyarka Jalal da dukkan wani nau’i na shaye2 karka dena, bazan kuma takura rayuwata akanka ba, na tafiyar da lokuta masu tarin yawa akan tunani dan ganin kazama mutum kamar kowa, sannan mutane sudena kyamatarka, nashiga damuwa da gwargwamaya saboda kai, but this is what I deserve from you, dana san abunda naimaka ze bata maka rai ta kai gaka mareni da banyi ba, ina me baka hakuri, Insha Allah dana kammala abunda nake zan dena maka shishshigi, balle incigaba da bata maka rai” gaba daya jikin Jalal yayi sanyi, be gama gane inda magamganun Jalila suka dosaba
“Cikani in tafi” yana kokarin yin magana, cikim Zafin Rai tace “Kacikani Jalal tun kafin in rama marin dakayimin, kaine mutum na biyu daya mareni a rayuwata, wadda taimin na farko seda na tabbatar da na koya mata darasi, kaima wasu dalilaine zasu hanani ramawa ka cikani nace maka” tai maganar tana Hawaye, gaba daya Jalal ya rikirkice, ta fizge hannuta ta fito waje ta tafi gida, seda ta tsaya a waje ta gyra fuskarta ta maze sannan ta shiga gida.
Ilham da take labe kuwa gida ta koma tana murna tareda yiwa Jalila Allah yakara.
Shikam Jalal guri yasamu ya zauna yai shiruu yana tunani, danasanine ya lullube shi, meyasa ya mareta ya akayi har ya mareta, “Jalila ce fa ya akayi na mareta ne? Mtseww yarinyar nan ta fiye shishshigi da taurin kai” magamganun Ilham da mamanta da sukayi a Asibiti ne suka dinga dawo masa. Mikewa yai da sauri yabi bayan Jalila amma kodayaje gidansu ma tariga ta shige cikin gida, dakin Jawwad ya tafi ya zauna yai shiru duk abun duniya ya dameshi musamman inya tuna Hawayen daya gani a fuskarta. Wayarsa ce tafara ringing, lambace ba suna ya daga yasa a kunensa, anan aka sanar da Jalal Jeje yana kwance a Asibiti rai a hannun Allah yana bukatar jini amma an rasa me bashi, bill din Asibitin dana magani ma ba’a biyaba, Jalal yace Insha Allah gobe zezo Asibitin aduba jininsa in yayi daidai asawa Jeje, sannan ze biya bill din Asibiti.
Jalila bata taba zaton Jalal ze iya marinta ba, yau taki kula kowa har dare ba wanda ta kula, duk yadda Naja taso ta tsokane ta suyi rigima Jalila taki yadda.

Washegari karfe sha daya na safe Jalal ya shirya ya tafi Asibitin da Jeje yake, ya tausaya masa ganin halin dayake ciki, bakowa a gurin Jeje se shikadai gashi ba’a wani kula dashi saboda ba’a biya kudin Asibiti ba, Jalal yana zuwa yabiya kudin Asibiti, sannan yasa aka canzawa Jeje daki, Jalal yana zaune agaban gadon Jeje, yana jira likitocin suzo aje lab a duba in jininsa zewa Jeje, ‘Yan sanda biyu suka shigo dakin suda wani babban mutum sekuma Jalila mamakine yakama Jalal ya tsaya yana kallonsu, Kokusa Jalila bata nuna tasan Jalal ba sukaje gaban gadon Jeje, y’ansandan suka mikawa Jalal hannu suka gaisa, amma hankalin sa yana kan Jalila, ta kalli babban mutumin ta nuna Jeje tace “Yallabai wannan ne, shine wannan” mutumin ya gyada kai yace “aidaganinsa kaga criminal, ni kaman na taba ganinsa a wani guri, amma wannan fa, dan uwansa ne kokuwa? Shima wannan da gani drunker ne” kalmar drunker da Suleiman yafadawa Jalal, Jalila taji bataji dadi ba, amma ba yadda zatayi tunda Jalal yana shaye2
Jalila tace “Yallabai yanzu zakaji komai daga bakinsa” ta taka a hankali ta tafi gaban gadon Jeje ta tsaya ta kalleshi ya kalleta tace “Yau nacika maka alkawarin dana dade inayi maka, senaga bayanka, inaga kusan sau hudu ina gayamaka wannan kalmar, bari inbaka wani sako kagayawa ubangidan ka Oga KB, kokuma ince Alhaji Kabiru, kagaya masa Ni Jalila Aliyu Imam, ni nasaka aka kamaka da shi da ‘yarsa a gidan karuwai” gaba daya suka juyo suna kallon ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button